Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Mufida’

Published

on

Suna: Mufida.
Labari: Sulaiman Bello Eazy.
Tsara Labari: Ahmad A. Kabugawa.
Daukar Nauyi: UK Entertainment.
Shiryawa: Kabiru A. Yako.
Umarni: Sulaiman Bello Eazy.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Sadik Sani Sadik, Teema Yola, Rukayya K.D, T. Money da sauransu.
Fim din Mufida fim ne da a ka gina shi a kan labarin wasu ma’aurata biyu wato Kabir (Sadik Sani Sadik) da Mufida (Teema Yola). A farkon fim din dai an nuno abokin Kabir ya na tambayar shi labarin wata budurwarsa, yayin da Kabir ya ke ba shi amsar cewa ai yarinyar nan ba ta da kirki, shi ya fita harkarta.
Ita dai Mufida mace ce mai tsananin kishin mijinta, ko kadan ba ta kaunar ya kusanci wata mace ko wata mace ta kusance shi. Shi kuma Kabir a nashi bangaren, namiji ne mai kalle-kalle, sai dai duk abinda ya ke ya na yin kaffa-kaffa saboda kar Mufida ta gano shi, saboda ya san ta na da tsananin kishinsa. Hakan ya sa ko waya zai yi da wata, sai ya ringa boyewa saboda kar ta ji shi ko ta gan shi. Ta taba kama shi sau daya ya na waya, amma sai ya ce mata mahaifiyarshi ce ta ke kiran sa a kan wata matsalar gidansu da ta taso.
A na nan ne watarana kawar Mufida mai suna A’isha ta yi mata waya a kan cewa ta na so ta zo Kano za ta yi jarrabawa kuma idan ta zo ta na so ta sauka a gidan Mufida. Nan take Mufida ta ce mata babu matsala ta na nan ta na zaman jiran ta. Bayan Kabir ya dawo daga aiki ta ke sanar da shi cewa za ta yi bakuwa wato A’isha za to ta dan zauna mu su na kwana biyu. Shi ma sai ya ce ai babu matsala.
Zuwan A’isha gidansu Mufida sai ya chanja yanayin zaman gidansu. Domin kuwa Kabir ya kyalla ido ya ga A’isha ranar da ta zo sai ya fara jin wani abu cikin zuciyarsa wani abu a kanta. Tun daga wannan rana Kabir ya fara bibiyar A’isha. Sai ya bari Mufida ta fita makaranta sai ya dawo gida ya nufi dakin A’isha. Sai dai tunda ya ke zuwa dakinta ba ta taba barin shi ya yi mata wani abu, saboda ta rike amanar kawarta Mufida. Kuma ta na masa kashaidin cewa idan bai daina shigowa dakinta ba za ta fadawa Mufida halin da a ke ciki.
Watarana motar Mufida ta samu matsala sai ta tsaya Kabir ya sauke ta da motarsa. Bayan sun fita ya sauke ta, sai ya kara dawowa gida domin ya je dakin A’isha kamar yadda yadda yadda saba. Sai dai ya na cikin dakin A’isha ya na ta kokarin ganin ya gamsar da ita domin biyan bukatarsa, kawai sai Mufida ta dawo gida, kuma kai tsaye sai ta zarce dakin A’isha. Shigar ta ke da wuya kawai sai ta riski Kabir a cikin dakin ya na tsaye a gaban A’isha, nan kuwa ta fito daga dakin da gudu ta na kuka ta fito falo. Nan ta ce ba za ta kara zama da Kabir ba tunda ya ci amanarta. Sannan ta yi wa A’isha Allah ya isa ta fice ta bar mu su gidan ta na kuka.
Abubuwan Yabawa
1. Fim din ya dace da sunansa.
2. An samu sauti mai kyau.
3. Hotuna ma sun dauku sosai a cikin fim din.
4. An nuna illar biyewa son zuciya, domin da Kabir bai nuna son zuciyarsa a kan A’isha ba, da bai rasa matarsa mai tsananin kaunar say da kishin say ba.
Kurakurai
1. Labarin fim din bai tsaru ba sosai, domin farkonsa da tsakiyarsa da karshensa ba su jeru yadda za su yi saukin fahimta ba.
2. Fim din ya kare a inda bai kamata ya kare ba.
3. Fitowar farko inda abokin Kabir ya ke tambayar shi a kan labarin budurwarsa, ba a ji amsar da ya ba shi ba, kawai sai ji a ka yi ya na amma yarinyar nan ba ta kyauta ba indai haka ne.
4. Daki daya a ka ringa amfani da shi a matsayin dakin Mufida da kuma wanda a ka sauki A’isha.
5. Mufida makaranta ta ke zuwa ba aiki ba, amma kuma da su na hira da A’isha sai a ka jiyo Tata na fadawa A’isha cewa tunda ta fara zuwa aikin nan………
karkarewa
Fim din Mufida ya samu aiki mai kyau, sai dai an dan samu matsaloli wajen tsara labarin fim din. Labarin fim din zai ba wa mai kallo wahala wajen gane hakikanin sakon da a ke so a isar a cikinsa. Amma aikin fim din ya yi kyau sosai. A kodayaushe mu na fadar cewa ba raina kokarin kowa mu ke ba, mu na nuni ne domin a kara inganta wannan sana’a.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: