Sharhin Fim Dim ‘Gida Uku’

Suna: Gida Uku

Tsara Labari: Fauziyya D. Sulaiman

Kamfani: S. Fulani Production

Shiryawa: Nazir Dan Hajiya

Umarni: Ali Gumzak

Jarumai: Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Maryam Yahya, Asiya Ahmad, Saifullahi S. Fulani, Nasir Bello Naba, Hajara Usman, Asma’u Sani, Maryam Ceeta, Masa’uda Ibrahim, Safwan Baba Hasin, Mariya Baba Hasin da sauransu.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

 

A farkon fim din an nuna Abdul (Ali Nuhu) ya fito cikin shirin komawa wajen aikin sa da ke can jihar Lagos, yayin da matar sa Zainab (Asiya Ahmad) ta biyo shi, don yi ma sa rakiya ta na korafin yawan tafiye tafiyen sa da kuma rashin son zama cikin iyalan sa, hakan ya sa Abdul yin fushi har yayi burgar fasa tafiya amma sai Zainab ta lallaba shi ya tafi.

Sai dai kuma bayan tafiyar Abdul bai zarce ko ina ba sai wajen wata karuwar sa Zee Baby (Masa’uda Ibrahim) wadda suke holewa tare, su ka wuce hotel ita da Abdul su ka yada zango a can. Yayin da a bangaren Sadiya (Maryam Yahya) wato kanwar Abdul wadda ke auren Kamal (Saifullahi S. Fulani) wanda mahaifiyar sa ta hado kayanta daga ainahin gidan ta ta dawo gidan dan ta Kamal da sunan zama tare dasu, hakan bai yiwa Sadiya dadi ba domin uwar mijin nata Hajiya (Hajara Usman) sam bata kaunar ta saboda ganin bata haihu ba, wulakancin yau daban na gobe daban, wannan dalilin ne ya sa daga Sadiya har mijinta Kamal basuyi murna da dawowar Hajiya gidan ba.

Yayin da a bangaren abokin Kamal (Nasir Bello Naba) shi kuma matar shi wadda ke dauke da tsohon ciki ta kasance me tsananin kazanta da rashin iya magana, abokin Kamal sam bayajin dadin zama da matar tasa domin tun bayan da ta samu juna biyu ko girki ba ta son yi, hakan ne yasa mijin nata yake fatan ina ma ace bata samu juna biyun ba, yayin da Kamal ya ke nuna ma sa shi ya so a ce matar shi Sadiya ce ke dauke da juna biyun haka da ya fi kowa farin ciki domin mahaifiyar sa za ta kyale sa su zauna lafiya. Domin halin mahaifiyar Kamal ne ya sa Sadiya har fushi ta yi ta bar gidan mijin nata ta koma gidan yayanta Abdul, sai dai kuma Zainab matar Abdul ta rarrashe ta gami da nuna mata kowa hakuri ya ke a gidan sa, a karshe ta nemo Kamal ta sasanta abin Sadiya ta koma dakinta, amma bayan komawarta sai mahaifiyarsa ta nuna Sadiya ta kasa zama a gidan su saboda rashin cima mai dadi.

Haka Sadiya ta cigaba da hakuri da halin surikar ta, yayin da ita kuma Zainab matar Abdul ta soma kosawa da halin mijinta saboda takan dau tsahon watanni bai zo inda ta ke da ‘ya’yanta biyu ba, wannan dalilin ne ya sa ta kai kukan ta wajen wata tsohuwar kawar ta ‘yar duniya wato Asabe (Teema Makamashi) yayin da Asabe ta tabbatar mata da cewar mijinta neman mata ya ke don haka itama ta fada cikin bariki don kawar da matsalolin gaban ta, jin hakan ne ya sa Zainab ta yi fushi ba ta dauki shawarar Asabe ba su ka rabu.

Yayin da shi kuma Abdul wata tafiyar gaggawa zuwa Lagos wajen aikinsa ta kama shi, hakan ya sa ya bar Zee Baby a dakinsa na hotel da ya kama mu su, ya gargade ta a kan kada ta je ko’ina har zuwa lokacin da zai je ya dawo, sai dai kuma bayan tafiyar sa sai Zee ta fara kawo maza cikin dakin ta suna holewa, har tsautsayi ya sa Abdul ya dawo ya rutsa ta da gardi a cikin daki daya, nan fa ya kori gardin sannan ita kuma Zee yayi mata duka wanda bayan komawar sa gida wajen matar sa Zainab, sai Zee ta debo masa ‘yan sanda su ka zo su ka tafi da shi, bayan rabuwar Abdul da ‘yan sanda ne wani abokinsa (Baballe Hayatu) ya ba shi shawarar ya sauya salon bariki, hakan ya sa ya dauke shi ya kai shi wajen Asabe wadda ta yi alkawarin nemo mishi kyakykyawar mace, a sannan ne Asabe tayi nasarar shawo kan Zainab wadda ta amince zata yi bariki don fita daga halin da mijinta ya jefa ta a ciki.

