Daga: Musa Ishak Muhammad.
Suna: Doya Da Manja.
Tsara labari: Umar Mai Jalingo.
Kamfani: TJ MULTIPURPOSE CONCEPT. .
Bada Umarni: Umar Mai Jalingo.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Aminu Sharif, Sulaiman Bosho, Hafsat Idris, Hajara Usman, Aina’u Ade, Peter Andrew, Aminu Mirror, Abdussalam Aminu, Usaina Annuri, Maryam Indiana, Zainab Autar Ala da sauransu.
Fim din “Doya da Manja” fim ne da a ka Gina shi a kan labarin wani matashin Dan sanda mai suna Balarabe (Aminu Sharif), da kuma wata masoyiyarsa mai suna Fasilat( Hafsat Idris). Soyayyar tasu dai ta ginu ne sakamakon ceton Fasilat da ya yi a lokacin da wasu ‘yan ta’adda su ka sato ta, kuma su ka sako ta a akwati cikin dare. Sai dai sun yi rashin sa’a domin kuwa sun yi kacibus da ‘yan sanda a lokacin da su ka zo wucewa da ita. Inda a wannan lokacin ne Balarabe ya ke karbar ta daga hannu ‘yan ta’addan bayan sun gudu.
Daga haka ne soyayyar Balarabe da Fasilat ta fara. Sai dai bambancin kabila ya so ya zamar mu su babban kalubale. Shi dai Balarabe Bahaushe ne, yayin da ita kuma Fasilat Beyarabiya ce. A bangarrnsa shi an amince masa ya aure ta, sai dai ita Fasilat an ce ba za a bata auren sa ba, saboda wai Hausawa ba sa rike aure, su na da saurin saki. Wannan hukunci ya saka su Balarabe cikin mawiyacin hali domin tun tuni sun yi nisa a cikin soyayyar junansu. Kuma hakan ne ya sa Fasilat ta gudu ta bar gidansu tunda ba za a bar ta ta auri wanda ta ke so ba.
A karshe dai Fasilat ta je ta kai karar iyayenta gurun wani malami babba a kabilarsu,
wanda kuma ya zo ya yi mu su fada cewa ai auren Balarabe da Fasilat ba haramun bane tunda dukansu musulmai ne. Saboda haka bai kamata kabilanci ya shigo cikin maganar ba. A karshe dai an daidaita kuma an amince mu su sun auri juna.
- Fim din ya bayyana muhimmancin zaman tare a tsakanin kabilu mabanbanta, domin gashi har auratayya ta shiga tsakaninsu kamar yadda a ka nuna a fim din.
- An nuna tasirin Jami’an tsaro na gari kamar yadda Balarabe ya nuna.
- An samu sauti mai kyau a cikin fim din.
- Ba a samu matsalar daukar hoto ba, domin hotunan sun fita sosai.
- Jaruman ciki sun yi kokari sosai musamman Fasilat yadda ta ringa kokarin yin Yarbanci kamar yarenta.
Kurakurai
- A lokacin da Fasilat ta je gaida Mamansu Balarabe, da su ka fara gaisawa ta manta ta fara yin magana kamar Bahaushiya, Sai daga baya ta tuna kuma sai ta koma magana da salon na Yarbanci din.
- A lokacin da su Balarabe su ka kama yan daban da su ka zo sace Fasilat a karo na biyu, ya ya a ka yi su ka san su na kofar gidan har su ka zo su ka kama su.
Karkarewa
Fim din “Doya da Manja” fim ne da ya samu aiki mai kyau, kuma ya samu nasarori masu tarun yawa. Domin fim din ya tura wasu muhimman sako, musamman na muhimmancin zaman lafiya a tsakanin kabilu mabanbanta da su ka samu kansu a zama a muhalli daya.