Hamza Gambo Umar" />

Sharhin Fim Din ‘Matar Uba’

Suna: Matar Uba
Tsara Labari: Shafi’u Dauda
Kamfani: Halifa Abubakar Inbestment Limited
Shiryawa: Halifa Abubakar
Umarni: Husaini Ali Muhammad
Jarumai: Ali Nuhu, Aina’u Ade, Sani Garba S.K, Shamsu Dan Iya, Ali Dawayya, Nana Muhammad, Basma Baba Hasin, Musbahu A.K.A Anfara da sauransu.
Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Basma (Azeema) tare da yayan ta Mustafa sun dawo daga makaranta amma bayan shigar su gida lokacin da mahaifiyar Azeema ta jawo su jikin ta tana dubasu, a sannan ne Asabe (Aina’u Ade) ta fito taja dan ta gami da nuna bata yarda ya cigaba da ala’ka da ‘kanwarsa Azeema ‘yar kishiyar ta ba. ‘Kiyayyar da take nunawa kishiyar ta Maryam ne ya sa wata rana bayan ta dawo daga unguwa ta tarar da dan ta Mustafa yana cin abinci tare da Azeema ta dauke shi gami da nunawa mijinta Malam (Ali Nuhu) bata yarda dan ta ya dinga cin abincin kishiyar ta ba don tana gudun kada a saka masa guba a ciki ya ci ya mutu, ganin Malam bai goyi bayan ta ba sai ta shirya taje wajen malami aka bata maganin da ta yi amfani da shi wajen korar kishiyar ta daga gidan, haka Maryam ta fita a haukace ta bar gida bayan wani dan lokaci akazo aka sanar da Malam labarin mutuwar matar sa Maryam, wadda bayan barin ta gidan sai Malam ya shiga damuwa aka soma cigiyar ta a yayin da Asabe ta tabbatar masa da cewar Maryam ta tafi kenan.
Bayan mutuwar Maryam da tsahon shekaru a sanda ‘yar ta Azeema ta zama budurwa, sai ya zamana cewa Asabe ta cigaba da gallaza mata domin takan dora mata talla kuma idan ta dawo kudi bai cika ba Asabe ta kan yi mata mugun duka, duk da Malam yana tsawatar wa Asabe ta hanyar yi mata nasiha akan rikon maraya amma hakan bai sa ta ragawa Azeema ba, har zuwa lokacin da Azeema ta hadu da wani saurayi (Ali Dawayya) wanda ya hure mata kunne ya bu’kaci ta gudu daga gida don samarwa da kanta ‘yanci.
Bayan Azeeza tabi zugar saurayin ta sun gudu, sai ya kaita hotel wanda kusan wajen da ya ajiye ta matattara ce ta karuwai da sauran ‘yan duniya, a can ya ajiye ta kuma ya kama mata daki ya ajiye ta a ciki.
Tun daga sannan sai Azeema ta zama karuwa wadda maza ke daukar ta, domin a sannan ne ta fara mu’amula da Dan Kulle (Musbahu A.K.A Anfara) wanda bai yarda Azeema tayi tarayya da wani da namiji ba sai shi, hakan ya sa lokacin da tayi wani ba’ko (Shamsu Dan Iya) ganin sa ne yasa Dan Kulle ya soma fushi kuma yaje wajen shugaban ‘yan barikin (Sani Garba S.K) ya nuna zai rabu da Azeema, amma sai shugaban ya nuna zai ja mata kunne, bayan shugaban yaje wajen ta ne da ‘korafi sai ta karbi kudi masu yawa a wajen saurayin da yazo wajen ta sannan ta ba da kudin aka kaiwa Dan Kulle don ya ajiye mata a matsayin toshiyar baki a bisa laifin da tayi masa, bayan saurayin ya bata kudi sai ya bu’kaci sanin labarin rayuwar ta, amma sai ta dinga yi masa yawo da hankali gami da ‘karairayi. Tun daga sannan Azeema ta cigaba da kawo samari dakin ta amma tana tsoran Dan Kulle ya sani, domin akwai sanda ta kawo wani abokin shedancin ta sai Dan Kulle yazo yana buga mata kofar daki zai shigo, jin zuwan sa ne ya sa ta boye saurayin da ta kawo a cikin kwaba sannan ta budewa Dan Kulle dakin ya shigo, kuma bayan ya shigo sai tayi dabarar da ta sallami saurayin ba tare da Dan Kulle yasan abinda ke faruwa ba. A bangaren mahaifin Azeema kuma ya shiga damuwa sosai saboda shigar ta bariki, domin akwai sanda kafin Azeema ta bar gida ta bu’kaci ya dauke ta daga cikin gidan ya kai ta wani wajen saboda ta gaji da azabar da kishiyar mahaifiyar ta Asabe ke gana mata, amma sai ya rarrashe ta ya bata hakuri.
Yana zaune cikin damuwar rashin sanin halin da Azeema ke ciki sai wata rana kwatsam Azeema ta dawo gida daga wajen yawon bariki. Hakan ne ya jefa mahaifinta cikin farin ciki yayin da ita kuma Asabe ta soma zagin Azeema tana yi mata gori na irin wula’kantacciyar rayuwar da ta jefa kanta. Bayan Azeema ta dawo gidan su da zama sai Asabe ta cigaba da gallaza mata ya zamana cewa wanki da duk sauran wasu ayyukan gida itace take yin sa, har zuwa lokacin da wata ‘kawar Azeema tazo gidan don su gaisa da Azeema amma sai Asabe ta soma zagin ta da miyagun maganganu, hakan ne ya sa ‘kawar Azeema ta yiwa Asabe rashin kunya kafin daga bisani da Malam ya shigo cikin gidan ya kori ‘kawar Azeemar yayin da Asabe ta cigaba da masifa gami da mamakin abinda ‘kawar Azeema tayi mata.
Ba’a dau tsahon lokaci da dawowar Azeema gida ba ta sake sulalewa ta gudu ta koma yawon bariki Wanda a sannan ne Mustafa dan da Asabe ta haifa shi kuma tuni ya lalace ta zama dan shaye-shaye domin akwai lokacin da Asabe take yiwa Malam rashin mutunci sai Mustafa ya shigo cikin gidan yayi yunkurin kai mata naushi amma sai ‘karfin shaye-shayen da yayi ya rinjaye sa ya fadi ‘kasa. Azeema kuwa bayan ta sake komawa yawon bariki sai suka soma samun sabani da saurayin ta Dan Kulle wanda har yayi mata duka kuma yaji mata rauni.
Duk da kawayen ta sun zo sun kwace ta a hannun sa amma sai wani saurayin ta yazo gidan ya bu’kaci ta hada kayan ta subar gidan, amma sai ‘kawayen ta da shugaban gidan barikin suka sasanta abin. A wannan lokacin ne kuma Mustafa ya shiga cikin falon Asabe ya sace kudin da ta ajiye, amma da ta shigo tayi masa magana sai ya kai mata naushi ta fadi a wajen ta mutu. Bayan mutuwar ta ne Azeema ta dawo gida da mijin da zata aura kuma ta tuba ta dai na yawon bariki.

