Sharhin Fim Din ‘Wani Labari’

Daga: Musa Ishak Muhammad

Suna: Wani Labari.
Kamfani: MB ENTERTAINMENT.
Labari: Yusha’u Idris.
Tsara Labari: Yusha’u Idris.
Daukar Nauyi: MJ BIGMAN
Shiryawa: AbdulKadir M Hassan Sanka.
Bada Umarni: Yusha’u Idris Umar.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad
Jarumai: Shehu Hassan Kano, Haj. Zilai Gaida, Umar Gombe, Amina Meenat Muhammad, Mas’ud Umar M.M Sidi, Yusha’u Idris Umar, Ahmad Atamby, Bashir S. Dorayi, Jamila Gwers da sauransu.
Fim din Wani Labari, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani matashi mai suna Abubakar (Umar Gombe) da sabuwar amaryarsa mai suna Zulaihat(Amina Meenat Muhammad) da kuma maigidansa wato Alhaji Sadi(Shehu Hassan Kano). Shi dai Abubakar ya kasance ya na aikie ne a karkashin Alhaji Sadi, domin kuwa ya na aiki ne a kamfaninsa. Watarana Abubakar sai ya kawo maigidansa Alhaji Sadi yarinyar da zai aura wato Zulaihat domin ta zo su gaisa da Alhajin ya ga wadda zai aura. Ai kuwa daga zuwanta ofis din ne fa, Alhaji ya kyallara ido ya gano ta. A nan take sai ya cewa Abubakar ya bashi dubu hamsin ya karasa shirye-shiryen biki, sannan zai ba shi gida a cikin gidajensa domin ya zauna, sannan ita kuma Zulaihat ya bata dubu ashirin. Shi Abubakar bai sani ba ashe Alhaji son Zulaihat ya ke.
Bayan an yi auren Abubakar da Zulaihat ne ba dadewa sai Alhaji ya fara bibiyar Zulaihat, daman ya samu lambar wayarta. Alhaji sai ya ringa amfani da aikin da Abubakar ya ke a karkashinsa, sai ya ringa ba shi aiki masu yawa, kuma ya ce masa kar ya je ko’ina har sai Alhajin ya je uzurinsa ya dawo. Ashe idan ya fita gidan Abubakar ya ke tafiya wajen Zulaihat. Shi Abubakar sam bai san da cin amanar da Alhaji su ke yi masa ba shi da Zulaihat.
A na nan ne watarana kamar yadda Alhaji ya saba, Abubakar ya na zuwa wajen aiki sai ya kirawo shi ya ba shi a aiki ya ce masa ya yi aikin nan shi zai je unguwa ya dawo, amma ko ya gama aikin kar ya tafi har sai Alhajin ya dawo, sai Abubakar ya ce masa to, ya zauna ya ci-gaba da aikinsa. Ashe Alhaji gidan Abubakar ya tafi. Ai kuwa ya na zuwa gidan nan, ashe abun ya zo wa Alhaji da karewar kwana, kawai sai Alhaji ya mutu a cikin gidan Abubakar. Zulaihat gaba daya ta rikice ta rasa ya za ta yi. A chan ma wajen aiki su Abubakar su na ta zaman jiran Alhaji. A karshe dai wani ya zo ya fada musu cewa ya ga motar Alhaji a wata unguwa, a na zuwa kuwa sai ga mota a kusa da gidan Abubakar. A na ci-gaba da matsawa da bincike sai ga gawar Alhaji nan a cikin gidan Abubakar. Nan da nan Abubakar ya saki Zulaihat, kuma ‘yan sanda su ka tafi da ita, domin ci-gaba da bincike.
ABUBUWAN YABAWA
1. Fim din ya dace da sunansa.
2. Labarin fim din ya tsaru, domin bai yanke ba tun daga farko har karshe.
3. An nuna muhimmancin daina aikata barna, domin mutum bai san a Ina ne za a karbi rayuwarsa ba, kuma bai san a wanne yanayi bane.
4. An nuna illar biyewa son zuciya kamar yadda Zulaihat ta yi.
Kurakurai
1. An samu matsalar hotuna a cikin shirin.
karkarewa
Fim din Wani Labari, fim ne da ya samu nasarori sosai, domin abubuwan yabawa a cikin shirin tabbas sun fi kurakuran cikinsa yawa. Fim din ya samu karbuwa a wajen masu kallo, kuma ya yi nasarar isar da sakon da ya ke dauke da shi ga masu kallo.

Exit mobile version