Daga Idris Umar
A ranar Alhamis da ta gabata ne ƙungiyar matasa masu hurɗa da shafin sada zumuta ta “internet”mai suna Arewa Social Media Forum ta karrama babban Alkalin babbar kotun ƙasa da ke Abuja “High Court” Malam Ishak Bello Ƙuliyan Zazzau a ofishinsa dake Abuja, sun karrama shi ne a matsayin garkuwar talakawan Arewa.
Wakilinmu ya na ɗaya daga cikin wakilan kafafen yaɗa labarai da suka sami halattar wannan buki kuma ya tattaro mana yadda wannan taro ya gudana.
Tun farko dai ƙungiyar ta wakilta shugabanta ne Malam Aliyu muhammad da mambobinta da suka fito daga jihohi daban daban na fadin tarayyar ƙasarnan ciki har da Abuja.
“Wato mai shari’a, Malam Ishak Bello Ƙulliyan Zazzau bayan karramashi kuma wannan ƙungiya za ta bashi sarautar ban girma na matsayin (garkuwar talawan Arewa) saboda cancantar sa, don haka muke son duniya ta ji ta shaida cewa, mun ba shi wannan sarautar tare da jinjina masa a kan ƙoƙarin da ya ke yi na kawo ci gaba a fadin Arewa da ƙasa baki ɗaya, da fatan mai shari’a zai ƙara dagewa a kan abin da ya saba na ƙoƙarin haɗa kan al’umma da kawo sulhu a tsakani ba tare da nuna wani kabilanci ba ko wariya ba”
Bayan Hajiya Nafisa ta gama nata jawabin ne sai shi shugabn ƙungiyar ya bayyana wa mutanen da suke wannan wajen manufofin ƙungiyar da dalilinsu na bayar da wannan kambun ga mai shari’a Malam Ishak Bello inda ya ce, ƙungiyar ta su tana mu’amula ne da yanar gizo, wato shafin sada zumunta na zamani kuma ya ce, sun kafa ƙungiyar ce don faɗakar da jama’a halin da ƙasarmu ke cikin a bangaren cigaban rayuwa, kuma sukan dubi wani abu da al’umma suke buƙata a ɓangaren cigaban rayuwa sai su yada shi don amfanarwa, musamman birni da ƙauye kuma suna taimakawa marasa lafiya ta hanyar nema masu tallfi ta yanar gizo, kuma su kan sanar da duk wani saƙon jarabawa da a kan zana don taimakawa juna, kuma su kan shirya taron ƙarawa juna sani ga samari don fahimtar yadda za su fashinci amfani da shafin sada zumunta, to bisa irin abin da ƙungiyar ta ke yi ne ta hango irin namijin ƙoƙari da mai shari’a ya ke yi ga al’umar ƙasarsa kuma su ka zartar da shawarar ƙarfafashi a kan hakan ta hanyar ba shi kambun girma don ya zama abin koyi ga al’umar ƙasa baki ɗaya da fatan Allah maɗaukakin Sarki zai ƙara masa ƙwarin guiywa a kan abin da ya ke yi.
Bayan karramashi ne tare da bashi takardar shaidar zama Garkuwan Talakawan Arewa da ƙungiyar ta ba shi, sai mai shari’a kuma babban al’ƙalin na babban kotun ƙasa “High Court” ya tashi domin yin jawabi a kan abin alkairin da a kazo masa dashi, amma daga farko ya miƙa godiyarsa ne ga Allah kuma ya yi wa Annabi Salati sannanya roki Allah ya baiwa shugaban ƙasa lafiya kuma ya nemi Allah ya ƙarawa Nijeriya zaman lafiya da wadatar arzuki.”
Ya ci gaba da cewa, ya ji daɗi sosai da har Allah Ya Sa ya yi wani abun alkairin da har za a gani a kuma yaba masa ba tare da ya san ya yi ba, don haka ya godewa Allah, Bayan haka kuma mai shari’an ya gargadi ƙungiyar akan abubuwa guda uku, na farko ya ce, kar su kuskura su zama ƙungiya mai yada fitina ga al’ummar da suke tare da su wato su zama uwa daya uba ɗaya don kawai a basu kudi da mota ya ce, yin haka babban kuskure ne ga rayuwar su don kuwa, komin daɗewa abin da suka aikata zai dawo kansu, ya ce, na biyu kuma, wajibi su kiyaye yaɗa labarin ƙanzon kurege wanda zaka ga wasu lokuta ana amfani da hakan anayiwa wasu yarfe a lokutan siyasa. “hakan bai dace ba” in ji shi.
Daga ƙarshe ya janwo hankalin duk wani ko wasu masu amfani da yanar gizo ko kuma shafin sada zumunta da su ji tsoron Allah, su yi amfani da shi wajan sada zumunci ba raba zumunci ba ya ce raba zumunci ba abu bane na nagari don haka kowa yaji tsaron ranar da za a tasheshi ya faɗi abin daya aikata a duniya, “wannan lokacin ba a tuba kuma don haka da muguwar rawa to gara kin tashi” in ji shi. Domin in kai musulmi ne to dage ka yi koyi da Islam domin Islam a na nufin zaman lafiya ne kuma in kai Kirista ne to riƙe baibul domin duk shwagabanin addinan baza ka taba jin tarihi ya nuna cewa sun kai ma wani hari ba sai dai kariya saboda in kana son mutun ya fahimce ka to sai ya ga abin kirki daga gareka wato sai ka zama mai tausaya masa.
A nasa jawabin “Grand Khadi” na Shari’a Court of Appeal Shaik Ibrahim Rufa’i Imam ya bayyana jin daɗin sa a kan yadda ya ji ƙungiyar ta zo da kyawawan manufofi a kan yadda suke gudanar da aikinsu na yada labarai a yanar gizo, don haka ya kara ƙarfafa cewa, su kula da abin da zasu riƙa yaɗawa ga al’ummar ƙasa baki ɗaya, don duk abinda suka rubuta Allah zai tambaye su a ranar ƙiyama, don haka ya basu ƙwarin guiwa a kan ƙokarin da shi babban mai shari’a ke yi a ɓangarori da dama da suka ba shi taimako da jin tausayin ƙasa da shi na bai wa kowa haƙƙinsa da ba da shawara ga abokan sa a duk inda ya hango wata matsala za ta taso, daga karshe ya yi fatan yadda su ka zo lafiya Allah ya mayar da su gida lafiya.
Shi ma babban Rajistra na “High Court”, CR Babangida Hasan ya nuna godiyarsa ne ga wannan ziyarar da karramci da aka kai masu kuma ya yi fatan zumunci zai ɗore ƙwarai a tsakanin su da ƙungiyar.