Daga CRI Hausa
Kwanan nan ne kasar Amurka da sauran wasu kasashen yammacin duniya sun yi ta yunkurin yada jita-jita gami da shafa ma gwanatin kasar Sin bakin fenti kan jihar Xinjiang, ta hanyar yada labarin bogi, wai Sin na yin wa ‘yan kabilar Uygur kisan kiyashi, a kokarin matsawa kasar Sin lamba. Game da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya musunta jita-jitar a yayin taron namena labaran da aka kira a kwanan baya, tare da bayyana cewa, wasu ‘yan siyasa na kasashen yammacin duniya sun fi yarda da karyar da wasu mutane suke yi, a maimakon yarda da kalaman al’ummar ‘yan kabilu daban daban miliyan 25 da ke jihar Xinjiang. Sun fi son hada baki tare da masu kin jinin kasar Sin, a maimakon amincewa da sahihin ci gaban da jihar Xinjiang ta samu. Lamarin da ya shaida cewa, ba su lura da abubuwa na zahiri dake faruwa, sai siyasa kawai, suna yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake samu a jihar Xinjiang da ma ci gaban kasar Sin, ta hanyar fakewa da batun Xinjiang da suka kitsa.
Game da batun “kisan kiyashi”, Minista Wang Yi ya ce, za a iya tuna al’ummar Amurkawa ‘yan asalin Indiya a karni na 16, da ‘yan kasashen Afirka da aka maida su bayi a karni na 19, da kuma al’ummar Yahudawa a karni na 20, har ma da ‘yan asalin Australiya wadanda har yanzu suke ta gwagwarmayar rayuwa. Abin da aka yi musu shi ne kisan kiyashi. Wa ya yi hakan? Kowa ya san cewa, Birtaniya da Amurka ne suka kashe al’ummar Amurkawa ‘yan asalin Indiya, kana ba a iya raba batun kisan bayi ‘yan Afirka da kasashen yammacin Turai da Amurka ba. Wa ya kashe al’ummar Yahudawa kuma? Kasar Jamus ce. Kasar Australiya kuma ita ce ta yiwa ‘yan asalin Australiya kisan kiyashi.
Duk wadannan kasashe,suke kan gaba wajen kawo cikas ga kasar Sin bisa hijjar batun Xinjiang. Ko wanensu ya taba yin kisan kiyashi. Sabo da marasa kunya ne, shi ya sa suke zaton cewa, wai tabbas kasar Sin ita ma ta aikata mummunan abu kamar su.
Amma a jihar Xinjiang ta kasar Sin, a shekaru sama da 40 da suka gabata, adadin ‘yan kabilar Uygur ya karu daga miliyan 5.55 zuwa sama da miliyan 12. A cikin shekaru sama da 60 da suka gabata, jimillar tattalin arzikin Xinjiang, ya karu sama da sau 200, kana, matsakaicin tsawon shekarun mutanen jihar ya karu daga shekaru 30 zuwa 72.
Minista Wang Yi ya ambaci wani littafi mai suna “Kawo karshen labaran bogi game da kabilar Uygur”da Maxime Vivas, wani marubuci dan kasar Faransa ya rubuta, inda ya bayyana sahihin jihar Xinjiantg mai wadata da zaman karko da ya ganam na idanunsa, bayan da ya ziyarci jihar har sau biyu. A cikin littafin, Vivas ya nuna cewa, Wadanda ba su taba zuwa jihar Xinjiang su ne ke watsa labaran bogi da ma yada jita-jita.
Hausawa kan ce, gani da ido maganin tambaya. A gaskiya ana jinjinta wa yadda Malam Vivas ke kiyaye adalci. Amma a sa’i daya kuma, ana damuwa kan makomarsa a nan gaba. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da a kwanan baya, wani marubuci dan kasar Faransa na daban wato Farfesa Christian Meistre ya gamu da babbar matsala sakamakon amincewar da ya nuna wa manufar yaki da ta’addanci da ake aiwatar a jihar Xinjiang.
Shekaru biyu da suka gabata, wannan marubucin ya ziyarci jihar Xinjiang, inda ya darajanta wasu matakan da kasar Sin ta dauka don yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, har ma yana ganin cewa, ya kamata Faransa ta koyi wasu dabarun yaki da ta’addanci daga wajen kasar Sin. Wadannan kalamai na Farfesa Christian Meistre sun bata ran wasu. Har ma wani dan jarida na kasar Faransa ya sake maimata kalaman farfesar, lamarin da ya tunzura wani gungu na Faransawa masu kyamar Sin, har ta kai su ga tursasa shaihun malamin ya yi ritaya daga aiki.
A kasashen Turai da Amurka, Nuna kin jinin kasar Sin ya zama tamkar hanya ce mai dacewa a siyasance, wanda ya soki kasar Sin zai samu goyon baya, amma wanda ke son fadin gaskiya game da kasar Sin, zai gamu da mummunan suka.
Masu nazari na nuna cewa, bayan yakin cacar baki, an kau da ra’ayin McCarthyism da ke nuna kin jinin Kwaminisanci sosai. Amma har yanzu wasu ‘yan siyasa na yammacin duniya na da irin wannan ra’ayin, ba sa son ganin ci gaba da wadatar kasar Sin. Yadda kasar Sin ke samun saurin bunkasuwa ya dame su sosai, har ma suna yunkurin kawo cikas ga ci gaban Sin daga dukkan fannoni.
Yanzu duk duniya na samun bunkasuwa cikin lumana, ra’ayin McCarthyism bai dace da wannan zamanin ba. Idan wadancan ‘yan siyasar yammacin duniya na son sake bin wannan ra’ayin, to tabbas za su dandana kudarsu.(Kande Gao daga sashen Hausa na CRI)