Musa Ishak Muhammad" />

Sharhin Fim Din ‘Corona Birus’

Corona Birus

Suna: Corona Birus.

Tsara labari:  Nabil Salisu.

Kamfani: Girma Multimedia Inbestment Ltd.

Daukar Nauyi: Aliyu Muhammad Kowa Ya bi.

Shiryawa: Bashir Girma .

Bada Umarni: Babannan One Boy.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Sulaiman Bosho, Bashir Na Yaya, Bashir Girma, Baba Dan Yarbawa, H. Adam, Tusuf Jagwal, Hamisu Tumbudi, Hauwa Ali Bulama, Bilkisu M Ahmad, A’isha Mai Labbaika, da sauransu.

A farkon fim din an hasko Baushe (Bashir Na Yaya) dauke da bindigarsa ya na shirin tafiya daji. Daga nan kuma sai a ka hasko (Sulaiman Bosho) da shi da ‘ya’yansa a gida ya na jiyar rashin lafiya a gida, yayin da ‘ya’yansa su ka dauki wani magani su ka bashi, nan take kansa ya juye ya fara surutai. Da kyar dai su ka samu kansa.

Daga nan sai a ka hasko su (Sulaiman Bosho) a cikin mota su na shirin tafiya domin yin kasuwanci. Sannan su ka fara tattaunawa cewa a hanyar da su ke bi fa akwai barayi, shi ne su ka tsara cewa idan sun gamu da ‘yan fashi shi Bosho zai wuf ya kama daya daga cikinsu, su kuma sauran sai su zo su kama sauran. Bayan sun gamu da ‘yan fashin ne sai a ka yi kamar yadda a ka tsara. Bosho ya yi sauri ya shake daya daga cikinsu, maimakon sauran abokan tafiyar tasu su zo su kama sauran, kawai sai su ka gudu su ka bar shi. Sai ‘yan fashin su ka zo su ka kama shi, su ka tafi da shi daji.

Daga karshe- karshen fim din ne a ka fara hasko jaruman sun fara saka rigunan leda da kuma hular Kano, da niyar wai su na yaki da cutar Corona Birus.

Abubuwan Yabawa

  1. An samu sauti mai kyau a fim din.
  2. Hotuna ma ba laifi, sun dauku sosai.

Kurakurai

  1. Kwata-kwata fim din bai da alaka da sunansa.
  2. Fim din bai bayyana wani sako da ya danganci wannan cuta ba.
  3. Fim din ya rasa cikakken jigo guda daya.
  4. Labarin fim din bai tsaru ba.
  5. Fim din zai sa ka mai kallo cikin nazarin gano ainihin sakon da a ke da bukatar fim din ya isar.
  6. An samu kalamai da ba su dace ba daga bakin Sulaiman Bosho, a lokacin da ‘yan fashi su ka kama shi.

Karkarewa

Wannan fim na Corona Birus, kawai an kirawo shi ne da wannan suna, amma ko kadan bai da alaka da sunan. Kamata ya yi a cikin fim din, a zo da bayanai na ilimantarwa a kan wannan cuta ta Corona Birus. A na nunawa masu kallo yadda a kan iya kamuwa da cutar, da kuma nuna masu hanyoyin kare-kai daga cutar. Duk wanda ya ga sunan wannan fim, zai yi zaton duk abinda zai gani a ciki ya na da alaka ne da wannan cuta, amma sai ga shi lamarin bai kasance haka ba.

Da fatan masu ruwa da tsaki, za su tsaya tsayin-daka domin ganin a na zuwar ma su kallo da fina-finai masu ma’ana, domin a ringa gamsar da masu kallo.

Exit mobile version