Abubuwan Birgewa:
1- Labarin ya fadakar domin yayi nuni da illar mugun rikon da wasu iyayen suke yiwa ‘ya’yan da ba nasu ba.
2- An nuna illar zaluntar dan wani domin hakan zai iya jefa naka dan cikin halaka wadda kaima zata shafeka.
3- Sauti ya fita radau, camera ma ba laifi.

Kurakurai:
1- A farkon fim din me kallo yaga Malam (Ali Nuhu) tare da iyalin sa a cikin wani gida na daban, amma bayan matar sa Maryam ta rasu ba da jimawa ba sai aka gansu a cikin wani gidan na daban, a ‘karshen fim din kuma aka sake ganin su a gidan su na farko. Shin wani gidan mahaifin Azeema ya siya? Idan kuma sun tashi daga wancan ne sun kama hayar wani to ya dace a yiwa me kallo bayani, amma kuma idan hayar wani gidan suka kama shin me ya sa a ‘karshen fim din aka sake ganin su a ainahin gidan su na farko?
2- Tun a farkon fim din lokacin da aka nuna Mustafa dan da Asabe ta haifa me kallo bai sake ganin sa ba sai a ‘karshe ‘karshen fim din lokacin da aka nuna ya zama dan shaye-shaye, ya dace a cigaba da nuno shi tun kafin akai gabar da ya lalace kuma a nuna silar lalacewar sa, domin tunda an nuna mahaifin su kamilin mutum ne, to rashin tarbiyyar mahaifiyar yaron ba zatasa shima ya zama mara tarbiyyar ba har sai an nuna silar da ya zamo dan shaye-shaye kuma mara tarbiyya.
3- Me kallo yaga Azeema ta daina yawon bariki ta dawo gida ta cigaba da zama cikin u’kuba kafin daga bisani da ta sake guduwa, shin me yaja hankalin Azeema wanda har ya zamo darasi a gareta da har ta dawo cikin u’kubar da ta bari? Ya dace a nuna dalilin dawowar ta gida a karon farko ko da ta hanyar nuna mahaifin ta yana addu’ar ganin ta dawo wanda ‘karfin addu’ar ne ya dawo da ita, amma ba wai aga haka kurum ta dawo ba, hakan ba abu ne da zai faru cikin sauki ba ga masu aikata irin rayuwar Azeema ba.
4- Lokacin da Azeema zata sake guduwa daga gidan su me kallo yaga Azeema ta rubuta wasika ta ajiye wa mahaifinta, shin me wannan wasikar ta ‘kunsa? Tunda ba’a nunawa me kallo abinda ke rubuce a wasi’kar ba, to ya dace aji ko shi mahaifin nata ne yayi bayanin abinda ke cikin wasi’kar don gudun kada a bar me kallo cikin tunani da wasu-wasi.
5- Lokacin da Azeema ta dawo daga yawon bariki, bai kamata me kallo yaga ta cigaba da bautawa kishiyar mahaifiyar ta cikin tsoro ba, ya dace a nuna irin futsarar da ta koyo wanda hakan ya kangarar da ita har ta dai na jin tsoron Asabe.

Karkarewa:
Labarin ya fadakar, amma zaren labarin ya dunkule a waje daya, wanda hakan yasa aka yi ta maimaita wasu abubuwan da bai kamata a sake nunawa me kallo ba. Wallahu a’alamu!

Exit mobile version