Connect with us

SHARHI

Sharhin Fim Din ‘Sabon Dan Tijara’

Published

on

Suna: Sabon Dan Tijara

Tsara Labari: Musa Mai Sana’a

Kamfani: Mai Sana’a Entertainment

Shiryawa: Abubakar Bashir Me Shadda

Umarni: Nasiru Ali ‘Koki

Jarumai: Ali Nuhu, Hajara Usman, Musa Mai Sana’a, Bashir Bala Chiroki, Babba Hikima, Baballe Hayatu, Alasan Kwalle, Halima Atete, Baba Labaran. Da sauransu.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

 

A farkon fim din an nuna Dan Tijara (Musa Mai Sana’a) yana tafe cikin unguwa akan mashin din sa yana zagin makwabtan sa akan rashin taimakon talakawa, a wannan lokacin ne wani makwabcin sa ya fito yake masa nasiha akan rashin dacewar abinda yake aikatawa, nan fa Dan Tijara yayi masa sabon rashin mutuncin sannan ya tafi. Daga nan kuma sai Dan Tijara ya kwasowa me wankin takalmi wasu manyan takalman sa akan ya wanke masa, amma ganin girmansu ya shallake tunani sai mai wankin takalman yace bazai yi ba, nan dai shima suka watse baram-baram. Haka a cikin gida Dan Tijara basa zaman lafiya da mahaifiyar sa (Hajara Usman) domin yana ganin kamar ba ta son sa tafi son ‘kanwar sa (Husaina Yusuf) duk da ya kasa gane cewa rashin kyauwun halin sa ne yasa mahaifiyar sa ke kyarar sa, domin a gaba ta yake shigo da karuwar sa cikin gidan da nufin shiga daki da ita, amma mahaifiyar sa ta hana shi aikata hakan. Haka daga cikin manyan unguwa akan sami wadanda zasu kai ‘karar rashin kirkin sa ga mahaifiyar sa, amma da zarar ta fada masa yadda sukayi sai yaje wajen dattijon da ya kawo ‘karar yaci mutuncin sa. A wannan lokacin ne wani attajirin me kudi (Babba Hikima) ya soma zuwa wajen ‘kanwar sa da nufin yana son ya aure ta, amma ita sam bata son shi saboda tana da wanda take so, Dan Tijara baya goyon bayan ‘kanwar sa ta rabu da attajirin me kudin da ya nuna yana son ta domin shi ya tsayawa Dan Tijara har ya siya masa mashin din hawa, hakan ce tasa Dan Tijara yake korar ainahin saurayin da ‘kanwar sa take so domin alhajin da ya tsaya masa yake so ta aura. Ganin cewar yarinyar bata son alhajin sai mahaifiyar su ta fito da kanta ta fadawa Alhajin gaskiya akan akwai wanda ‘kanwar Dan Tijara take so, haka ya hakura ya tafi ba don yaso ba. Bayan dan wani lokaci a sanda bikin ‘kanwar Dan Tijara ya taso, sai mahaifiyar su ta shiga damuwa saboda rashin samun kudin da zasuyi hidimar biki dasu, hakan ne yasa ita da ‘yar ta suka yanke hukunci akan su dauki akuyar da Dan Tijara yake kiwo su siyar don su sami kudin yin hidima lokacin biki, bayan an kira me soyan akuya yazo ya dauka ya tafi, sai Dan Tijara yazo gidan neman akuyar sa bai amma bai gani ba, da ya neme ta ne sai mahaifiyar sa ta fada mishi cewar sun sitar da akuya kuma ta tada masa dalilin ta nayin haka gami da alkawarin bayan biki zata sayo masa wata akuyar ta hada masa da riba ta mayar masa, amma Dan Tijara ya nuna sam bai yarda da hakan ba ya zama dole a biyashi akuyar sa, nan fa suka soma rigima da mahaifiyar sa daga bisani kuma yaci alwashin daukar mataki. Lokacin da aka soma bikin ‘kanwar Dan Tijara bayan an kawo kayan lefe da komai ana tsaka da shagalin biki a sanda gayyar mata suka cika gidan, a wannan lokacin ne Dan Tijara ya iso ‘kofar gidan su tare da ‘yan sanda a mortar su, kuma ya soma rokar ‘yan sanda akan kada su sassautawa mahaifiyar sa suyi mata duk abinda ya dace, nan fa akayi sallama da mahaifiyar sa, bayan ‘kanwar sa ta fito taga wadanda suke sallama ne taje ta fada mata, haka mahaifiyar sa ta fito suka shiga motar ‘yan sanda don zuwa wajen hukuma. Bayan tafiyar su wajen hukuma ne mata ‘yan biki suka soma jajen amarya da mahaifiyar ta, a sannan ne Dan Tijara ya shiga gidan kuma ya fada musu rashin mutuncin da ya tafka, sannan suma yaci mutuncin su. Wasu saga cikin mata ‘yan biki sun je har wajen hukumar ‘yan sanda da nufin su karbo mahaifiyar Dan Tijara, amma basuyi nasarar karbo su ba sai ma tabbatar musu da akayi bayan dan wani lokaci za’a tura maganar zuwa kotu. A wannan lokacin ne Dan Tijara yaje wajen alhajin dake soyayya da ‘kanwar sa yayi masa ‘karya don a daukar masa lauyan da zai tsaya masa, anan ne ya hada shi da wani lauyan sa wato Sa’idu ‘koki (Baballe) wanda ya kira Dan Tijara suka zauna yaji duk abinda ke faruwa, bayan an shiga kotu ne aka soma shari’a wadda Jama’a sukayi mamakin jin Dan Tijara na ‘karar mahaifiyar shi. A ‘karshen shari’ar ne al’kali ya kori shari’ar saboda ganin bata da wani tushe bare makama.

A bangare daya kuma sarkin garin su Dan Tijara (Ali Nihu) ya samu labarin abinda ya faru daga bakin matar sa (Halima Atete) wadda sarkin gida (Bala Chiroki) ya fada mata labarin Dan Tijara wanda yakai ‘karar mahaifiyar sa zuwa kotu. Jin abinda ya faru ne yasa Sarki ya bukaci azo masa da Dan Tijara, bayan an kawo sa ne aka soma yi masa hukunci na ‘kuntatawa. Data bisani aka kira mahaifiyar sa da makwabcin su wanda ya bada labarin cewa ishara ce Allah ya nuna wa Dan Tijara domin mahaifinsa kafin ya dasu mutum ne shi mai aibata ‘ya’yan wasu.

Bayan dan lokaci kadan sai Dan Tijara ya shiryu ya zama mutum nagari har ya soma ‘ko’karin taimakawa mahaifiyar sa da abubuwan bukata kuma yaje gidan ‘kanwar sa ya nemi gafarar ta da ta mijin ta.

 

Abubuwan Birgewa:

1- Labarin ya nishadantar, musamman Musa Mai Sana’a yayi ‘ko’kari sosai wajen nishadantar da jama’a.

2- An nuna darasi ga wasu iyayen masu aibata ‘ya’yan wasu.

 

Kurakurai:

1- Lokacin da jami’an tsaro suka zo don tafiya da mahaifiyar Dan Tijara bai kamata me kallo yaga an bude mata murfin mota ta shiga wajen zaman marasa laifi ba. Ya kamata ta zauna a kujerun baya inda ake saka kowane mai laifi da aka kama shi.

2- Bayan mahaifiyar Dan Tijara ta siyar da akuyar sa, me kallo yaji lokacin da mahaifiyar Dan Tijara ta fadi cewar da kudin akuyar ta sayi buhun shinkafa guda biyu, da kaji guda goma gami da naman rago. Shin a wane irin farashi aka siyar da akuya guda daya wadda har kudin suka kai adadin da akayi hidindimu masu yawa haka? Ya dace a samar da wani dalilin yadda akayi ta samu kudin yin hidimar biki masu yawa haka, domin kudin akuyar da aka fada bazai kai adadin da za’ayi manyan siyayya dasu haka ba.

3- Lokacin da akayi shari’ar su Dan Tijara a kotu, zantukan da lauya Sa’idu ‘Ko’ki yake yi bai yi kama da ainahin yadda lauyoyin gaske suke magana a gaban al’kali ba, domin babu nutsuwa ko cikakken ladabi a yanayin yadda yake magana a kotun.

4- Sa’insar da lauyoyin kotun suke yi a tsakanin su kuma a gaban al’kali da sauran jama’a, sam hakan bai kamata ba. Sannan kuma sutturar dake jikin lauyoyin batayi kama da ainahin yadda lauyoyin gaske suke saka suttura ba. Musamman kayan dake jikin Sa’idu ‘Ko’ki yafi rashin kama da na ainahin lauya.

5- Camera tayi rawa a lokacin da Sarki ya fara fitowa harabar gidan sa don zuwa fada.

6- Scene din da akayi na biyun ‘karshe wanda ma’kocin su Dan Tijara yake yiwa wata futsarrariya nasiha yayinda ta rusa ihu yaji tsoro ya gudu. Wannan scene din sam bashi da ala’ka da labarin, kuma wane sa’ko ake son isarwa a wajen?

 

Karkarewa:

Labarin ya nishadantar kuma an nuna darasi ga iyayen da ke aibata ‘ya’yan wasu, amma hukuncin da Dan Tijara ya yanke wajen kai mahaifiyar sa ‘kara kotu yayi tsauri, kuma hakan dabi’ar turawa ce ba ta musulmi ko kuma dabi’ar bahaushe ba. Haka kuma ya dace a nunawa Dan Tijara wani babban darasi don a ‘kara nunawa mai kallo illar wulakanta iyaye, domin hukuncin da akayi masa yayi ‘karanci idan akayi duba da irin cin mutuncin da yayiwa mahaifiyar sa. Wallahu a’alamu!
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: