Hamza Gambo Umar">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Hajjaju’  

by Hamza Gambo Umar
April 28, 2020
in BIDIYO, SHARHI
11 min read
Sharhin Fim Din ‘Hajjaju’   
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Suna: Hajjaju

samndaads

Tsara labari: Abdullahi Amdaz

Kamfani: Kabugawa Production

Bada Umarni: Ali Gumzak

Jarumai: Hadiza Muhammad, Shamsu Dan Iya, Maryam Yahya, Nuhu Abdullahi, Shehu Hassan, Bashir Na Yaya, Asma’u Sani da sauransu.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Hajjaju (Hadiza Muhammad) a zaune cikin dakin ta tana kwalliya a fuskarta, yayin da ‘yar ta Amira (Maryam Yahya) ta shigo cikin dakin tana nuna takaicin abinda mahaifiyar ta take yi na yin kwalliya don zuwa wajen bazawarin ta. A wannan lokacin ne Samir (Shamsu dan iya) ya shigo cikin gidan sai yaci karo da bazawarin mahaifiyar sa a tsaye yana jiran ta (Shehu Hassan Kano) bayan sun gaisa ne Samir ya shiga cikin gida ya nunawa mahaifiyar sa rashin jin dadin sa akan auren da zata yi, anan ta nuna masa batayi tsufan da zata ha’kura da aure don mahaifin su ya rasu ba.

Jin hakan ne yasa Samir ya fito ya riski bazawarin mahaifiyar sa ya soma yi masa rashin kunya gami da ‘kokarin korar sa. A sannan ne Hajjaju ta fito daga cikin gida taga abinda ke faruwa, cikin fushi ta kori Samir sannan suka soma hira da bazawarin ta. A wannan lokacin ne Safwan ya shigo cikin gidan (Nuhu Abdullahi) bayan ya shiga falo ne Amira ta fito wajen sa tana gaya masa ba’ka’ken maganganu akan ya takurawa rayuwar ta alhalin ita bata son sa domin matsayin su daya da yayanta tunda shi abokin yayanta ne.

A wannan lokacin ne Amira ta tuna wani lokaci da suke zaune da ‘kawarta a wajen sha’katawa inda ‘kawarta ke bata shawara akan ta daina wulakanta Safwan akan ya nuna yana sonta, amma sai Amira ta nuna itama ai tana son sa lokacin bayyana masa hakan ne baiyi ba, suna cikin hirar ne yazo ya riske ta saboda alamu sun bayyana cewa yaji hirar da suke yi, amma anan Amira ta sake cin mutuncin sa ta nuna ya fita daga rayuwar ta.

Bayan Amira ta gama wannan tunani ne yayan ta Safwan ya fito daga daki ya kawo mata waya a sanda Hajjaju ke kiran wayar ta da nufin ta kawowa bazawarin ta ruwan sha, a sannan ne Samir da Amira suka hada mugunta, nan fa Amira taje ha hada ruwan zafi a kofi ta kai masa, a sanda ta fita bata gaishe shi ba ta dangwarar da kofin ruwan a gaban sa, hakan ne ya batawa Hajjaju rai ta soma nuna wa bazawarin nata halin ‘ya’yan nata sai hakuri, amma sai ya basar ya nuna hakan ba komai bane.

Ganin halin da ta shiga tana kuka sai hankalin ‘ya’yan ta ya tashi suka soma neman gafarar ta amma ba wai sun amince dai tayi auren ba.

A wannan lokacin ne Hajjaju ta soma tunanin neman wata mafitar, hakan ne yasa ta umarci ‘ya’yanta Amira da Safwan akan su fito da wadanda zasu aura don su tashi su bar gidan ko hakan zai sa ta samu damar yin aure. Jin hakan ne yasa Amira ta bawa Safwan damar fitowa don suyi aure kuma ta nuna masa dama can tana son sa. Safwan da abokin sa Samir sun ji dadin amincewar da Amira tayi, hakan ne kuma ya bawa Hajjaju damar sauya dabara watarana ta rutsa Safwan saurayin ‘yarta ta nuna masa tana so ya bata hadin kai suyi rayuwa mai dadi kuma tayi masa al’kawarin zata ba shi kudi da ababen more rayuwa gami da ba shi auren Amira, jin hakan yasa Safwan yayi mamaki kuma ya fice yabar gidan gami da dauke ‘kafarsa gaba daya ya daina zuwa.

Hakan ne yasa Amira da Samir suka soma mamakin abinda yasa ya daina zuwa gidan, Amira taje har gidan iyayen Safwan tana neman sa, amma sai ‘kanwar Safwan ta nuna mata baya nan, tayi ‘kokarin kira mata shi a waya amma bai daga wayar ba. A bangaren Hajjaju kuwa rashin ganin Safwan duk sai ya dameta ya zamana cewa ko ta kwanta bacci bata komai sai tunani, a sannan ne taje dakin Amira cikin dare ta dauki wayar Amira ta turawa Safwan sa’ko akan tana son ganin sa, washe gari Hajjaju ta aiki Samir da Amira a sanda Safwan yazo ta rufe ‘kofa har ta hilace shi ya amince da ita.

2- Jaruman sun yi ‘ko’kari wajen isar da sa’kon labarin.

3- Daraktan yayi ‘ko’kari wajen ganin an tafiyar da camera ta hanyar da ta dace.

4- Sauti ya fita radau, haka ma camera don an samar da hoto me kyau.

Kurakurai:

Karkarewa:

Fim din ya fadakar, kuma zaren labarin har ya dire bai karye ba. Sai dai kuma ya kamata ace karshen fim din yafi haka inganci. Wallahu a’alamu.

SendShareTweetShare
Previous Post

Mako Mai Zuwa Za A Sassauta Dokar Zirga-zirga A Abuja –Buhari

Next Post

Korona: Za A Yi Wa ‘Yan Wasan Firimiyar Nijeriya Da Shugabanninsu Gwaji

RelatedPosts

NIS

Kwazon NIS Bisa Aiki Da Kundin Kula Da Iyakokin Kasa Na 2019-2023

by Hamza Gambo Umar
1 week ago
0

Daga Abdulrazak Yahuza Jere, Hukumar Kula da Shige da Fice...

Marigayi Sam

Al’ummomi Na Ci Gaba Da Bayyana Kyawawan Halayen Marigayi Sam Nda-Isaiah  

by Hamza Gambo Umar
3 weeks ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa,   Al’ummomi daban-daban na ci gaba...

Shin Wane Irin Tallafi Shirin ‘Future Assured’ Ya Yi A Kano?

Shin Wane Irin Tallafi Shirin ‘Future Assured’ Ya Yi A Kano?

by Hamza Gambo Umar
1 month ago
0

A watan Mayu na wannan shekarar na rubuta Makala akan...

Next Post

Korona: Za A Yi Wa ‘Yan Wasan Firimiyar Nijeriya Da Shugabanninsu Gwaji

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version