Musa Ishak Muhammad" />

Sharhin Fim Din “Ta Leko Ta Koma”

Suna: Ta Leko Ta Koma.

Tsara labari: Saifullahi Saif.   

Kamfani: G.G Films Production.

Daukar Nauyi: G.G Films Production.

Shiryawa: Sani Mai Iyali.

Bada Umarni: Ali Gumzak.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Nuhu Abdullahi, Abdul M. Shariff, Haseeya Ahmad, Shehu Hassan Kano, Hadiza Muhammad, Hajara Usman. Da sauransu.

Fim din “Ta Leko Ta Koma”, labari ne na wata baiwar Allah mai Suna Ummi wato (Haseeya Ahmad) wadda ta kasance cikin wani mawiyacin hali sakamakon rashin iyayenta da kuma rashin  masoyinta, wanda kuma shi ne jigo a cikin rayuwarta tun bayan rasuwar mahaifiyarta. Ita dai Ummi ta kasance makauniya ce ba ta gani, kuma tana rayuwa ne tare da mahaifiyarta wato (Hjara Usman) da kuma kaninta Abba a nan gidansu.

Watarana Ummi sun fita da kaninta Abba yana yi mata jagora, shi ne ya tafi yabar ta ita kadai a kan titi ,hakan ya saka har mai keke ya kusa buge ta. To a wannan lokacin ne sai ga wani saurayi mai Suna Sani wato (Nuhu Abdullahi) ya zo ya taimaketa. Daga nan kuma ya maida su gida, sannan ya shiga har ciki ya gaida babar tasu, sannan ya nemi a yi masa alfarma da ya ringa zuwa gidan. A lokaci kadan suka shaku da Sani sosai, kuma yana taimaka musu sosai da kayan abinci da kuma sauran bukatunsu.

Bayan an kwna biyu ne, sai Sani ya kawo kudurin cewa  zai turo a yi maganar aurensu da Ummi, kuma shi zai yi musu duk wata dawainiya da ake yi ta aure. Ana cikin wannan maganar auren ne sai Allah ya yi wa mahaifiyar Ummi rasuwa sakamakon rashin lafiyar da ta yi fama da ita. Bayan rasuwarta ne, sai Sani ya ci-gaba da kula da Ummi da kuma kaninta. A sakamakon hakan nema ya dauke ta ya kai ta asibiti sannan ya dauki nawin biyan kudin da za a yi mata aikin ido da shi, kuma Alhamdulillah an samu nasara a aikin da aka yi a karkashin kulawar Dr. Ahmad wato (Shehu Hassan Kano.)

Bayan an samu nasara a aikin ne, shi ne Dr. Ahmad ya fadawa Sani cewa ai nan da awa uku za a budewa Ummi idanunta bayan bandejin da aka saka a idon bayan an yi aikin. Daga nan Sani ya shiga dakin da Ummi take suna farin ciki da samun labarin cewa anjima kadan za abude idon domin ganin nasarar da aka samu. Shi ne yake fada mata bari ya je ya yi wanka ya dawo kafun awa ukun. Bayan ya fita ne sai aka ji shiu shiru har fiye da awa ukun ma, gashi kuma Dr. Ahmad yana so ya gama ya koma Kano. A na cikin wannan yanayin ne sai ga Abba kanin Ummi ya shigo yana kuka yana fada musu cewa ai wasu mutane sun kashe Sani. A nan ne Ummi ta yi ta kuka tana cewa ita kawai Dr. Ahmad ya rufe mata idonta ta hakura da ganin.

Duba da irin halin da Ummi take ciki ne na rashin mahaifiyarta da kuma Sani wanda shi ne kadai garkuwarta, kuma shi kadai ne wanda ta sani, hakan ne yasa Dr. Ahmad ya dauke ta ya taho da ita gidansa domin ya taimaka musu ya kuma basu kulawa duba da irin yanayin da Ummi ta samu kanta bayan rasuwar Sani. A haka dai Dr. ya yi ta kokarin basu kulawa dukkansu tare da hadin gwiwar matarsa Fatima wato (Hadiza Muhammad), Wadda ita ma ta rike amanarta sosai tamkar ‘yar da ta haifa a cikinta.

Rayuwar Ummi ta fara chanjawa ne a lokacin da suka fita yin siyaya da ita da matar Dr. inda a nan ne wani saurayi mai suna Kamal ya ganta, kuma nan take ya ji ya kamu da sonta. Ya yi kokarin sanar da ita halin da yake ciki sai dai ko kalma daya bata fada masa ta kama hanya ta yi tafiyarta. Daga nan sai ya dauki mota ya bi su har sai da yaje gidansu sannan ya tsaya yana jiran ko wani zai fito daga cikin gidan. Yana cikin jiran ne can sai ga Dr. ya fito, shi ne ya je ya same shi ya ke fada masa abinda ya kawo shi, sannan ya nemi a yi masa izini ya fara zuwa gurinta.

Bayan wani dan lokaci kadan Kamal ya yi nasarar samun soyayyar Ummi, sun shaku sosai kuma har magnar aure ta shiga. Ana daf da yin auren ne labari ya fara chanjawa, bayan da wata rana kwatsam aka kirawo Kamal a waya cewa dan uwansa da ya bata watanni takwas da suka wuce an same shi a asibiti. Ashe dai Sani tsohon saurayin Ummi da aka yi zaton ya mutu, ashe shi ne dan uwan Kamal. To bayan Kamal ya dakko Sani daga asibiti ne sai su ka dawo gida su ka shirya su ka fita wajen baikon Kamal da Ummi da ake yi a wannan ranar.

Zuwansu ke da wuya, sai Sani ya ga Ummi ce budurwarsa matar da Kamal zai aura, amma sai ya danne bai nuna masa ya santa ba. Ita kuwa daman Ummi bata son fuskar Sani ba, tunda bata taba ganinsa ba tunda lokacin da suka yi soyayya ita makauniya ce. A haka dai ya yi ta nisanta kansa da Ummi ya ki bari su hadu saboda kar ta gane muryarsa. Wata rana kwatsam ba zato sai Ummi ta ji muryar Sani, kuma ta ji tabbas muryar saurayinta ne. Amma ba ta yi saurin nuna ta gane shi ba, har sai da tayi dogon bincike sannan da ta gano shi ne sai ta fara yunkurin yadda za a yi ta sanar da shi.

A lokacin da Ummi ta tabbatar da cewa Sani shi ne fa saurayinta, sai ta fara juyawa Kamal baya domin ita Sani ne zabinta kuma tana so ta koma gareshi. Amma shi a nashi bangaren Sani ya nuna ya hakura ya barwa dan uwansa Kamal ya aure ta. To abubuwa suka fara yawa ne, shi ne aka kira zama na musamman tsakanin iyayen Kamal, da Kamal din da Sani da Ummi da kuma Dr. Ahmad. Wanda a karshe bayan Ummi ta bada labarin duk abinda ya faru,  shi ne aka bawa Kamal hakuri aka ce ya bari Sani ya auri Ummi tunda daman shi ne masoyinta na farko kuma har yanzu suna son junansu. A nan shi ma Kamal ya amince da auren na Sani da Ummi.

ABUBUWAN YABAWA

1. Sunan fim din ya dace da labarin.

2. Jaruman sun yi kokari wajen isar da labarin yadda ya kamata.

3. An nuna tasirin soyayyar gaskiya.

4. Hotuna da sauti sun fita radau.

5. An samu kalamai masu dadi da kayatarwa a cikin fim din.

6. Babu sarkakiya a cikin labarin, mikakken labari ne mai saukin fahimta a gurun mai kallo.

KURAKURAI

1. A fitowa ta farko an hasko titi har na tsahon dakika 22, amma ba a nunawa mai kallo ko mutum daya ko wata mota da take nuna alakar titin da fim din ba.

2. Idan har ana so a nuna fitowar farko da aka hasko titi tana da alaka da fitowa ta biyu da aka nuno Hjiya Fatima da ummi a shagon siyayya, to ya kamata tsahon dakikun da aka dauka ana hasko titin ace an hasko su a titin suna tafiya izuwa shagon.

3. Sautin wakar turanci da aka saka a lokacin da Kamal yake wa Ummi magana a shagon siyayyar sam ba ta dace da gurun ba.

4. An samu maimaituwar fitowar da Kamal yake fadawa Sani cewa ai Ummi tana kofar gida za ta shigo gidansu har sau biyu. Bayan an gama wannan fitowar kuma sai kawai wannan fitowar dai ta kara maimaituwa, wadda kuma ya kamata ace an cire daya kafun a saki fim din ya zo kasuwa.

5. Kiran waya kawai da aka yi aka ce Kamal ya zo asibiti, ya yi kadan wajen gamsar da mai kallo alakar da ke tsakanin Kamal da Sani, ya kamata ace an zo da wani abu gamsasshe da zai bayyana alakar tasu.

KARKAREWA

Wannan fim na “Ta Leko Ta Koma” fim ne da ya dace da labarinsa. Kuma ya samu aiki mai kyau, kuma ya yi nasarar isar da sakon da ake da burin isarwa. Sannan ya kamata masu ruwa-da-tsaki su ringa maida hankali sosai wajen ganin an kauda kowacce matsala da za ta iya kawowa fim matsala wajen samun karbuwa a gurun masu kallo.

Exit mobile version