Sharhi: Kasashen Duniya Za Su Gano Amsa In Sun Kwatanta Tarukan Koli Na Xi’an Da Hiroshima
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharhi: Kasashen Duniya Za Su Gano Amsa In Sun Kwatanta Tarukan Koli Na Xi’an Da Hiroshima

byCMG Hausa
2 years ago
Hiroshima

A kwanakin nan, an gudanar da manyan tarukan koli guda biyu kusan a lokaci guda, wato taron kolin kasar Sin da kasashen da ke tsakiyar Asiya wanda aka gudanar a birnin Xi’an na kasar Sin, birnin dake zama mafarin hanyar siliki, da kuma taron kolin kungiyar G7, wanda aka gudanar a birnin Hiroshima, birni na farko a duniya da aka kai masa harin nukiliya, hakan nan kuma tarukan biyu sun bambanta sosai bisa la’akari da abubuwan da suke neman cimmawa.

Taron kolin kasar Sin da kasashen da ke tsakiyar Asiya wanda aka kammala shi ba da jimawa ba, ya mai da hankali a kan karfafa hadin gwiwa don tinkarar kalubale, kuma manufar taron shi ne karfafa hadin kai a maimakon yin fito na fito.

  • Shugabannin Kasashen Tsakiyar Asiya Sun Yi Alkawarin Kara Hadin Gwiwa Da Sin

Kamar dai yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a jawabinsa cewa, duniya na fatan ganin tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaba da jituwa da hadewa da juna a tsakiyar Asiya, ya kamata a gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a tsakanin Sin da kasashen da ke tsakiyar Asiya, kuma ya kamata kasashen su tsaya kan taimakon juna da tabbatar da ci gaban juna da tsaronsu na bai daya da sada zumunta da juna daga zuriya zuwa zuriya.

Haka nan kuma ya shaida yadda kasar Sin ke cudanya da kasashen biyar din da ke tsakiyar Asiya bisa tushen zaman daidaito, kuma ba domin dakile wata kasa ba suke hulda da juna.

Taron na yini biyu ya cimma gagaruman nasarori, kuma babu shakka ya shaida ainihin ma’anar cudanyar kasa kasa, tare da kiyaye tsari da adalci a duniya.

A daya bangare kuma, taron kolin G7 da har yanzu ke gudana a birnin Hiroshima, yana mai da hankali a kan haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen duniya, wato su kulla kawance don yin fito na fito da wasu kasashe. Kasar Japan mai masaukin baki tana amfani da damarta ta karbar bakuncin taron, don neman kulla kawance da sauran kasashen kungiyar, a yunkurin tinkarar abin da take kira wai “barazana daga Rasha da Sin da kuma Koriya ta arewa”, a sa’i daya kuma, tana neman goyon baya daga kawayen nan nata a kan batun zuba dagwalon ruwan nukiliya cikin tekun Pasifik. Ita kuma kasar Amurka ma burinta a bayyane ne, wato tana ci gaba da neman rura wutar rikicin Ukraine, tare da karfafa kawancenta da kasashen G7 wajen tinkarar kasar Sin. Da haka, muke iya gano cewa, manufar taron G7 shi ne su karfafa kawancensu don dakile sauran kasashe.

In mun kwatanta tarukan biyu, cikin sauki za mu gane cewa, tarukan biyu sun bambanta sosai daga dalilan gudanar da su da ma burin da ake neman cimmawa. Taron da aka gudanar a birnin Xi’an an gudanar da shi ne sabo da neman ci gaba na bai daya, don haka ma, abin da aka tattauna a gun taron shi ne ta yaya za a tabbatar da ci gaban kasashen.

A sa’i daya kuma, taron da aka gudanar a Hiroshima ya shaida yadda kasashen G7 suke da ra’ayin nan na samun ci gaba daga faduwar wani, don haka ma, sun fi mai da hankali a kan yadda za su kulla kawance da juna don yin fito na fito da wasu.

Daga Xi’an zuwa Hiroshima, tarukan biyu tamkar wani madubi ne dake haskakawa kasashen duniya, don gano amsa idan sun kwatanta su. (Lubabatu Lei)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
Kasa Da Wata Biyu Ya Bar Mulki, Shin Ko Buhari Ya Cika Wa ‘Yan Nijeriya Alkawarin Da Ya Yi Mu Su?

…Yadda Daura Ke Haramar Tarbar Buhari – Alhaji Saleh

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version