Hamza Gambo Umar" />

Sharhin Fim Din ‘Mijin Badariyya’

Suna: Mijin Badariyya

Tsara Labari: Munzali M. Bichi da Aminu U/Ginu

Kamfani: Jidawa International

Shiryawa: Ibrahim S. Jidawa

Umarni: Ali Gumzak

Jarumai: Ali Nuhu, Tijjani Faraga, Ladi Muhammad, Umma Shehu, Teema Makamashi, Adamu Hassan Nagudu, Malam Inuwa, Hajiya Zulai. Da sauran su.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Binta (Teema Makamashi) a zaune a gefen titi tana bara cikin suffar marasa hankali, a wannan lokacin ne kuma Badariyya (Umma Shehu) ta bata sadakar kudi, sai dai kuma bayan ta sansana kudin sai ta sanar da Badariyya cewar ta kusa mutuwa, suna cikin haka kuwa sai mota ta buge Badariyya sa’in da tazo tsallaka titi. A daidai sannan ne Badariyya ta farka daga mummunan mafarkin da tayi na wannan mace mara hankali.

A lokuta da dama an nuna cewar Badariyya tana miyagun mafarkai inda take ganin Binta mahaukaciya a cikin mummunar siffa tana firgita ta, wanda hakan yasa Fahad (Ali Nuhu) saurayin da Badariyya zata aura ya dauke ta ya kaita wajen mahaifin shi suka sanar mishi da halin da Badariyya take ciki, a lokacin ne mahaifin Fahad wato Malam (Malam Inuwa) ya sake yiwa Badariyya tuni akan dagewa wajen yin addu’a. Sai dai kuma tun kafin Badariyya da Fahad su fito daga cikin gidan sai ciwon kai mai tsanani ya rufe ta wanda ya zamo silar da suka garzaya asibiti don ganin likita.

A asibiti ne kuma likita (Adamu Hassan Nagudu) yaga Badariyya kuma yaji ya kamu da son ta a cikin ran shi, hakan yasa da ya fuskanci suna gab da yin aure ita da Fahad sai yayi mata karyar cewa Fahad yana dauke da cutar kanjamau don haka kada tayi kuskuren yin tarayya dashi bayan aure har sai an gama binciken lafiyar Fahad din. Jin haka ne yasa bayan auren Fahad da Badariyya ta tashi hankalin ta akan lallai sai ya saketa ba zata iya cigaba da zama dashi ba, dalilin hakan yasa Badariyya ta koma gidan iyayen ta amma sai mahaifin ta (Tijjani Faraga) ya dauki makami ya korata akan lallai sai ta zauna da mijinta.

Ganin da Badariyya tayi na cewar bata samu goyon bayan iyayen ta akan  rabuwar auren ta da Fahad ba, hakan yasa ta koma gida tayi mishi rauni da makami sannan ta sake fitowa don zuwa wajen likitan da ya sanar mata cewar mijin ta yana dauke da cutar kanjamau, amma bayan zuwan ta sai ta tsinkayi hirar da likitan suke yi da abokin shi inda ya tabbatar wa da abokin cewar soyayyar da yake yiwa Badariyya ce tasa yayiwa mijinta kazafi don yayi nasarar raba auren su sannan shi kuma ya aure ta. Jin hakan ne ya tashi hankalin Badariyya ta shiga cikin ofis din ta fadawa likitan miyagun maganganu sannan ta koma gidan mijinta, yayin da shima likitan yayi nadamar makircin da ya kulla mata wanda hakan yasa yabi bayan ta don neman gafarar su ita da mijinta.

