Connect with us

RAHOTANNI

Sharhi: Layukan Dogo 3 Sun Zama Shaidu A Kan Hadin Gwiwar Sin da Afirka

Published

on

 

 

Yanzu ci gaban aikin gina kayayyakin more rayuwa ya zama wata shaida ta halayyar Sinawa ta himma da kwazo, da jan hali. Sai dai a shekaru fiye da 40 da suka wuce, yayin da kasar Sin ke taimakawa kasashen Tanzania da Zambia wajen shimfida layin dogo a tsakaninsu, babu kayayyaki da na’urori masu inganci, ko kuma fasahohi na ci gaba da za a iya amfani da su. Abun da kawai aka dogara da shi, shi ne huldar ‘yan uwantaka dake tsakanin Sinawa da jama’ar Afirka.

A shekarun 1960, kasashen Tanzania da Zambia da suka samu ‘yancin kansu ba da dadewa ba sun yi shirin shimfida wani layin dogo. Kasashen sun nemi taimakon wasu kasashen dake nahiyar Turai, gami da bankin duniya, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba. Daga baya sun bukaci neman taimako daga kasar Sin, kuma Sin ta yarda.

A lokacin kasar Sin ita ma na fama da koma bayan tattalin arzikinta. Dalilin da ya sa ta yarda da ba da tallafi na gina wannan layin dogon mai tsawon kilomita 1860, shi ne domin Sin dake da tarihi na zama karkashin danniyar ‘yan mulkin mallaka, ta fahimci bukatun kasashen Afirka na neman ‘yancin kansu. A watan Yulin shekarar 1976, an kammala gina layin dogon, inda ma’aikata Sinawa fiye da 60 suka sadaukar da rayukansu domin gina wannan layi.

Zuwa yanzu ana ci gaba da kokarin raya huldar cude-ni-in-cude-ka tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Bayan wasu shekaru 40 da kasar Sin ta shafe tana aiwatar da matakan gyare-gyare da bude kofa a kasar, Sin ta kasance kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kana ta fitar da ‘yan kasar fiye da miliyan 700 daga kangin talauci. Sai dai har yanzu, kasashe da dama dake nahiyar Afirka ba sa iya dogaro da kansu a fannin tattalin arziki.

Yayin da ake kokarin raya huldar dake tsakanin Sin da Afirka, kullum ana mai da hankali kan hadin gwiwarsu, da neman samu ci gaba tare. A shekarar 2000, an kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, sa’an nan a shekarar 2006, an gabatar da manyan matakai guda 8 game da raya huldar dake tsakanin Sin da Afirka. A shekarar 2015, yayin taron kolin da aka kira a Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu karkashin laimar FOCAC, an gabatar da manyan shirye-shiryen hadin gwiwa guda 10, don taimakawa nahiyar Afirka daidaita wasu matsalolin da take fuskanta.

Daga bisani, a watan Oktoban shekarar 2016, an fara yin amfani da layin dogon da ya hada Addis Ababa na kasar Habasha da kuma birnin Djibouti na kasar ta Djibouti. Wannan layin dogo na zamani ya kunshi fasahohi masu ci gaba kirar kasar Sin. Ana kiran wannan layin dogon da suna “Layin dogon Tanzania-Zambia na sabon zamani”.

A watan Mayu na shekarar 2017, layin dogo da kamfanin kasar Sin ya gina tsakanin biranen Mombasa da Nairobi na kasar Kenya ya fara aiki,. Jirgin yana sufurin fasinjojin a gudun kilomita 120 cikin ko wace sa’a, yayin da yake sufurin kayayyaki cikin gudun kilomita 80 ko wace awa, shi ya sa ake kiransa “layin dogo mai saurin tafiya na Afirka”. Bugu da kari, layin dogon ya samar da guraban ayyukan yi fiye da dubu 46 ga Kenya, baya ga taimakawa ga karuwar tattalin arzikin kasar, inda GDP na kasar ya karu da 1.5%. A nan gaba, ana sa ran layin dogon zai hadu da layukan dogo na kasashen Uganda da Ruwanda da Burundi da ma Sudan ta Kudu, ta yadda za a iya hada gabashin Afirka waje guda

Me ya sa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka ya samu amincewar jama’a da kyawawan sakamako? Manufar “kulla dangantaka da kasashen Afrika bisa gaskiya da kauna da yarda da aminci” da kuma dabarar “cimma muradu da kuma martaba ka’idoji” da kasar Sin ke aiwatarwa su ne dalilai. A cikin shekaru biyar da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar Afirka har sau hudu. Kasar Sin ma ta kasance abokiyar Afirka mafi girma ta fuskar cinikayya a shekaru tara a jere, inda jimillar kudaden da Sin ta zuba wa Afirka ta zarce Dala biliyan 110. Ban da wannan, kasar Sin ta soke harajin sa ake karba bisa 97% na hajojin da kasashen Afirka 33 wadanda ke fama da kangin talauci suke shigarwa Sin. Duk wadannan sun shaida cewa, ba ma kawai Sin da ‘yan uwanta da ke Afirka sun sha wahala tare ba, har ma za su samu wadata gaba daya.

A halin yanzu, akwai wasu da ke ra’ayin daukar matakai daga gefe daya kurum da ma ra’ayin nuna fin karfi ta fuskar cinikayya a duniya. Hakan ya sa kyautata hadin gwiwar Sin da Afirka da raya makomarsu ta bai daya ta zama wajibi. A yayin taron koli na FOCAC da za a gudanar a ranakun 3 da 4 na watan Satumba, ana sa ran hade shawarar “Ziri daya da Hanya daya” da Ajandar AU game da raya nahiyar nan da shekarar 2063 da Ajandar neman samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 ta MDD da ma shirye-shiryen kasashen Afirka tare, domin sa kaimi ga raya makoma ta bai daya tsakanin bangarorin biyu, da ma kawo alheri ga jama’a kimamin biliyan 2.4 na bangarorin biyu.

Bisa al’adun gargajiyar kasar Sin, “Duk da cewa an samu wadata, amma ba za a manta da abokai yayin da suke cikin talauci ba” wani ra’ayi ne na Sinawa. Sin da Afirka aminai ne a ko da yaushe wadanda ke amincewa da juna, ganin yadda Sin ta taimaka wa Afirka wajen shimfida layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya, da layin dogo mai saurin tafiya a tsakanin Addis Ababa da Djibouti, da ma tsakanin Mombasa da Nairobi, da samar da taimakon agaji ga yammacin Afirka wajen yaki da cutar Ebola, da tura jiragen ruwan yaki zuwa mashigin teku na Aden da fadin teku na Somaliya don ba da kariya ga jiragen ruwa. Ba shakka taron koli na Beijing na FOCAC da zai gudana zai raya wata makoma mai haske ga bangarorin biyu. (Bello Wang / Kande Gao)
Advertisement

labarai