Musa Ishak Muhammad">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Auren Halliru’

by Musa Ishak Muhammad
September 13, 2020
in BIDIYO
2 min read
Sharhin Fim Din ‘Auren Halliru’
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Suna: Auren Halliru
Labari: B.M Shabbab.
Tsara Labari: B.M Shabbab.
Kamfani: Shabbab Production.
Daukar Nauyi: B.M Shabbab.
Shiryawa: Abban Hajiya.
Bada Umarni: Nura Mai Shabbabu.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Alhassan Kwalli, Ayatullahi Tage, Yusuf Abubakar Sheka, Abban Hajiya, Hajiya Duduwa, Saudat Muhammad, Ummi Ladan, Ummi Shattima, Hassina Muhammad da sauran su.
Fim din Auren Halliru fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani bawan Allah mai suna Halliru (Alhassan Kwalli), wanda ko kadan bai son aure. Ko da maganar aure a ka yi masa to babban bacin ransa kenan. A haka kullum mahaifiyarsa ke fama da shi a kan maganar aure amma ya ki sauraran ta. Kuma gashi ya tara shekaru masu yawa amma ko kadan bai da niyar auren. Ko da abokansa ma haka su ke fama da shi, kullum maganar da su ke yi masa kenan. Amma har cewa ya ke zai daina kula su idan su na yi masa maganar auren.
Da mahaifiyar Halliru ta ga dai da gaske ba auren nan ya ke so ya yi ba, sai ta ce masa ta ba shi sati biyu a kan lallai ya nemo wadda zai aura, idan kuwa ba haka ba za ta samo masa kowacce mace ta gadama ta aura masa. Ko da kuwa kuturwa ce ko makauniya ko gurguwa. Sai Halliru ya tafi wajen amininsa (Ayatullahi Tage) ya ke fada masa abunda mahaifiyarsa ta fada masa, sai ya bashi shawarar cewa koda ba zai yi auren ba, to ya daure ya fara zuwa zance, idan ya na zuwa zancen zai samu saukin matsin da ya ke samu, za a ce ai ya na da niyya tunda har zance ya ke zuwa.
A gefe daya, kanwar Halliru ta na nan ta na bibiyar kawayenta ko za a samu wadda za ta amince ta auri Halliru, amma kowacce sai ta ce ba za ta auri tsoho ba, ya je ya auri bazawara mana ga su nan sun cika gari ta ko’ina. A haka dai ita ma ta gama kokarinta amma ba ta samu nasarar samo ko guda daya ba.
To da wa’adin da mahaifiyar Halliru ta bashi ya cika bai samo matar ba, kawai sai ta je gidan yayanta ta nemo masa auren wata yarinya kamar mai aljanu. A haka dai a ka yi wa Halliru aure duk da ransa ba ya so kuma a kace dole ya zauna da ita. A haka ya zauna ba ya shiga dakinta kuma ba ya cin abincinta. Karshe dai ya yanke shawarar zai gudu ya bar ta a gidan.
ABUBUWAN YABAWA.
1. Fim din ya nuna illar kin yin aure a kan lokaci.
2. Fim din ya dace da sunan labarin fim din.
3. Labarin fim din bai yanke ba tun daga farko har karshe.
4. Fim din ya samu aiki mai kyau, babu matsalar hoto ko sauti.
KURAKURAI
1. Sakon da a ke so a isar zai yi wa mai kallo wahalar ganewa, duba da yadda fim din ya kare.
2. An ya kuwa ya na yiwu wa don kawai mutum ya ki aure da wuri mahaifiyarsa ta auro masa kowacce iriyar mace ko zai cutu?
3. Fim din bai kamata ya kare a inda a ka nuna ya kare ba.
KARKAREWA
Fim din Auren Halliru fim ne da ya samu aiki mai kyau. Kuma ya yi nasarar isar da sako mai muhimmanci ga al’umma. Nasarorin da fim din ya samu, ya fi kurakuren da ya samu yawa. Fatanmu dai shi ne a hada karfi da karfe wajen inganta wannan sana’a, da kuma zuwar wa masu kallo da abinda zai ilimantar da su ya kuma kayatar da su.

SendShareTweetShare
Previous Post

Mun Fahimci Juna Sosai Da Iyayena Kafin Na Fara Sana’ar Fim– Jaruma Teema Yola

Next Post

NDE Ta Horas Da Matasa 100 Hanyoyin Aikin Noma Na Zamani A Jihar Adamawa

RelatedPosts

Fim Din ‘ANGO’

Sharhin Fim Din ‘ANGO’

by Musa Ishak Muhammad
1 week ago
0

Suna: Ango. Tsara labari: Kaddafi Mai Addu'a. Kamfani: Sultan Films...

Sharhin Fim din ‘Yarda Da Amini’

Sharhin Fim din ‘Yarda Da Amini’

by Musa Ishak Muhammad
2 months ago
0

Suna: Yarda Da Amini. Kamfani: FASAHA Concept. Labari: Habibu Yaro....

‘Wani Labari’

Sharhin Fim Din ‘Wani Labari’

by Musa Ishak Muhammad
2 months ago
0

Suna: Wani Labari. Kamfani: MB ENTERTAINMENT. Labari: Yusha'u Idris. Tsara...

Next Post
Noman Dawa: An Tallafawa Manoman 36,000 Da Naira Biliyan Shida A Gombe

NDE Ta Horas Da Matasa 100 Hanyoyin Aikin Noma Na Zamani A Jihar Adamawa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version