Hamza Gambo Umar" />

Sharhin Fim Din ‘Akushi’

Suna: Akushi
Tsara Labari: Abdullahi Amdaz
Kamfani: Oscar International
Shiryawa: Nazir Dan Hajiya
Umarni: Sunusi Oscar 442
Jarumai: Ali Nuhu, Hadiza Gabon, Garzali Miko, Hassana Muhammad, Asma’u Sani, Zulaihat Ibrahim, Hamza Indabawa, Shamsu Dan Iya, Baba Karami da sauransu.

A farkon fim din an nuna Shahid (Garzali Miko) zaune a gaban iyayen sa suna rarrashin sa akan rashin masoyiyar sa Husna wadda ta rasu. Yayin da kuma daga baya ya shiga jami’a ya soma karatu, sai dai kuma anan ya soma firgita saboda tunanin masoyiyar sa Husna har takai idan yaga mace yakan tare ta da zaton masoyiyar sa Husna ya gani, yayin da a bangaren wata ‘yar uwar sa Nusaiba (Zulaihat Ibrahim) ita kuma take tsananin son Shahid wanda har hakan takai tana zuwa gidan su tayi masa wanki da wasu ayyukan don ganin ta sace zuciyar sa amma hakan ba ta samuwa domin sam Shahid yaki amincewa da soyayyar ta saboda a kowane lokaci yana ganin masoyiyar sa Husna da ta rasu zata dawo.
A bangare guda kuma Mahfuz (Shamsu Dan Iya) wanda ke zaune a gidan dan uwansa (Ali Nuhu) ya kasance mutum ne mai neman fitina gami da son jan rigima, sau da yawa idan Mahfuz yaje wajen wani taron sai an yi rigima dashi saboda mugun halin sa a wasu lokutan ma har akan Santana matsalar da ofishin ‘yan sanda, hakan sam ba ya yiwa budurwar sa Amira dadi (Hassana Muhammad) wadda suke zaune a cikin gida daya, burin ta a kullum bai wuce Mahfuz ya nutsu don su cigaba da gudanar da soyayyar su har zuwa lokacin da zasuyi aure.
Tsananin son da Amira take yiwa Mahfuz ne yasa ko tayi fushi dashi take saurin saukowa, domin akwai lokacin da ta tarar yana waya da wata budurwar sa har yana kushe Amirar a wajen waccan budurwar tasa, hakan yasa Amira tayi fushi musamman da Mahfuz ya nuna mata cewar yayi Haka ne don ya samu wasu ‘yan kudi a wajen waccan budurwar tasa. Halayyar Mahfuz mara kyau ce tasa Nusaiba take fatan ganin ranar da saurayin ta Shahid zai soma rama irin cin fuskar da yake masa a makaranta, amma sam shi Shahid halayyar Mahfuz bata sameshi ba.
Ganin yadda Nusaiba take nuna kulawar ta ga Shahid ne yasa yadan fara bata lokacin sa suna soyayya saboda jin alkawarin da tayi masa na fitar dashi daga halin rashin masoyiyar sa Amira. Sai dai kwatsam kuma wata rana Shahid suna tare da Nusaiba sai ga Amira ta wuce ta gaban sa, ganin ta ne yaga sak bata da bambanci da budurwar sa Amira wadda ta rasu hakan yasa yabi bayan ta yana kiran ta sai dai kuma tun kafin ya karasa Mahfuz ya tare sa yana gargadin sa akan wani laifin.
Bayan komawar Shahid gida ne yake bawa mahaifiyar sa (Asma’u Sani) labarin cewar yaga masoyiyar sa Husna wadda ta rasu, amma sai ta kasa gasgata hakan gami da yi masa gargadi don gudun kada kwakwalwar sa ta tabu. Gain bata amince bane yasa Shahid ya tafi gidan iyayen Husna ya sanar dasu cewar yaga Husna da zaton ko za a yarda dashi, amma mahaifin Husna (Baba Karami) bai kula sa ba ya bar shi a wajen.
Hankalin Shahid ya tashi ganin ya cigaba da haduwa da Amira a makaranta wadda yake zargin cewa Husna din sa ce wadda ta rasu, yayin da itama Amira ganin irin nacin da yake yi mata na sai ta kula shi har ta soma jin tausayin sa, sai dai kuma daga karshe Shahid ya rutsa Amira da fada akan lallai itace budurwar sa in kuma ba ita bace sai ta fada masa yadda akayi suke kama da juna, anan ne rigima ta kaure tsakanin sa da Mahfuz saurayin Amira wanda hakan ya dangana da ofishin Head Of Department na makaranta da suke. A can ne da aka taru gaba daya sai aka gano gaskiyar cewa Amira ‘yar uwa ce ga Husna kuma tagwaye ne wanda bayan an haife su sai kishiyar mahaifiyar su ta sa aka sace Hasanar wato Amira, dalilin hakan ne ya zamo silar zamanta a wajen wanda take zaton shine dan uwan mahaifinta (Ali Nuhu) yayin da a karshe kishiyar mahaifiyar su Amira wadda duk ta hada makircin ta haukace.