Bayan Zainab ta biyo Asabe sun tafi hotel din da zasu hadu da wanda zasuyi fasikanci ne sai kwatsam Zainab taga mijinta Abdul ya shigo dakin a matsayin wanda aka hada ta dashi, nan ta firgita wanda a karshe ta bukaci ya bata takaddar saki, shi kuma Abdul ya nemi gafarar ta ya nuna ya daina bariki sannan suka koma suka zauna lafiya shi da matar sa Zainab.

Yayin da ita kuma mahaifiyar Kamal ta dage akan sai Kamal ya saki matar sa saboda wani dalilin nata na daban, sai gashi kuma bayan ya saketa ya kwanta ciwo a dalilin zuciyar sa da ta kumbura. Kuma a sannan ne matar sa Sadiya aka tabbatar da ta samu juna biyu,  hakan ne yasa mahaifiyar Kamal tayi nadamar cuzgunawa dan ta Kamal tare da matar sa Sadiya, a karshe itama tayi nadama ta nemi gafarar su.

 

Abubuwan Birgewa:

1- Sunan fim din ya dace da Labarin wato “Gida Uku” domin an tabo matsalolin gidajen gami da kawo gyara a zamantakewar mutanen dake cikin gidajen.

2- Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa, kuma anyi nasarar rike me kallo sannan kuma labarin har ya dire bai karye ba.

3- Anyi kokarin samar da wuraren da suka dace da labarin.

4- Hoto ya fita radau, haka ma sauti ba laifi.

5- Daraktan yayi kokari wajen nuna kwarewar sa wajen ganin labarin ya tafi yadda ya dace ba tare da ya karye ba, haka kuma yayi kokari wajen ganin cewar jaruman sun yi abinda ya kamata, domin jaruman sun taka rawar da ta dace.

 

Kurakurai:

1- Lokacin sa Zainab (Asiya Ahmad) ta hangi wucewar motar mijin ta akan titi, me kallo yaga lokacin da ta kira wayar mijin nata inda take sanar dashi taga kamar motar sa akan titin Tal’udu. Sai dai kuma titin da aka nuna ba titin Tal’udu bane kamar yadda Zainab ta ambata, ya dace a samar da zahirin abinda mai kallo zai gamsu da abinda Zainab din ta fada.

2- Shin wane irin aiki Kamal (Saifullahi S. Fulani) yake yi? An nuna shi mutum mai wadata wanda yake cikin gidan sa na kan sa, ga mota da sauran wasu abubuwa irin na more rayuwa, sai dai kuma ko sau daya ba’a nuna yaje aiki ko kuma ya dawo daga wajen aikin ba. Ya dace ko da baki ne a bayyana irin sana’ar da yake yi a cikin fim din.

3- Lokacin da Kamal yaje gidan abokin sa (Nasir Naba) me kallo yaga lokacin da Zainab ta kira sa don sanar masa cewar matar sa Sadiya ta baro gidan sa ta koma gidan wanta, me kallo yaji sa’in da Kamal ya daga wayar ya ambaci matar wan Sadiya da suna Anti Zilai a madadin Anti Zainab, shin manta sunan nata yayi?

4- Shin Zainab bata da kowa ne a tsakanin dangi da iyaye? Ko sau daya ba’a nuna wani daga cikin dangin ta ya ziyarce ta ba, musamman lokacin da take fuskantar matsalar rashin samun kulawa daga wajen mijinta Abdul, ya dace kafin ta fara neman shawarar tsohuwar kawar ta Asabe ‘yar duniya, a fara ganin ta nemi shawarar wani daga cikin dangi ko kuma kawa ta gari, idan matsalar tata bata gyaru ba a sannan sai a nuna tabi gurbatacciyar hanyar neman shawara ta hanyar zuwa wajen ‘yar duniya Asabe, tun da an fada a baki cewa ta gujewa Asabe saboda ganin ba mace bace ta gari, to bai dace kuma aga ta fara zuwa wajen ta a karon farko da sunan neman shawara ba.

 

Karkarewa:

Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa, sannan kuma fim din yayi nasara wajen fito da wasu matsaloli wadanda suka shafi zamantakewar aure, tare da kawo gyara a cikin lamarin. Wallahu a’alamu!

Exit mobile version