Suna: Yarda Da Amini.
Kamfani: FASAHA Concept.
Labari: Habibu Yaro.
Tsara Labari: Habibu Yaro.
Daukar Nauyi: Hassan Yaro.
Shiryawa: Habibu Yaro.
Bada Umarni: Habibu Yaro.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad
Jarumai: Shehu Hassan Kano, Sulaiman Bosho, Malam Iliyasu, Rukayya Auwal, Zainab Abdullahi, Habibu Yaro, da sauransu.
Fim din Yarda Da Amini, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wasu aminai guda biyu, wadanda su ka yi matukar shakuwa da junansu. Abokan nan wato Saminu (Sulaiman Bosho) da kuma Rabe (Shehu Hassan Kano). Sai dai wata gaba ta shi ka tsakaninsu. Wadda ta kai ‘ya’yansu sun kamu da soyayyar junansu. Amma har an kai kudin auren a ka dawo da su, saboda gabar da ta ke tsakaninsu.
Dalilin gabar tasu ta samo asali ne sakamakon cin amanar da Saminu ya yi wa Rabe, ta hanyar zuga shi ya saki matarsa Jamila, sannan shi kuma ya kewaye ya je ya aure ta. Kullum dai Saminu ba shi da aiki sai dai ya ringa zuga Rabe a kan lallai ya saki Jamila domin ba ta da kirki. A karshe dai Saminu ya yi nasara domin kuwa Rabe ya sake Jamila. Shi kuma kawai sai ya kewaye ya je ya aure Jamila.
To fa tun daga nan gaba mai tsanani ta barke a tsakaninsu, wadda har ta kai ga sun yi burus a kan cewa lallai ba za a yi wannan auren ba. Kuma gashi su yaran nan su na matukar kaunar junansu. A dalilin kaunar da su ke wa junansu ne, da kuma hana su auren da a ka yi, har ta kai sun aikata fasadi, domin har ciki ya shiga tsakaninsu.
Abubuwan Yabawa
1. Labarin fim din ya dace da sunan fim din.
2. Labarin fim din ya tsaru sosai.
3. An samu sauti mai kyau a cikin fim din.
4. An samu hotuna masu kyau ba tare da wata matsala ba a cikin fim din.
5. An nuna illar son zuciya, domin son zuciyar su Saminu da Rabe, ya jawo ‘ya’yansu su ka afkawa barna.
6. An nuna illar cin amana, da kuma irin abunda ta ke haifarwa.
Kurakurai
1. Inda fim din ya kare bai dace ace ya kare a nan ba.
2. Ba a nuna wani mummunan sakamako ga Rabe ba bisa cin amanar amininsa da ya yi.
karkarewa
Fim din Yarda Da Amini fim ne da ya samu aiki mai kyau, kuma ya samu nasarar isar da sakonni muhimmai a cikinsa. Duk da cewa an dan samu kurakurai kadan, amma nasarorin sun rinjayi kurakuren.
Sharhin Fim Din ‘ANGO’
Suna: Ango. Tsara labari: Kaddafi Mai Addu'a. Kamfani: Sultan Films...