Musa Ishak Muhammad" />

Sharhin Fim Din ‘Gidan Na Rage’

Suna: Gidan Na Rage.
Tsara labari: Auwal M. Sarki.
Kamfani: MIA Enterprises.
Daukar Nauyi: Ansar Abdulkais.
Shiryawa: Muhammad MIA.
Bada Umarni: Ali Gumzak.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Aminu Sharif Momo, Mustafa Naburaska, Alhassan Kwalli, Isiyaku Jalingo, Aina’u Ade, Hafsat Bauchi, Rahama MK, Fatima Shu’uma, da sauransu.
Fim din Gidan Na Rage, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani attajiri mai suna Na Rage(Aminu Sharif Momo), wanda ya ke da mata guda uku. Farkon fim din an nuna Na Rage ya shigo gida da shi da hadiminsa mai suna mulmuli (Mustafa Naburaska) da kayayyaki a hannunsu kuma cike da walwala da farin ciki a fuskokinsu. Bayan duka matan sun fito ne sai su ke shaida musu cewa ai aure zai kara, domin ya cike mata ta hudu.
Ranar da Na Rage ya ke tarewa da amaryarsa, ta zamar masa mafarin rikici da rashin sukuni agareshi da dukkanin ahalin wannan gida. Domin a wannan daren da ya ke tarewa ne ya nemi jakar kudinsa ya rasa, wadda ta ke dauke da kudi har naira miliyan daya da rabi. Batan wannan kudi ya tashi hankalin kowa a gidan, wanda hakan sai da ya tilasta mu su zuwa gurin ‘yan sanda domin a yi binciken wanda ya dauki wannan kudin. Sai dai hakan bai samar da mafita ba, domin kuwa dukkanninsu ba wanda ya amsa cewa shi ne ya dauka.
A haka dai a ka yi ta zaman zulumi domin kuwa Na Rage ya hana kowa sukuni a wannan gida. Si dai duk da wannan matsin da ya ke ta yi, abun ya ki chanjawa domin babu labarin wannan jakar kudin. Sai dai a karshe an ga wannan jaka a tsakiyar falo, amma an rasa wane ne ya kawo ta. Amma bayan an bincike jakar an riski babu dubu dari a ciki.wadda mulmuli ya dauke a lokacin da ya ga wannan jaka a falo. Sai ya yi sauri ya kai ta daki ya zari kudin sannan ya dawo da su inda ya dauka.
Abubuwan Yabawa
1. Takaice fim din a gida daya wato gidan Alhaji Na Rage, ya sa fim din ya dace da sunansa.
2. An samu sauti mai kyau a cikin fim din.
3. Hotuna ma sun dauku sosai.
4. An samu nishadantarwa a cikin fim din.
Kurakurai
1. Fim din zai wahalar da mai kallo wajen fahimtar ainihin sakon da fim din ya ke dauke da shi.
2. Ya kamata a nuna lokacin da Na Rage ya ajje jakar tashi, a kuma nuna lokacin da a ka dauke ta.
3. Ya kamata a ce bayan an gama dambarwar da a ka yi, a ce a karshe an nuna wanda ya dauki jakar.
4. Inda fim din ya kare bai yi dai-dai da irin gurun da ya kamata a ce fim ya kare ba.
5. Shin wane irin darasi a ke so a dauka a cikin fim din ne? Domin tun daga farkonsa har karshensa ba a nuna wata alkibla da a ka dora fim din a kai ba.
karkarewa
Fim din Gidan Na Rage fim ne da ya kebanta da jigo na nishadantarwa, sai dai zai ba da wahalar gane wane sako a ke so ya isar ga masu kallonsa. Fim din ya samu aiki mai kyau a zahiri, amma sai dai bai fuskanci wata mikakkiyar alkibla guda daya ba. Nishadantarwa wani yanki ne daga cikin jigon fim, ko da an samu nishadantarwa a fim to ya kamata a samu wani jigon kuma wanda ya ke dauke da wani sako na musamman zuwa ga masu kallo da saurare.

Exit mobile version