Abubuwan Birgewa:
1- Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa.
2- Hoto ya fita radau, Haka kuma anyi kokari sosai wajen nuna salon daukar hoton fim din.
3- Daraktan yayi kokari wajen ganin fim din ya tafi yadda ya dace, haka kuma yayi kokarin ganin cewa jaruman sun isar da sakon da ake bukata, domin sun taka rawar da ta dace.
4- Wakokin fim din sun nishadantar
Kurakurai:
1- Lokacin da aka fara nuna Shahid (Garzali Miko) zaune a harabar makaranta suna hira da abokin sa, me kallo yaga wasu ‘yan mata sun wuce ta bayan kujerar su Shahid, amma bayan giftwar su sai ya juyo a firgice ya nufo su yana ambaton sunan budurwar sa, sai dai kuma yanayin yadda ‘yan matan suka wuce ta bayan Shahid hakan bai nuna alamun cewar Shahid ya gan su ba, kuma juyowar sa tafi kama da ta wanda yasan dama zasu wuce, ya dace a nuna alamun da zai tabbatar da cewar Shahid ya gan su ko da ta hanyar jin muryar su ko kuma a nuna sun gifta ta gaban sa ne ba ta bayan sa ba.
2- Wakoki sun yi rambatsau da yawa a film din, domin wasu ma basu samu kyakykyawan gurbi ba.
3- An nuna Shahid yana shirye-shiryen auren Husna kafin rasuwar ta, sai dai kuma har a sannan ba’a nuna sana’ar da yake yi wadda zai rike kansa da matar sa ba, tunda kuma ba’a nuna cewar iyayen sa ne za su dau nauyin auren sa ba, to ya dace ko a baki ne a fadi wata sana’a da yake wadda zai rike iyalin nasa da ita.
4- Shin wane dalilin ne yasa mahaifin Husna (Baba Karami) yaki amincewa da auren ta da Shahid? Ya dace a bayyana dalilin da yasa yaki amincewa da auren, domin komai yana da dalilin sa.
5- Bayan Shahid ya gane cewar Amira ‘yar uwar Husna ce, shin Mahfuz zai hakura da Amira ne ya bar wa Shahid? Sannan kuma meye makomar soyayyar da Nusaiba take yiwa Shahid? Su biyun zai hada ya aura ko kuma hakura zai yi da ita? Ya dace a warwarewa me kallo zaren da aka tufka.
Karkarewa:
Labarin ya fadakar domin an nuna illar makircin wasu kishiyoyin da karshen masu hali irin nasu a duniya. Sai dai kuma fim din ya kare tun labarin bai gama direwa ba, domin akwai abubuwan da ba’a karkare su ba. Wallahu a’alamu!

Exit mobile version