Sharhin Fim Din ‘Uwa Biyu’

Daga: Musa Ishak Muhammad

Suna: Uwa Biyu.
Labari: Haidar M. Aliyu.
Tsara Labari: Haidar M. Aliyu.
Daukar Nauyi: Taneem Sanity.
Shiryawa: Shamsu Dan Hajiya.
Bada Umarni: Abubakar S. Shehu.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad
Jarumai: Sadik Sani Sadik, Bilkisu Abdullahi, Yusuf S. kura, Baba Karkuzu, Abubakar S. Shehu, Taneem Sanity, Habiba Adamu, Babai Aliyu Bauchi, Abdullahi Saleh, Shamsu Dan Hajiya, Ummi Me Kyau.
Fim din Uwa Biyu, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wata mata (Ummi Me Kyau) matar (Sadik Sani Sadik) wadda Allah Ya azurta su da samun ‘ya mace. Ita dai wannan ‘yar tasu ta samu shakuwa sosai-sosai da malamar makarantarsu wato (Bilkisu Abdullahi). Malama ta na yawan bibiyar yarinyar, watarana ma har gidanta ta kai ta. Ita kuma babar yarinyar a na ta bangaren ta kasa samun sukuni a kan alakar ‘yarta da malamarta, domin ta yi wani mafarki wai malamar ta kwace mata ‘yar daga hannunta. Hakan ne yasa kullum ta ke kasa samun nutsuwa.
A na cikin hakan ne watarana, sai babar yarinyar nan ta zo daukar ta a makaranta amma ba ta same ta ba, ta tafi gidan malama, ita ma ta ce ba ta son inda ta yi ba. Nan da nan hankalinta ya tashi, kawai sai ta tafi wajen ‘yan sanda ta na karar malama a kan sace mata ‘yarta. Nan fa a ka je a ka kamo malama a ka fara binciken ta a kan batan yarinyar nan. Sai chan daga baya a ka gane cewa malama ba ta da hannu cikin batan yarinyar nan domin ashe yarinyar ma gidan kakanninta ta tafi bayan an tashi daga makarantar.
A karshen fim din dai an gano ashe ita yarinyar ma asalin ‘yar malamar ce ta cikinta. Shi Sadik Sani Sadik ba su ne mahaifanta ba, lokacin da ya kawo matar tasa asibiti za ta haihu sai ta haifi yaron ba rai, a lokacin ita kuma malama ta yo cikin shege daga kauye, ta zo ta haife ta a asibiti sai ta gudu. To a nan ne shi Sadik Sani Sadik ya nemi alfarmar a maye masa gurbin jaririnsa da wannan yarinyar zai rike ta bisa amana kamar shi ya haife ta. A karshe dai malama ta yi alkawarin barwa su Sadik Sani Sadik yarinyar su, sai dai shi ma ya nemi alfarmar auren ta, kuma ta amince.
Abubuwan Yabawa
1. Fim din ya dace da sunansa, domin sunan ya dace da labarin.
2. Labarin fim din bai yanke ba tun daga farko har karshe.
3. An samu aiki mai kyau a cikin fim din.
4. Babu matsalar sauti ko hoto a fim din.
5. An nuna illar zaluntar ‘ya’yan mutane, kamar yadda ya faru a cikin fim din.
6. An nuna muhimmancin kyautatawa mutane zato.
karkarewa
Fim din Uwa Biyu fim ne da ya samu nasarori da yawa. Kuma yanayin aikinsa ne ya sa ya samu karbuwa a wajen masu kallo. Fim din ya tafi ba tare da yankewa ba. Kuma fim din ya samu nasarori da yawa, yayin da ya rasa watta babbar matsala ta zahiri a ciki. Fim din an yi kokari sosai a ciki.

 

Exit mobile version