Sai dai kuma bayan Badariyya ta koma gida ne ta tarar da Binta mahaukaciya a gidan su, anan ne kuma aka tabbatar mata da cewar Binta ce mahaifiyar ta wadda bayan rasuwar mijin ta sai Malam mahaifin Fahad yayiwa Binta din ciki,  ganin ta samu juna biyu da Malam kuma bata hanyar aure ba sai Malam din ya bukaci ta zubar da juna biyun amma Binta (Teema Makamashi) taki amincewa, hakan yasa Malam ya turo da likita da nufin ayi mata allurar da za’a kashe ta sannan a batar da gawar ta, amma sai likitan bai aikata hakan ba yayin da Binta ta gudu ta batar da ainahin kamannin ta ta zama kamar mahaukaciya,  kuma bayan ta haihu sai ta yadda jaririyar a kofar gidan wani Alhaji. (Tijjani Faraga) silar hakan ne yasa bayan dawowar alhajin daga masallaci da ya tsimci jaririyar sai ya kaiwa matarshi suka cigaba da renonta kuma suka sanya mata suna Badariyya.

A lokacin da Fahad ya samu labarin cewa Badariyya ‘yar mahaifin shi ce sai ya saketa wanda hakan ne kuma ya bawa likitan da yayi musu kazafi damar zuwa neman yafiyar Fahad sannan kuma aka bashi auren Badariyya a yayin da shi kuma Malam ya nemi gafarar Binta da ta matarshi akan laifin zina da ya aikata da Binta din kanwar matarshi.

Abubuwan Birgewa:

1- Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa sannan kuma an yi kokarin rike me kallo har zuwa inda ake son a kai shi.

2- Daraktan yayi kokari wajen ganin labarin ya tafi yadda ya dace, sannan kuma yayi kokarin ganin jaruman sun isar da sakon da ake bukata, domin jaruman sun taka rawar da ta dace.

3- An samar da wuraren, da suka dace da labarin, wato ‘locations.’

4- Sauti ya fita radau.

Kurakurai:

1- Lokacin da Badariyya tare da Fahad suka je gidan mahaifin Fahad din (Malam Inuwa) da nufin yi mishi korafi akan miyagun mafarkan da take yi, an samu disashewar hoto a ‘wide shot’

2- Lokacin da Fahad ya dawo ofishin likita bayan ya siyo maganin da likita (Adamu Hasan Nagudu) ya tura shi siyowa, bayan ya dawo ofis din ne likita ya sanar mishi da cewar Badariyya wadda suka zo tare ta tafi gida, sai gashi kuma a nunowa ta gaba ‘nedt scene’ me kallo ya sake jin maimacin maganganu da likita suka yi da Fahad duk da kasancewar wani wajen na daban aka bayyana.

3- An nuna Binta tana tafe a gefen titi cikin duhu, sai dai kuma nunawar tayi tsawo gami da jan lokaci har kusan mintuna biyu da sakwan talatin ba tare kuma da an nuna wani muhimmin sako a wajen ba wanda ya haifar da jan lokacin, ya dace a takaice scene din don gudun gajiyar da me kallo akan nuna mishi abinda bazai rike shi ba.

4- Lokacin da Mai babur din adaidaita sahu (Ali Dawayya) ya dauko Badariyya a cikin babur din shi da nufin zai kai ta zoo road, sa’in da suka tafiya yana bata labari, me kallo yaga fuskar wani mutum wanda yake dariya a cikin madubin hannun hagun me babur din, wanda kuma alamu sun nuna a makale yake a jikin babur din suna tafiya dashi. Ya dace ayi kokarin dusashe fuskar mutumin tunda bashi da alaka da labarin.

Karkarewa:

Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa, kuma fim din yayi nasarar yin nuni da wasu muhimman darussa akan mutanen da suke ganin kaddarar aikata zina bazata iya hawa kan su ba, haka kuma an nuna illa ga matayen da suke kadaice kan su bayan mutuwar mazajen su ba tare da sun yi wani auren ba ko kuma sun zauna a hannun ‘yan uwan su. Tabbas an nuna darussa masu karfi a fim din wadanda al’umma zasu amfana. Wallahu a’alamu!

Exit mobile version