Musa Ishak Muhammad" />

Sharhin Fim Din ‘Nisan Kwana’

Suna: Nisan Kwana.
Kamfani: UK Entertainment.
Labari: Yaseen Auwal.
Tsara Labari: Yakubu M Kumo.
Daukar Nauyi: Entertainment And Motion Pictures Production.
Shiryawa: Umar Sani Lawan.
Umarni: Yaseen Auwal.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Sadik Sani Sadik, Umar Gombe, Abba El-mustafa, Musa Mai Sana’a, Umar Tage, Isiyaku Abubakar, Yusuf Sasen, Rahama Sadau, Fati Abubakar, Yaseera Yola, Hafsat ‘Yar Gatan Baba, Amina Amal da sauransu.
Fim din Nisan Kwana fim ne da a ka gina shi a kan labarin wasu ma’aurata biyu wato (Rahama Sadau) da kuma mijinta (Sadik Sani Sadik), wanda bikin nasu ya zo ya zo da tangarda sakamakon batan wasu mata guda uku a lokacin da a ke shirin tafiya wajen taron (dinner). Su dai wadannan matan su uku an saka su ne a cikin wata mota da ta zo wajen a lokacin da a ke tafiya wajen wannan taro. Daya daga cikin abokan ango mai suna Ahmad (Umar Gombe) shi ne ya dora wannan mata a cikin wannan motar ba tare da ya tsaya duba ma wane ne direban ba. Sai da Kowa ya isa wajen taro amma ba a ga wadannan matan ba.
Cikin wadannan matan dai da su ka bata akwai kanwar Amarya mai suna Lubuna(Amina Amal) da kuma wata Jamila wadda ita wannan matar mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ce. Rashin ganin Jamila shi ne ya dagula komai, domin kuwa mijin nata ya kirawo ta a waya ta ce masa ta na gida, alhalin kuma ba ta gidan ta kama hanyar tafiya wajen wannan taron bikin nan. Lokacin da ya dawo gida ya tarar ba ta nan ne fa ya rikice domin ya kirawo wayarta ya ji a kashe kuma ya zo gidansa ya tarar ba ta nan. Daga nan ne sai ya kirawo kawarta, shi ne ta ke fada masa ai wajen taron biki ta tafi, nan ta ke ya juya mota ya nufi wajen taron.
Isowarsa ke da wuya ya zo ya iske kowa ya yi jungum-jungum a na ta maida maganar batan nasu. Ya zo ya ce ina matarsa a ka ce masa ai ga halin da a ke ciki, kuma matarsa ta na cikin wadanda su ka bata. Ai kuwa sai ya ce babu wanda zai fita daga wajen taron nan har sai an ga matarsa. A nan fa ya kirawo ‘Yansanda ya ce su zo su tsare masa wajen taron nan ta yarda babu wani ko wata dai zai fita daga wajen. A karshe dai an yi nasarar ganin su, bayan motar wadanda su ka sace su ta lalace mu su a hanya. A nan bakaniken da zai musu gyaran wajen karfe biyu na dare ya ke ganin matan a cikin motar, daga nan ne kuma asirin ya ke tonuwa, a ke kama su. A karshe sai ‘yan sanda su zo su tafi da su. Daga nan ne kuma a ke barin kowa ya tafi daga wajen taron tunda Yallabai ya samu labarin matarsa.
ABUBUWAN YABAWA
1. Fim din ya samu aiki mai kyau kwarai da gaske.
2. Sunan fim dia dace da labarin fim din.
3. Labarin fim din bai yanke ba tun daga farko har karshe.
4. Babu matsalar sauti ko kadan a cikin fim din, ko’ina sauti ya fito rangadadau.
5. Hotuna sun fito tar, babu inda a ka samu matsala, ko kadawar na’ura.
6. Fim din ya fadakantar kuma ya nishadantar a lokaci guda.
7. Fim din ya yi nasarar isar da sakonni da yawa a cikinsa.
8. An nuna muhimmanci tantance masu zuwa wajen taro da motoci, domin kuwa da a ce an tantance da ba a dorawa masu motar nan matan ba.
kARKAREWA
Fim din Nisan Kwana fim ne da ya tsaro, kuma ya samu aiki mai kyau, daga bangaren jagororin fim din har zuwa kan jaruaman cikinsa. Fim din ya fadakar kuma ya nishadantar. Cikin nishadi a ka isar da muhimmin sako zuwa ga masu kallo. Fim din Nisan Kwana ya na daga cikin fitattun fina-finan da su ka shahara a cikin wannan shekarar ta 2020. Fim din ya yi la’akari da abubuwan da zamani ya ke tafiya a kai, musamman a kan abinda ya shafi sabgogin biki da Kuma tarukan biki.

Exit mobile version