Musa Ishak Muhammad">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Da Kamar Wuya’

by Musa Ishak Muhammad
October 11, 2020
in BIDIYO
3 min read
‘Da Kamar Wuya’
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Suna: Da Kamar Wuya.

Labari: Abdulkarim Isah.

samndaads

Tsara Labari: Abdulkarim Isah.

Kamfani: M.D Entertainment.

Shiryawa: Abdulkarim Isah

Bada Umarni: Muhammad Abubakar.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad

Jarumai: Sani Garba SK, Asama’u Nas, Sadik Ahmad, Ladidi Tubulas, Khadija Ahmad, Umar Khan, Rahama Isa, Sadiya Sulaiman, Abubakar Wizi da sauransu.

Fim din “Da Kamar Wuya” fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani matashi mai suna Abubakar. Shi dai Abubakar matashi ne mai son neman na kansa. Mahaifinsa ya rasu, daga shi sai mahaifiyarsa su ke rayuwa a gidansu. Wannan yanayin da ya samu kansa ne ya sa ko kadan ba ya wasa da sana’a domin ya rufawa kansa asiri ya kuma kula da mahaifiyarsa. Babu irin sana’ar da Abubakar ya ke rainawa, kowacce iri ta zo masa in dai zai samu ko ya ya ne to zai je ya yi ta. Ya na sayar da mai, ya na sayar da gurasa da sauran sana’o’in da ya ke gabatarwa.

A cikin sana’o’in da Abubakar ya ke yi ne, Allah ya hada shi da wata baiwar Allah mai suna Mero. Mero ‘yar masu kudi ce, domin haduwarsu ta farko ma da Abubakar, fetir ta je siya a wajensa za ta zuba a motarta. Ganin yadda Abubakar ya ke da kwazon neman na kansa ne ya sa Mero ta ji ta na son shi, kuma ta yi alkawarin taimakawa rayuwarsa. Mero ta samu ta budewa Abubakar wani katon shago na sayar da kayan kichin. Bayan ta bude masa wannan shagon ne kuma sai ta ke fada masa idan ya amince ta na so su yi aure. Bayan auren Abubakar da Mero, sai Mero ta sake sakarwa Abubakar dukkanin harkokinta ta dora shi a kai.

A farkon auren Abubakar ya rike amanar Mero, ya na kulawa da ita kuma ya na kulawa da dukiyarta da ta ke hannunsa. Amma daga baya sai mahaifiyarsa ta fara ba shi shawarwarin banza, ta na umartar sa da ya ringa cin kudaden nan, kawai ya ke yin yadda ya gadama da dukiyar. Ai kuwa Abubakar ya dauki wannan shawarar, ya lalata dukiyarta, sannan ya samo wata Hajiyar su ka ci-gaba da soyayya wai auren ta zai yi. Daga nan ne ya fara wulakanta Mero, wulakancin yau daban na gobe daban. Karshe ma bayan  daina zaman gidanta da ya yi, a karshe ma kawai sai ya sake ta saboda wai ta dame su, su kuma so su ke su tafi Dubai da shi da sabuwar Hajiyarsa.

Abubuwan Yabawa

  1. Fim din ya samu aiki mai kyau.
  2. Babu matsalar sauti ko hoto a cikin fim din.
  3. Labarin fim din bai yanke ba tun daga farko har karshe.
  4. An nuna illar cin amana.
  5. An nuna sakamakon son zuciya ba ya haifar da sakamako mai kyau.
  6. An nuna soyayya ta gaskiya tsakani da Allah kamar yadda Mero ta yi wa Abubakar.

Kurakurai

  1. Labarin fim din bai da ma’ana ta kai tsaye da sunan fim din.
  2. Ba a nuna mai ya raba Hajiya da Abubakar ba, kawai sai hasko shi a ka yi a kwance wai ba shi da lafiya.
  3. Ba a nuna yadda Nura su ka hadu da Mero ba, bayan dukansu sun rabu da aurensu na farko, kawai sai gani a ka yi sun kara yin aure, ba tare da an nunawa mai kallo silar haduwarsu ba.
  4. Halin da mahaifin matar Nura ya ringa nunawa game da ‘yarsa bai yi kama da abunda ya ke faruwa a gaske ba.

Karkarewa

Fim din “Da Kamar Wuya” fim ne da ya samu aiki mai kyau tare da nasarori masu yawa. Sai dai an dan samu wasu kurakurai kadan, amma ba za su rinjayi nasarorin da fim din ya samu ba. Fatanmu dai shi ne a kara Inganta aiki domin a ringa bawa mai kallo gamsuwa a abunda ya ke kalla.

SendShareTweetShare
Previous Post

Shugaban NIS Babandede Ya Samu Lambar Yabo A Kan Matakan Rigakafin Yaduwar Korona

Next Post

Wata Kungiya Ta Fara Fadakar Da Matasa Illolin Shaye-shaye

RelatedPosts

Fim Din ‘ANGO’

Sharhin Fim Din ‘ANGO’

by Musa Ishak Muhammad
1 week ago
0

Suna: Ango. Tsara labari: Kaddafi Mai Addu'a. Kamfani: Sultan Films...

Sharhin Fim din ‘Yarda Da Amini’

Sharhin Fim din ‘Yarda Da Amini’

by Musa Ishak Muhammad
2 months ago
0

Suna: Yarda Da Amini. Kamfani: FASAHA Concept. Labari: Habibu Yaro....

‘Wani Labari’

Sharhin Fim Din ‘Wani Labari’

by Musa Ishak Muhammad
2 months ago
0

Suna: Wani Labari. Kamfani: MB ENTERTAINMENT. Labari: Yusha'u Idris. Tsara...

Next Post
kwayoyi

Wata Kungiya Ta Fara Fadakar Da Matasa Illolin Shaye-shaye

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version