Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Amatullah’

Published

on

Suna: Amatullah.

Tsara labari: Ibrahim Birniwa.
Kamfani: FAMLI Inbestment Ltd.
Daukar Nauyi: Abubukar Tukuntawa .
Shiryawa: Sani Mai Iyali.
Bada Umarni: Ali Gumzak Sak.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Sadik Sani Sadik, Shehu Hassan Kano, Hadiza Muhammad, Mustapha Naburuska, Fiddausi Muhammad, Garzali Miko, Umar Gombe, Ilyasu Tantiri, Kazaza, Yusuf Sasin da sauransu.
Fim din “Amatullah” fim ne da a ka gina shi a kan labarin wata budurwa mai Suna Amatullah (Fiddausi Muhammad) wadda ta kasance mai tarbiya da hankali, kowa da kowa na yabonta a kan wannan kyakkyawar dabi’ar tata. Sai dai kash rayuwarta ta zo da rudani a karshe bayan an samu gawarta a cikin wani Otel. Wanda wannan yanayi ya saka iyayenta wato (Shehu Hassan Kano) da kuma (Hadiza Muhammad) cikin wani mawiyacin hali.
Ita dai Amatullah an samu gawarta ne a cikin wani Otel, bayan mai yin share-share a otel din ya shiga dakin da take kawai sai ya ga gawarta a kasa a kwance. Nan take ya yi sauri ya sanar da manajan wannan otel din inda a lokacin a ka sanar da ‘yan sanda, domin su zo su gudanar da bincike a kan gawar.
A daya bangaren kuma, mahaifin Amatullah ya kafe a kan sam shi ba za a yi wa Amatullah sutura a gidansa ba. Saboda a cewarsa ba yadda za a yi ace ‘yarsa ta mutu a Otel, don haka shi Amatullah yanzu ba ‘yarsa bace. Haka dai a kai ta bashi baki a kan cewa ya daure ya bari a yi mata sutura a gidan tunda bata da wani gida da ya wuce nan din. Bayan doguwar muhawara ne dai, Alhajin ya amince da a shiga a yi mata suturar bayan limamin garin ya tilasta shi a kan sai ya bari an yi mata sutura a gidan.
A haka dai aka binne Amatullah cikin wannan yanayi na rudani, wanda da yawan mutane su ka kasa gamsuwa a kan yanayin mutuwarta. Saboda kowa yasan irin dabiunta amma kuma sai gashi ta yi wata mutuwa ta ban mamaki, wanda gaba daya mutane ba su yi mata zaton irin wannan mutuwar ba. Sai dai a na ta bangaren, mahaifiyar Amatullah kullum tana addu’ar Allah ya kawo wata hanyar da za a wanke Amatullah bisa zargin da ake mata akan mutuwarta. Ita dai mahaifiyarta kodayaushe tana kyautata mata zato, kuma ta san Amatullah ba za ta taba zuwa Otel don aikata wata barna ba. Amma duk da haka ta kasa samun sukuni saboda rudanin da mutuwar ta zo da shi.
Sai dai a karshe an samu wasu dalilai guda biyu da suka dan wanke zargin da a ke yi wa Amatullah. Na farko maganar kudi da kawar Amatullah ta ji tana cewa za ta zo amma sai dai idan za a bata dubu dari biyu, inda wani abokin yayanta ya zo ya sanar da cewa ai da shi su ke waya a kan yana so ta zo ta ringa koyawa matarsa karatun Al-kurani, shi ne ta ke fada masa ba za ta zo ba sai ya biya kudi dubu dari biyu. Sannan maganar mutuwarta a Otel kuma, shi ma wani makocinsu ya zo ya bayyana cewa ai wani abokinsa ne saurayinta shi ne ya yaudare ta har ya kirawo ta Otel. Amma lokacin da ta zo da ta fahimci cewa yana so ya keta mata haddi ne, shi ne fa ta ki amincewa da shi har garin kokawa ya ture ta gefe, kuma a nan ne tana faduwa ai kuwa sai ta fadi a mace.
Bayan wannan bayanai sun fita ne, sai hankalin iyayen Amatullah ya kwanta da kuma na sauran jama’ar gari wadanda suke mata kyakkyawan zato. Inda kuma nan da nan ‘yan sanda su ka yi umarnin a je a kamo wannan saurayin nata wato (Garzali Miko) domin a hukunta shi dai-dai da abinda ya aikata.
Abubuwan Yabawa
Sunan fim din ya dace da labarin.
An samu aiki mai kyau a cikin fim din.
Hotuna da sauti sun fita radau.
Jarumai sun taka rawa sosai a ciki.
An nuna tasirin kyakkyawar dabi’a gurun samun shaida ta gari a gurun jama’a.
Kurakurai
Yadda a ka fara ginin labarin sam ba zai gamsar da mai kallo ba. Saboda ya kamata a ce an nuna rayuwar Amatullah a gida kafin mutuwarta, domin mai kallo ya tabbatarwa da kansa kyakkyawar dabi’ar da a ke so a nuna masa tana da ita.
Hujjojin da aka bayar domin wanke Amatullah, sam-sam ba su da karfin da za su wanke zargin da a ke yi mata, domin hujjoji ne da za iya kirkirar su. saboda ba hujjoji bane na zahiri da kowa zai gamsu da su.
A yadda a ka nuna irin kyawawan halayen Amatullah, bai kamata a ce cikin kankanin lokaci har an rinjaye ta ta yarda ta je gurun saurayi a Otel ba.
Ya kamata a ce an bayyana kama saurayin da a ke zargi da kisan Amatullah, domin a hukunta shi dai-dai da abinda ya aikata.
Ya kamata ace an bayyana kokarin ‘yan sanda wajen gane gaskiyar lamarin kisar, amma ko sau daya ba a nuno ‘yan sanda sun zo gidansu Amatullah dan neman wani karin bayani a kan kisan ba.
Labarin bai samu tsari mai kyau ba. Ya kamata a ce an tsara shi ta yadda zai tafi a tsare ba tare da yankewa ba tun daga farko har karshe. Ta yadda duk wanda ya kalla zai gane sakon da a ke so a isar masa ba tare da wata gargada ba.
karkarewa
Fim din Amatullah ya yi kokarin bayyyana yadda kyakkyawar dabi’ar Amatullah ta janyo mata kyakkyawr shaida a gurun iyayenta da kuma mutanen unguwa. Duk da cewa mutuwarta ta zo da wani irin yanayi mai rikitarwa, amma hakan bai sa kyakkyawan yabon da a ke mata ya dusashe ba. Sannan an yi kokarin nuna tasirin bawa ya zama na Allah, to tabbas Allah ba zai tozarta shi ba a lokacin rayuwarsa ko bayan mutuwarsa. Duk da cewa fim din ya samu matsaloli da kurakurai a cikinsa, amma duk da hakan ya samu nasarar isar da muhimmin sakon da ya ke son isarwa. Sannan ya na da kyau masu ruwa da tsaki a harkar fina-finai musamman masu tsara labari da masu shiryawa, da su ringa mai da hankali gurun tsara da kuma shirya labari ta yadda zai isar da sakon da a ke so ya isar cikin nasara zuwa ga masu kallo.
Advertisement

labarai