Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘ANGO’

Published

on

Suna: Ango.

Tsara labari: Kaddafi Mai Addu’a.
Kamfani: Sultan Films Factory.
Daukar Nauyi: Sultan Abdurrazak.
Shiryawa: Abba Kabugawa.
Bada Umarni: Hassan Ali Muhammad.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Adam A. Zango, Sultan Abdurrazak, Rabi’u Rikadawa, Balarabe Jaji, Salisu Sase, Salisu S. Fulani, Aisha Aliyu Tsamiya, Momy Gombe, Aisha NTA da sauransu.

Fim din Ango fim ne da a ka yi shi a kan labarin wani Ango mai suna Ammar(Adam A. Zango), wanda ya samu kansa cikin wani mawiyacin hali a cikin kasa da minti talatin bayan kawo masa sabuwar amaryarsa mai suna Sadiya (Momy Gombe) gidansa. Bayan ‘yan rakiya sun watse ne Kuma, sai ya shiga bandaki domin yin alola, fitowarsa ke da wuya kawai sai ya zo ya same ta kwance cikin jini an yankata. Nan take kuwa sai ya rikice ya kama sumbatu shi kadai. Daga nan sai ya kirawo amininsa Haidar (Salisu S. Fulani), ya shaida masa abunda ya ke faruwa.

Shi kuma a nashi bangaren, mahaifin Sadiya wato Alhaji (Rabi’u Rikadawa) tuni ya nemo ‘yan sanda su ka kama Ammar, ya na ikirarin yadda ya kashe masa ‘yarsa to shi ma dole sai an kashe shi. Abu kamar wasa dai, har magana ta je kotu, kuma a ka saka ranar da za a fara zama domin sauraren shari’ar.

A na nan rana ta zo a ka fara shari’a. Sai dai shari’ar ta zo da abun mamaki, domin kuwa a karshe ta tabbatar da Nuratu (Aisha Tsamiya) wato Kanwa ga Ammar a matsayin wadda ta kashe Sadiya, kamar yadda ta tabbatar da kanta a gaban kotu. Ita dai Nuratu ‘ya ce a gurun kanin Hajiyar Ammar. A nan gidansu ta girma, kuma ta yi ta dakon soyayyar Ammar tsahon lokaci, amma ba tare da ta sanar da shi halin da ta ke ciki ba. A na cikin hakan ne, sai watarana Ammar ya kawo Sadiya gida ta gaida Hajiya sannan ta gan ta domin ita ce wadda zai aura. Zuwan Sadiya ya tayar wa da Nuratu hankali, kuma tun daga wannan lokacin ne ta kuduri niyar hallaka Sadiya tunda ta raba ta da burinta. Wanda hakan ya sa ta bita har gida ta yankata a ranar da ta tare a matsayin amarya.

A karshe dai, bayan Nuratu ta amsa laifinta da kanta a kotu, sai Alkali ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya. Sannan kuma kotu ta wanke Ammar daga zargin da a ke yi masa.

ABUBUWAN YABAWA

  1. Fim din ya samu aiki mai kyau domin labarin ya tsaru yadda ya kamata.
  2. Sunan fim din ya dace da labarinsa.
  3. Sauti ya fito rangadadau.
  4. Hotuna sun fita sosai, babu duhu ko dishi-dishi.
  5. Dukkanin jaruman fim din sun dace da guraben da a ka dora su.

KURAKURAI

  1. A lokacin da Nuratu ta yanka Sadiya, ko kadan ba a nuna alamar jini a wuyan Sadiyar ko jikin wukar ba. Har Sadiya ta fadi a kwance ba jini a wuyanta kuma babu a jikin wukar da a ka yanka ta.
  2. A cikin fim din kaf ba a nuna ta ya ya Nuratu ta fita daga gidan Ammar ba, bayan ta yanka Sadiya.
  3. Tunda Nuratu ce ta ke bada labarin soyayyar Ammar da Sadiya a kotu, to bai kamata a saka wakar da a ka nuno Ammar su na yi da Sadiya a cikin labarin na Nuratun ba.

KARKAREWA

Fim din “Ango” fim ne da ya samu aiki mai kyau. Fim din ya samu nasarar isar da sakon da a ke da burin isarwa. Hakika fim din Ango, na daya daga cikin fina-finan da su ka haskaka kuma su ka samu karbuwa a wannan shekarar.
Advertisement

labarai