Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim din ‘Tsananin Rabo’

Published

on

Suna: Tsananin Rabo.
Labari: Nabil Salisu.
Tsara Labari: Yusuf Uba.
Kamfani: Girma International.
Daukar Nauyi: Bilkisu M. Ahmad .
Shryawa: Bashir Girma.
Bada Umarni: Babannan Sulaiman One Boy.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Isah Feriskan, Bashir Girma, Tsalha Dandano, Ahmad Aliyu Tage, Baba Labaran Ahmad, Hajiya Mama, Zainab M. Ahmad, Bilkisu Alhassan, Saratu, da sauransu.
Fim din Tsananin Rabo fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani matashi mai suna Dan Bala( Isa Feriskan) mai sayar da mangwaro. Shi dai Dan Bala ya kasance ya na da wata budurwa wadda su ka dade su na soyayya da ita mai suna Talatu, kwatsam watarana sai wani Attajiri ya zo ya ce ya na son ta. Kuma ya na zuwa sai ya yi amfani da kudinsa wajen siye ra’ayin mahaifinta. Kuma ya yi nasarar shawo hankalin nasa domin kuwa ya tsaya tsayin-daka a kan cewa lallai sai Alhaji ya auri ‘yarsa Talatu.
Ita kuwa a na ta bangaren Talatu ta na tsananin kaunar Dan Bala, kuma ta ki bawa Alhaji kofar shiga zuciyarta. Ya yi dukkanin kokarinsa amma abun ya ki ya yiwu. Kuma ga shi sai hidima ya ke mata da ita da mahaifinta. Dan Bala shi ne zabinta Kuma shi ta ke so, Talatu ta sanarwa da mahaifinta hakan. Sai Dai shi ya ce ya na nan a kan bakarsa cewa lallai sai Talatu ta auri Alhaji ko ta na so ko ba ta so.
A haka dai Dan Bala da Talatu su ka ci-gaba da zama cikin damuwa, duk da cewa su na son junansu to amma fa rashin kudi ya na nema ya kawo musu tsaiko wajen mallakar junansu. Shi dai Dan Bala ba shi da sana’a mai karfi wadda zai iya yin aure da ita. Kuma chan ga Alhaji ya na musu barazana da kudi. Komai sai kara chakude musu ya ke. A na cikin wannan hali ne sai abokin Dan Bala ya ba shi shawarar cewa mai zai hana tunda Alhaji ya na son Talatu sosai ta matsa masa ya sama masa wani aiki da zai ringa yi ya na biyan shi. Bayan wannan shawara ne sai Talatu ta sanar da Alhaji abunda ta ke so ya yi mata, nan take ya amince ya dauki Dan Bala aiki a gidansa.
A karshe dai mahaifin Talatu ya juyawa Alhaji baya inda ya ce sam ba zai ba shi auren ‘yarsa ba, tunda ya bincika ya gane cewa ya fiya auri-saki kuma ba ya haihuwa. Saboda haka maganar aure a tsakaninsu babu ita ko kadan. Bayan an kori Alhaji, sai a ka bawa Dan Bala dama ya fito ya nemi auren Talatu kuma har a ka saka mu su ranar aurensu.
ABUBUWAN YABAWA
1. Sunan fim din ya dace da labarinsa.
2. An nuna tasirin soyayya ta gaskiya kamar yadda ta faru a kan Dan Bala da Talatu.
3. An nuna cewa ba komai ne kudi ya ke iya mallakawa bawa ba kamar yadda ya faru a kan Alhaji.
4. Labarin fim din bai yanke ba tun daga farko har karshe.
5. An samu sauti mai kyau a cikin fim din.
6. Ba a samu matsalar hotuna ba a cikin fim din, komai ya dauku radau.
KURAKURAI
1. An samu matsalar Editin, domin an samu maimaituwar maganganu da kuma hotuna mabanbanta a wasu gurare.
2. Mutum ya dauki saurayin budurwarsa aiki alhalin kuma ya san ba rabuwa su ka yi ba, wannan bai fiya kasancewa ba a cikin wannan zamani.
KARKAREWA
Fim din Tsananin Rabo ya samu nasarar isar da sakon da ya dakko. Fim din ya samu tsaruwar labari, kuma ya rike mai kallo daga farko har karshensa. Fim din ya dan samu kurakurai kadan, amma nasarorin da ya samu sun fi kurakuren yawa nesa ba kusa ba.
Advertisement

labarai