Musa Ishak Muhammad" />

Sharhin Fim Din (Hafeez)

Suna: Hafeez.

Tsara labari: Abubakar Bashir Mai Shadda.   

Kamfani: Mai Shadda Global.

Daukar Nauyi: Ali Nuhu.

Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda.

Bada Umarni: Ali Nuhu.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Ali Nuhu, Umar M Sharif, Yakubu Muhammad, Sani Garba SK, Salisu S. Fulani, Abba El-mustafa, Jamila Nagudu, Maryam Yahaya, Bilkisu Shema, Hassana Muhammad da sauransu.

Fim din Hafeez fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani matashi mai suna Hafeez (Umar M Sharif). Shi dai Hafeez yaro ne mai gata, domin kuwa mahaifinsa (Yakubu Muhammad) mutum ne mai arziki kuma ya na tsananin kaunar Hafeez. Wannan ce ta saka ya ke matukar girmama ra’ayinsa. Wannan kudi da mahaifin Hafeez ya ke da shi ne ya saka mata da yawa ke kawo tallar soyayyarsu zuwa gareshi. Amma sai dai sam shi ko kadan hankalinsa ba ya garesu.

Hafeez ya kasance yaro ne mai ji da kanshi ga gadara da kuma rashin ganin mutuncin mutane. Wannan dalili ne ya sa duk matan da su ke kawo tallar soyayyarsu gareshi ya ke wulakanta su ya ke cewa sam ba su dace da ajinsa ba. Akodayaushe bibiyarsa su ke amma shi kullum kara nisanta kansa ya ke da su.

Duk da cewa Hafeez ya na samun tallar soyayya daga ‘ya’yan manyan mutane, amma kwatsam sai watarana ya kamu da soyayyar wata yarinya mai suna Safna(Hassana Muhammad), wadda su ka hadu ta dalilin ruwa da ta taimaka masa ya zuba a motarsa. Ita dai Safna mahaifinta wato (Ali Nuhu) talaka ne sosai, amma talaucinsa bai sa ka shi zubar da kimarsa da mutuncinsa ba. Shi mutum ne mai akida da kuma kulawa da mutuncinsa da kuma na iyalinsa.

A kokarin mahaifin Hafeez na ganin ya samar masa da abinda ya ke so, ya taso da kansa domin ya nemarwa Hafeez auren Safna. A lokacin ne ya zo da kudi har Naira miliyan biyu a kan cewa ya na so a saka ranar Hafeez da Safna. Sai dai mahaifinta ya ce ba zai karbi ko kwandala a cikin kudin ba, domin shi ba zai siyar da ‘yarsa a kan kudi ba, Kuma bazai aurar da ita ga Wanda ba ta so ba. Sannan ya cewa Alhajin ya turo Hafeez ya nemi soyayyar Safna, idan ya samu nasarar samun soyayyarta to shikenan sai a zo a yi maganar aurensu.

A hankali Hafeez ya samu nasarar samun soyayyar Safna, sai dai kash komai ya chanja a ranar da mahaifin Safna ya fara haduwa da Hafeez ya zo gurun Safna. Matsalar da ya samu kuwa ita ce, a wasu lokuta a baya Hafeez ya taba buge mahaifin Safna da mota,kuma sannan ya bi shi da zagi da cin mutunci, wanda ya kai har da yunkurin marin mahaifin nata. Wannan dalilin ne ya sa shi kuma ya ce sam ba zai taba ba shi aurenta ba. Hafeez ya samu kansa cikn rudani a dalilin haka, wanda hakan ya sanya masa ciwo har ya kai shi ga kwantawa a asibiti.

A karshe dai Hafeez ya yanke shawarar yin nisa da iyayensa domin komawa kauyen da su Safna su ka koma bayan an kore su daga gidan da su ke. Haka ya ajje duk wani gata nashi ya koma rayuwa a kauye duk domin ya samu nasarar samun soyayyar Safna. Kuma a karshe ya samu nasara domin kuwa mahaifin Safna ya ji tausayin yanayin da ya ga Hafeez a ciki, wanda hakan ya sanya ya yafe masa abinda ya yi masa kuma ya amince ya ba shi auren Safna.

Abubuwan Yabawa

1. Sunan fim din ya dace da labarin fim din.

2. Labarin ya tsaru kuma ya samu nasarar rike mai kallo har zuwa karshe.

3. Sauti ya fita radau.

4. An nuna tasirin tabbata a kan ra’ayi domin kare mutunci, kamar yadda mahaifin Safna ya rike talaucinsa.

5. An nuna cewa ba komai bane mutum ya ke iya samu dan ya na da kudi.

Kurakurai

1. An samu kamewar hoto na kusan dakiku 40 a lokacin da mahaifin Hafeez su ke cin abinci da mahaifiyar Hafeez.

2. An samu sabawar sautin magana da kuma motsawar baki a wasu gurare a cikin fim din.

3. Hotuna sun dan yi duhu a wasu gurare marasa yawa a cikin fim din.

Karkarewa

Fim din Hafeez fim ne da ya yi kokari wajen bayyana alakar soyayya tsakanin dan masu kudi da kuma ‘yar talakawa. Fim din ya nuna tasirin soyayyar gaakiya da kuma tasirin kare mutuncin kai saboda gudun janyowa kai wulakanci da cin mutunci. An samu aiki mai kyau a fim din domin kuwa nasarorin da a ka samu sun Fi matsalolin da a ka samu yawa nesa ba kusa ba.

Exit mobile version