Musa Ishak Muhammad" />

Sharhin Fim Din ‘Wukar Fawa’

Suna: Wukar Fawa
Tsara labari: Nura Mustafa Waye.
Kamfani: Tarore Inbestment.
Shiryawa: Abdullahi Tarore.
Bada Umarni: Nura Mustafa Waye
SHARHI: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Bashir Nayaya, Kawu Habibu, Lawan G. Taura, Malam Inuwa, Abdul Kabeji, Khadija Kyari, Maimanatu Wata Yarinya, Hajiya Zulai, Hajiya Magajiya, Ummi Gombe da sauransu.
Labarin fim din wukar fawa labari ne akan wasu al‘ummar Fulani da kuma Mahauata wadanda suke rayuwa a gari guda. A farkon fim din an nuno sarkin fawa (Lawan G. Taura) suna tattaunawa da wani Bafulatani a tebirinsa da yake saida nama. Suna ta zolayar juna har Bafulatanin nan yake fadawa Sarkin fawa cewa rigima tsakanin FuLani da Mahauta rigima ce ta gado saboda haka har abada ba za su daina ta ba.
Wannan gari dai ya hada kabilu ne guda biyu da suke rayuwa a gari daya karkashin jagorancin mai gari da kuma mai unguwa wanda shi ma Bafulatani ne, sai kuma Sarkin fawa wanda shi ne yake wakiltar Mahautan wannan gari. Duk da cewa wadannan mutane suna zaune ne a gari daya, amma hakan ba ya hana su yin zaman doya da manja, domin kuwa in banda kyamar juna ba abunda suke yi kuma ko auratayya basa yi a tsakaninsu.
Ana cikin wannan yanayi ne kuma sai soyayya ta kullu tsakanin ‘yar gidan Sarkin fawa karimatu (Khadija Kyari) da kuma Sanda (Kawu Habibu) wanda shi kuma Bafulatani ne tsantsa. A haka suka ci-gaba da soyayyarsu duk da tarun kalubale da suka ringa fuskanta a gurun jama’ar gari duba da rashin jituwar da take tsakanin wadannan kabilu guda biyu.
A daya bangaren kuma akwai ‘yar gidan mai gari Zinatu (Maimuna wata yarinya) wadda take tsananin kaunar Sanda wanda shi kuma d’a ne ga baiwar gidansu,amma shi kuma Sanda hankalinsa ya fi karkata ne izuwa karimatu ‘yar mahauta. Bayan soyayyar karimatu ta yi nisa sosai ne, kuma zinatau ta samu kanta a tsananin soyayyar sanda wanda ta kasa samun karkatowar hankalinsa izuwa gareta, wanda ta kai a gidansu mahaifiyarta har gori take mata cewa me za ta yi da d’an baiwa alhalin ita ‘yar sarauta ce kuma mai cikakken gata domin kuwa a duk duniya babu abunda mai gairi yafi kauna kamar ‘yarsa Zinatu. Yana tsananin kaunar ta kuma yana bata kulawa.
A can tsakiyar fim din labarin ya canja salo lokacin da zinatu ta ke fadawa karimatu cewa ita ‘yar tsintuwa ce kuma ba ‘yar halak ba ce, wanda hakan ya matukar tayar mata da hankali wanda kuma hakan ya tilasta mata zuwa ta tambayi mahifinta sarkin fawa wanda a karshe yake fada mata cewa tsintar ta yi, ya raine ta har ta girma. Tayar da wannan sirri da aka yi shi ne ya chanjawa labarin salo domin kuwa mahaifiyar Sanda watoTani (Hajiya Zulai) ta bayyana wani boyayyen aiki da suka taba yi da mai unguwa. Wato aikin chanja jaririyar da aka haifa a gidan mai gari da kuma wadda aka haifa a gidan shi mai unguwwar wanda hakan yake bayyana cewa karimatu da aka tsinta ita ce ainihin ‘yar mai gari wadda Tani ta je ta jefar shi kuma Sarkin fawa ya tsinta, ita kuma zinatu ita ce ainihin ‘yar mai ungyuwa.
A karshe dai mai gari ya kori mai unuguwa daga gari shi da ‘yarsa Zinatu,sai dai tace ce ita ba za ta bi shi ba tafi so ta zauna tare da mai gari, sannan mai gari ya bawa Sanda umarnim auren karimatu nan take, sannan kuma aka fada masa cewa zai auri ita ma Zinatu daga baya.
Abubuwan Yabawa
1. Fim din ya yi kokarin nuna yadda zamantakewa take a tsakanin kabilu mabanbanta.
2. Fim din ya nuna tasirin shugabanci duba da irin karfin iko da mai gari yake da shi a wannan gari.
3. Mahimmancin rike amana duba da irin yadda Sarkin fawa ya rike karimatu.
4. Labarin bai yanke ba tun daga farko har karshe.
5. Fim din ya samu aiki mai kyau,domin akwai ingantattun hotuna da kuma sauti mai kyau.
KURAKURAI
1. A fim din an so a nuna zamantakewar Fulani da Mahauta ne a gari daya,amma sai gashi gidan mahautan daya ne kawai wato gidan Sarkin fawa, yayin da su kuma Fulanin suka mamaye garin.
2. An bayyana sarkin fawa a matsayin sarkin mahauta amma kuma daga shi sai matarsa sai ‘yarsu ta tsintuwa Zinatu su kadai aka nuna a matsayin mahauta. To daman ana samun sarki ba tare da mutanen da za a mulka ba?
3. A lokacin da aka nuno Tani tana tunani bayan ta dawo gari bayan shekaru biyu da ta kwashe bata nan, an nuno ta tana tuna lokacin da Zinatu ta kwada mata mari. Kayan da aka nuno Tani da su kafun ta tafi tunanin,su ne dai a jikinta lokacin da ake marin nata, wanda hakan zai je fa mai kallo cikin kokonto.
4. Me ne ne hikimar mai unguwa idan ‘yarsa ta girma a gidan mai gari kuma a matsayin ‘yar mai gari, wanda hakan yasa aka chanja ‘yar mai gari karimatu da ‘yarsa zinatu?
5. Ya kamata a bayyana Tani tun farkon labarin domin mai kallo yasan dalilin barin ta gari, ba kawai a hasko ta a karshe a ce ta dawo ba.
6. Yawan maimata furucin “Aradun Allah” da mai unguwa yake yi a kowacce Magana ya wuce gona da iri domin ba haka tsarin maganar Fulanin take ba.
KARKAREWA
Labarin fim din yana da matukar mahimmanci duba da irin yadda ake samun zamantakewa ta kabilu mabanbanta musamman a wannan kasa tamu Nijeriya. Samun irin wannan finafinai zai taimaka wajen samun hadin kai da kaunar juna a tsakanin kabilun da Allah ya kaddara yin rayuwarsu a inuwa daya. Sannan ya kamata idan za a yi finafinai irin wadannan, a ringa kula sosai saboda kar a afkawa wata kabilar ko a danganta ta da wani abu da ka iya zama cin zarafi ga kabilar cikin rashin sani.

Exit mobile version