Sharhin Fim Din ‘Dan Marka’

Suna: Dan Marka

Tsara Labari: 50 Mai Kalangu

Kamfani: Dan Hajia Films Productions

Shiryawa: Ibrahim K.

Umarni: Sunusi Oscar 442

Jarumai: Sulaiman Yahya Bosho, Halima Atete, Garzali Miko, Amal Umar, Hassana Muhammad, Salisu S. Fulani, Hajara Usman, Danjuma Salisu, Saudat Umar. Da sauran su.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Alhaji Teku (Sulaiman Bosho) tsaye a gaban motarsa, yayin da wasu matasan kauyensu ka zo don gaisawa da shi amma sai ya nemi gayawa mahaifin su bakar magana, da su ka nuna rashin jin dadinsu a kan haka kuma sai ya sa yaron gidan sa ya raka su da duka.

Alhaji Teku ya kasance attajirin kauye wanda babu kamar sa a fannin dukiya domin an nuna kaf fadin kauyen shi kadai ne yake da motar hawa, hakan ne yasa ya zamo mutum mai jiji da kai wanda ba ya daukar raini a wajen kowa. Sai dai kuma duk yawan dukiyar tasa ba ta amfanar mutanen kauyen da komai, domin ba ya kyauta ko sadaka haka kuma a cikin gida ma bai wadata iyalan sa da dukiyar tasa ba, kuma mutum ne shi mai siya wa kansa raini, domin hatta daya daga cikin matansa ba ta ganin darajarsa (Halima Atete). Domin duk lokacin da rigima ta hado ta da kishiyar ta da zarar Alhaji Teku ya saka baki don neman sulhu a cikin rigimar haka ta ke yi ma sa zagin cin mutunci, wanda sanadin hakan ya sa Alhaji Teku ya sake ta.

Babbar matsalar Alhaji Teku ita ce, yawan son mata domin ya na da budurwar zuciya ba ya duba yawan shekarunsa, duk lokacin da ya kyallara ido ya ga mace musamman kananan yara ‘yan mata sai ya makale mu su ya dinga kashe musu kudi don su aure shi. A irin hakan ne ya raba Habu (Saifullahi S. Fulani) da budurwar sa wadda ta ke ikirarin cewar ta na kaunar sa, amma daga lokacin da Alhaji Teku ya sakar ma ta kudi sai ta guji saurayin ta wato Habu ta koma ga Alhaji Teku.

Haka kuma shima Dan Marka (Garzali Miko) wanda ya kasance dan uwa ga Alhaji Teku a koda yaushe samun sabani suke da Alhajin domin yakan je neman taimako wajen Alhajin amma sai ya hana sa, wanda sanadin hakan ke fusata Dan Marka saboda ganin Alhaji bai rasa abinda zai taimake sa dashi ba, yayin da kuma Hauwa (Hassana Muhammad) take jin haushin Dan Marka a duk lokacin da yaje neman taimako bai samu ba, da zarar ya soma fada sai ta dinga ganin rashin hakurin sa wanda a karshe ma tayi yaji ta koma gidan su kuma ta bukaci Dan Marka ya sake ta.

Lokacin da matar Dan Marka ta guje sa sai yaje wajen Alhaji Teku don yasa baki ga iyayen ta matar sa ta dawo gidan sa. Amma sai Alhaji yaki yin hakan karshe ma bayan Dan Marka ya saki matar tasa Hauwa sai Alhaji Teku ya zagaye ya aure ta. Haka bayan Dan Marka ya sake yin wani auren Alhaji Teku ya raba sa da matar tasa, fushin hakan ne yasa Dan Marka da wasu jama’ar wadanda basa goyon bayan Alhaji Teku suka je gidan sa da nufin yi masa duka, amma sai ya gudu wajen maigari. Sanadin hakan ne yasa aka soma neman Dan Marka za’a yi masa hukunci amma sai mahaifiyar sa Marka (Hajara Usman) ta bashi shawarar ya tafi birni neman sana’a.

Cikin sa’a kuwa Dan Marka ya dawo daga birni da dumbin arziki domin ya sayi mota me tsada kuma ya taho  da budurwar da zai aura. Yayin da a lokacin tuni arzikin Alhaji Teku ya soma ha baya. Ita kuma Hauwa tsohuwar matar Dan Marka tuni Alhaji Teku yayi mata saki uku yayin da ta saura yana nadama. Haka ma Ladidi matar sa ta biyu da ta guje sa (Amal Umar) nan itama ta soma nadamar gujewa Dan Marka kuma ta bukaci ya mayar da ita dakin ta saboda ganin yayi kudi amma sai ya nuna lokaci ya kure mata don shi tuni ya taho da matar da zai aura.

Abubuwan Birgewa:

1- Labarin ya nishadantar kuma ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa.

2- Sauti ya fita radau, haka ma hoto ba laifi.

3- Anyi kokari wajen nuna salon daukar hoto wanda hakan ya karasa fim din armashi.

4- Daraktan yayi kokari wajen ganin labarin ya tafi ta hanyar da ta dace, haka kuma yayi kokari wajen ganin jaruman sun taka rawar da ta dace, domin jaruman ma sun yi kokari.

5- An samar da wuraren da suka dace da labarin.

6- Wakokin fim din sun yi dadi gami da nishadantar da masu kallo.

Kurakurai:

1- Wakar farko ta cikin fim din wanda Dan Marka da Hauwa (Hassana Muhammad) suka yi an saka ta a muhallin da bai dace ba, saboda scene din da yazo kafin wakar an nuna Dan Marka sun samu sabani da matar shi Hauwa, amma a nuno wa ta gaba sai aka gan su suna rawa da waka cikin farin ciki. Bayan gama wakar kuma aka ga tayi yaji ta tafi gidan su.

2- Shin meye matsayin Jan Darma (Danjuma Salisu) wanda har Alhaji Teku (Sulaiman Bosho) ya kira shi ya ba shi izinin dukan iyalan shi? Hakan sam bai dace ba domin ya saba wa addini da shari’a saboda ko shi Alhaji Tekun shari’a bata bashi damar daukar madoki don dukan iyalan nasa ba, balantana kuma dan aiken sa.

3-Rawanin da Megari ya nada a kan sa yafi kama da kallabi ko mayafin mace ba ainahin rawani ba, saboda akwai ado na kyallin mayafi wanda hakan ya kara tabbatar da ba rawanin zahiri bane.

4- Lokacin da su Dan Marka suka biyo Alhaji Teku rike da makamai da nufin yi masa duka, wanda sanadin hakan yasa Alhaji Teku ya nufo wajen Megari, sai dai kuma bayan zuwan su wajen Megari yanayin yadda duk suka tsaya a gaban Megari suna mayar da martanin abinda ya faru, hakan bai yi kama da zahirin yadda ake sauraron korafi a gaban Maigari ba.

Karkarewa:

Labarin ya nishadantar sosai kuma ya rike me kallo, haka kuma an yi kokarin isar da wani darasi na illar cin amana da kwadayi ko gujewa masoyin gaskiya saboda bashi da abin duniya, wanda a karshe hakan ya jefa mutum cikin nadama da danasani. Wallahu a’alamu!

Exit mobile version