Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Sharhi: Pompeo Dan Siyasa Ne Maras Dattaku

Published

on

Kwanan baya, shafin yanar gizo na Politico na kasar Amurka ya soki sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Mike Pompeo, inda ya ce “Pompeo ba shi da kwarewar shugabanci ko kadan, sa’an nan yana kokarin yin amfani da cutar COVID-19 wajen takalar wasu kasashe, musamman ma Sin da Iran, lamarin da ya raunana hadin gwiwar da ake yi wajen dakile yaduwar cutar a duniya.”

A sha yiwa jami’in irin wannan suka, domin ’yan kasar ba su yarda da wasu abubuwan da mista Pompeo ya yi ba. Misali, tun bayan barkewar cutar COVID-19 a kasar Amurka, mista Pompeo bai dauki wani mataki da ya dace game da aikin hana yaduwar cutar ba, maimakon haka, sai ya rika kokarin shafa wa kasar Sin bakin fenti. Ban da haka, mista Pompeo ya yi ikirarin cewa, kasar Amurka watakila ba za ta maido da tallafin da ya kamata kasar ta baiwa hukumar lafiya ta duniya WHO ba. Ko da yake, jami’in na ci gaba da takama cewa, kasar Amurka za ta zama mai jagorantar aikin dakile cutar COVID-19 a duniya.

Hakika abubuwan da mista Pompeo ya yi sun nuna cewa, rayukan jama’ar kasar Amurka bai dame shi ba, abin da ke gabansa shi ne, neman kitsa makarkashiyar siyasa don biyan bukatar kashin kansa. (Bello Wang)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: