Sharhin Fim Din (Sandar Makauniya)

Daga: Musa Ishak Muhammad.

Suna: Sandar Makauniya.
Tsara labari: Aminu Uba Mai Dawa.
Kamfani: A.A. Production.
Daukar Nauyi: Anas Ali.
Shiryawa: Yunusa Mu’azu.
Bada Umarni: Ali Gumzak.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Sadik Sani Sadik, Malam Inuwa, Rabi’u Rikadawa, Anas Ali, Fati Zinariya, Amal Umar, Jamila Nagudu, Hadiza Muhammad, Ladidi Fagge, Ladi Mutukaraba, da sauransu.
Fim din Sandar Makauniya fim ne da a ka gina shi a kan labarin wata baiwar Allah mai suna Karime (Fati Zinariya) wadda ta samu kanta cikin wani yanayi matsananci, sakamakon riko da mahaifiyarta ta tafi da ita a gidan sabon mijinta.
A farkon fim din an nuna wani Bafulatani mai suna Gidado, wanda ya je makabarta domin yin addu’a. Ya na cikin yin wanna addu’ar ne kawai sai yaga kabarin da ya ke kusa da shi ya na motsi, ai kuwa chan sai ga wata mace ta na fitowa daga cikin wanna kabari ta taso ta na tunkaro inda ya ke, ga ta kuma dauke da tsohon ciki. Ai kuwa nan take sai Gidado ya tashi da gudu, ya na fitowa daga cikin makabartar ne sai ya hadu da Baffansa (Rabi’u Rikadawa), sai ya fada masa abunda ya gani, shi ne sai su ka koma su ka taho da ita gidansu domin su taimaka mata.
Daga nan ne su ka ci-gaba da taimaka mata da addu’o’i da kuma magunguna har ta samu ta haifi danta namiji. Daga nan ne Karime ta samu baki, kuma ta kwashe labarinta duka ta bawa Baffa da Iyalansa wato motarsa (Hadiza Muhammad) da dansu Gidado.
Ta basu labarin cewa ita dai tun farko marainiya ce wadda ta rasa mahaifinta tun ta na da shekaru 13, daga nan ne mahaifiyarta ta sake aure kuma ta tafi da ita gidan sabon mijinta a matsayin Agola. Sai dai da ita da mahaifiyartata wato (Ladi Mutukaraba) sun kasa samun jin dadin gidan, sakamakon matsi da kiyayya da su ke fuskanta daga gurun kishiyar mahaifiyartata wato (Ladidi Fagge) da kuma ‘yarta Hama (Jamila Nagudu). Kiyayyar tasu ta kara bayyana ne karara, a lokacin da Abashe (Ali Nuhu) dan gidan Mai gari ya auri Karime. Wannan aure bai yi wa Hama da mahaifiyarta dadi ba, domin kuwa Karime ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali a gidan Abashe. Wannan dalili ne ya saka su zuwa gidan boka domin su samu nasarar ganin Hama ta auri Abashe.Hakan kuwa a ka yi, domin kuwa ya aureta. A lokacin da Karime ta samu ciki ne sai hankalin su Hama ya kara tashi domin boka ya ce musu ka da su bari Karime ta riga Hama haihuwa a wannan gida. A sakamakon haka ne su ka yanke shawarar binne Karime da ranta wanda hakan ne har ya saka su Gidado da Baffansa su ka tsince ta a makabarta.
A karshe dai asirinsu ya karye domin kuwa Abashe ya maida matarsa Karime gidansa sannan ya yi wa Hama saki uku, yayin da ita ma mahaifiyarta ta samu saki uku a wannan lokaci, wanda hakan ya zima silar haukacewarsu dukan su. Shi ma kuma boka a nashi bangaren ya yanke jiki ya fadi wanda hakan ya zama silar mutuwarsa.
Abubuwan Yabawa
1. Labarin fim din mikakken labari ne, domin kuwa bai yanke ba tun daga farko har karshe.
2. An nuna karshen mugaye da masu mugun nufi ba ya yin kyau, kamar yadda ya faru ga Hama da mahaifiyarta.
3. An nuna cewa tabbas mahakurci mawadaci ne kamar yadda ya faru ga Karime da mahaifiyarta.
4. Fim din ya samu aiki mai kyau, sauti da hotuna sun fita radau.
Kurakurai
1. Sunan fim din zai ba wa mai kallo wahalar danganta fim din da ma’anar sunansa.
2. An nuna cewa Abashe Dan Mai gari ne, amma ba a taba nuna mahaifin nashi a fada ko da wata alama ta sarauta ba.
3. Ta ya ya Hama da mahaifiyarta su ka binne Karime da ranta?
4. Ya ya a ka yi har a ka binne Karime rana-tsaka amma ba tare da anga wadanda su ka binne ta ba.
5. Ko kadan ba a nuna mahaifan Karime ko Abashe su na neman ta ba a lokacin da ba su ganta ba bayan su Hama sun binne ta da ranta.
karkarewa
Fim din Sandar Makauniya fim ne mai cike da darusa masu tarun yawa. Fim din ya bayyana illar gina ramun mugunta, sannan ya nuna cewa duk wanda ya dogara da Allah, to Allah zai isar masa. A takaice fim din ya samu nasarori da yawa, kuma ba a samu kurakurai da yawa a ciki ba.

 

Exit mobile version