Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din Ke Duniya

Published

on

Suna: Ke Duniya.
Kamfani: T.J Multipurpose Concepts.
Labari: Salisu Mu’azu Rijiyar Zaki.
Tsara Labari: Salisu Mu’azu Rijiyar Zaki.
Daukar Nauyi: Hafsa Salisu Mu’azu.
Shiryawa: Baba Isma’il Mazaje.
Umarni: Salisu Mu’azu Rijiyar Zaki.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Sulaiman Bosho, Salisu Mu’azu Rijiyar Zaki, Lawan Taura, Umar Faruk, Musa Dameji,Lubabatu Madaki, Hajiya Zulaihat, Rukayya Muhammad, Zaituna Cameroon da sauransu.
Fim din Ke Duniya fim ne da a ka gina shi a kan labarin wata mata wato Hajiya (Lubabatu Madaki) wadda ta kamu da soyayyar saurayin ‘yarta wato (Umar Faruk). Shi dai asalalinsa saurayin ‘yarta ne mai suna Ummi. Watarana dai Hajiya ta kasa boye abunda ya dade ya na damunta a cikin zuciyarta game da soyayyar saurayin’yar nan tata, domin kuwa ta fito fili ta sanar da shi abunda ya ke cikin ranta. Sannan ta ba shi dama a kan ya je ya yi shawara, sannan ta nemi ya bata lambarsa ta banki domin ta turasa masa kudi har miliyan goma domin ya yi amfani da su.
Da farko da Umar bai amince da bukatar Hajiya ba, amma daga baya sai ya yanke shawarar karbar soyayyarta tunda hakan bai sabawa addininsa ba. Domin kafun ya yanke hukunci sai da ya je ya tambayi malami a ka ba shi fatawa a kan hakan. Da farko babban yayansa ya so ya hana wannan auren, amma dai karshe shi ma dole ya hakura ya amince, saboda ganin yadda kanin nasa ya makance a kan soyayyar Hajiya da kuma ganin cewa auren nasu bai haramta ba ko a addinance.
A daya bangaren kuma, wani bawan Allah ne mai suna Tijjani (Salisu Mu’azu Rijiyar Zaki) shi ma ya hadu da makamancin irin wannan matsalar, domin kuwa ya samu kansa a cikin damuwa domin kuwa mahaifinsa ne ya kamu da son yarinyar da ya je ya nuna masa a matsayin wadda zai aura. Tunda ya tsallara ido ya ganta shikenan fa ya ce lallai shi sai ya aure ta. Haka nan a ka yi ta rigima a tsakanin uban da dan. Rigimar tasu ta zama kamar wasa ta zaga ko’ina a cikin gari. A haka dai a ka yi ta fama sai dai a karshe da uban da dan ba wanda ya samu nasarar auren ta.
Abubuwan Yabawa
1. Fim din ya samu aiki mai kyau, kuma jaruman sun yi kokarin ba da abinda a ka tsara a labarin.
2. Sunan fim din ya dace da labarin fim din.
3. Fim din ya nuna muhimmancin dattako.
Kurakurai
1. An samu kwan-gaba-kwan-baya a wajen tsara labarin fim din.
2. An samu maimaituwar wasu dauka a gurare daban-daban.
3. Fim din ya kare ba tare da ya nuna yin auren kowanne daga cikinsu ba.
4. Abubuwan da Tijjani ya ringa yi wa mahaifinsa, ya yi yawa.
4. Labarin fim din ya na da wuyar kasancewa musamman abunda a ka nuna a bangaren Tijjani.
5. Ya kamata a nuna wani ya auri Baby, amma har fim din ya kare ba a nuna wani ya aure ta ba.
karkarewa
Fim din ya samu aiki mai kyau, amma dai ya samu matsalar tantancewa. Domin an samu maimaituwar gurare daban-daban, wanda hakan matsalar tantancewa ce, Edita din bai yi aiki mai kyau ba, ko kuma mai ba da umarni bai tsaya ya yi aikinsa ba yadda ya kamata.

Advertisement

labarai