Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Sharhi: A gaji Abubuwan Tarihi Iri Na Al’adu Da Na Halittu A Yi Kokarin Samun Sabuwar Hanyar Kawar Da Talauci

Published

on

Yau Asabar, rana ce da MDD ta kebe domin jaddada muhimmancin kare abubuwan tarihi na al’adun gargajiya da na halittu da aka gada daga kakannin kakanni. Babban jigon wannan rana ta bana shi ne “gadon abubuwan tarihi da kuma tabbatar da kiwon lafiya”. Don wannan rana ta musamman, an gudanar da wasu bukukuwa fiye da 4,600 a wurare daban daban a kasar Sin, da nufin nuna kwarin gwiwar mutanen kasar kan al’adunsu na gargajiya, da amfani da al’adu wajen raya kauyuka, da taimakawa aikin kawar da talauci.

A nan kasar Sin, kusoshin gwamnatin kasar, sun ba da muhimmanci sosai ga aikin kare abubuwan tarihi na al’adun gargajiya da aka gada daga kakannin kakanni. Alal misali, shugaban kasar, Mr. Xi Jinping ya sha nanata cewa, al’adun gargajiya albarkatu ne masu daraja da ba za a sake kera su ba, balle a maye gurbinsu. Bugu da kari, idan ya yi rangadi a 撒sassa daban daban na kasar Sin, a kullum ya kan kai ziyara gidajen adana kayayyakin tarihi ko wadanda suka kware wajen kera kayayyakin hannu bisa fasahohin gargajiya. Bugu da kari, shugaba Xi ya kan ce, dole ne a kullum a ba da muhimmanci ga aikin kare kayayyaki da abubuwan tarihi.
A yayin gagarumin biki na tunawa da ranar da aka shirya a birnin Guilin dake kudancin kasar Sin a yau Asabar, darektan hukuma mai kula da aikin kare kayayyakin tarihi ta kasar Sin, Mista Liu Yuzhu, ya ce, kawo karshen shekarar 2018, yawan abubuwan tarihi na al’adun gargajiya da aka gada daga kakannin kakanni na kasar Sin da aka shigar da su takardar sunayen abubuwan tarihi na al’adun gargajiya da aka gada daga kakannin kakanni ta MDD ya kai 40, wato kasar Sin ta zama kasa mafi yawan abubuwan tarihi na al’adun gargajiya da aka gada daga kakannin kakanni a duk fadin duniya.
Ba ma kawai, ana kokarin kare su ba, har ma ana kokarin ba abubuwan tarihi na al’adun gargajiya da aka gada daga kakannin kakanni damar taka rawa wajen kawar da kangin talauci a kasar Sin.
Mr. Wang Chenyang, wani jami’in hukumar kula da abubuwan tarihi na al’adun gargajiya da aka gada daga kakannin kakanni ta ma’aikatar kula da harkokin al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ya bayyana cewa, kawo yanzu, an kafa shagunan samar da kayayyakin al’adun gargajiya fiye da dubu 2, inda ake gudanar da shirye-shirye fiye da 2200 irin na abubuwan tarihi na al’adu, da kuma horar da mutane kusan dubu 180, har ma samar da guraben aikin yi ga mutane kusan dubu 500. Sakamakon haka, yawan magidanta fiye da dubu 200 sun kubutar da kansu daga kangin talauci.
Alal misali, kauyen Zhanqi dake karkarar birnin Chengdu dake yammacin kasar Sin, ya yi suna sosai wajen samar da takalma irin na gargajiya. Yanzu kauyen ya zama wani wurin shakatawa. Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, a shekarar 2019, yawan mutanen da suka bude ido a kauyen ya kai fiye da miliyan 1 da dubu 100 wadanda suka kawo wa kauyen kudin shiga na gomman miliyoyi. Galibin masu yawon bude ido a kauyen sun fi son sayen takalman da aka yi a kauyen.
Jama’a masu karatu, kare abubuwan tarihi na al’adun gargajiya da aka gada daga kakannin kakanni, ba ma kawai babban shiri ne na wata kasa ko wata kabila ba, har ma yana ba da gudummawa sosai wajen kyautata zaman rayuwar al’umma. A kasar Sin, muna da dimbin abubuwan tarihi na al’adun gargajiya da aka gada daga kakannin kakanni, a kasar Najeriya ma, ana da wasu sanannun abubuwan tarihi na al’adun gargajiya da aka gada daga kakannin kakanni, kamar su Oral Heretage of Gelede na Yoruba Nago da wasu kabilun Mahi and Feng da Ijele masquerade da wasu unguwannin mazauna jihar Anambra suka sanya da kuma Ifa Divination System ta Yoruba da dai makamatansu. Mu yi kokari tare wajen kare su, kuma a nan gaba, za mu iya yin mu’amalarsu a tsakanin kasashen Sin da Najeriya. (Sanusi Chen)

Advertisement

labarai