A duk shekara gasar firimiya ta kasar ingila tana zama ta daya a manyan gasanni na nahiyar turai koma ince na duniya a matsayin kasar da take fin kowacce gasa kasha kudi wajen siyan sababbin yan wasa a fadin duniya inda kungiyoyin da suke gasar suke kasha makudan kudade wajen siyan manya da kananan yan wasa domin fafatawa a gasar.
Sai dai a wannan shekarar ma haka akayi domin gasar ta firimiya itace gasar datafi kowacce gasa kasha kudi wajen siyan sababbin yan wasa aciki da wajen kasar duk domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
A kakar wasan data gabata ne masana harkokin wasanni suka bayyna cewa za’abuga gasar datafi kowacce gasa zafi ganin yadda manyan kungiyoyin gasar suka kawo manyan masu koyarwa irinsu Antonio Conte da Mourinho da Guardiola da Roland Koyman na Eberton.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ce ta lashe gasar yayinda Tottenham tayi na biyu a gasar sai Asenal tayi ta uku Liberpool ta hudu yayinda Manchester united ta kare a matsayi na biya.
A wannan kakar ta shekara ta 2017zuwa 2018 kungiyoyin gasar firimiya sun kasha kudi fam biliyan daya da miliyan dari hudu da ashirin da biyar, adadin dayafi na kowacce shekara a tarihi.
Kasha ashirin cikin dari na kungiyoyin firimiya da suka hada da Manchester united da Manchester city da Chelsea da Eberton sun kashe sama da fam miliyan dari yayinda kungiyoyi irinsu Westham da Tottenham da Stoke city suka kasha kusan fam miliyan dari.
Kungiyoyi hudu da suke buga gasar sun sayi yan wasa sha uku uku, yayinda kungiyar kwallon kafa ta Asenal ce ta siyi yan wasa kadan inda yan wasa biyu kawai kungiyar ta iya dauka.
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester city ce tafi kowacce kungiya kasha kudi inda ta kasha kudi inda ta kasha fam miliyan dari biyu da ashirin da daya sai Manchester united a matsayi na biyu inda ta kasha fam miliyan dari da arba’in da biyar sai Chelsea a matsayi na uku inda itama ta kasha fam miliyan dari da tamanin da biyar, eberton ce take binsu a baya inda ta kashe fam miliyan dari da arba’in da tara.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tafi kowacce kungiya siyar da yan wasa inda ta tasamu kudi fam miliyan dari da tara wajen siyar da yan wasa da suka hada da Nemanja Matic zuwa Manchester united sai kuma Juan Cuadrado daya koma Jubentus ta kasar italiya.
SAI DAI KO YAYA MANYAN KUNGIYOYIN GASAR SUKE GANIN AMFANIN IRIN SIYAYYAR DA SUKAYI?
ARSENAL
Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal itace kungiyar da bata kasha kudi da yawa a wannan shekarar ba inda ta kawo sababbin yan wasa ne kawai guda biyu, Kolasinac wanda yazo kungiyar batare da sunbiya kudi ba wato (free transfer) sai Aledandre Lacazatte wanda kungiyar ta kasha fam miliyan 48 da dugo takwas ta siyo daga Lyon ta kasar faransa.
Babban abinda kungiyar tayi shine na ganin yuan was anta guda biyu Aledis Sanches da Mesut Ozil wadanda duk a karshen kakar wasannan kwantaraginsu zai kare da kungiyar, dan wasa Aled Odlaid Chamberlain ne dan wasan dayaga bazai iya zama a kungiyar ba inda ya koma Liberpool a ranar da aka rufe kasuwar siyan yan wasa.
Kociyan kungiyar Arsene Wenger yana shan suka daga tsofaffin yan wasan kungiyar irinsu Thierry Henry da sauransu wajen yadda yake tafiyar da kungiyar inda suma masana harkokin wasanni a nahiyar turai suma suka soki kociyan wajen yadda baya siyowa kungiyar manyan yasa yadda kungiyar zata goga da ragowar manyan kungiyoyi a kasar ta ingila.
Acikin wasanni hudu da kungiyar ta fafata a daidai wannan lokaci tasamu nasara a wasanni biyu inda tayi rashin nasara a wasanni biyu.
Kungiyar tasamu nasara a wasan farko wanda ta fafata da tsofaffin zakarun gasar Leicester city da kungiyar Bournemouth a satin daya gabata, sai dai tayi rashin nasara a hannun Stoke city da Liberpool, abinda masana suke cewa kungiyar bazata kai bantanta ba idan har zata dinga karawa da manyan kungiyoyi ganin yadda kungiyar batada manyan yan wasa irin na ragowar.
Sai dai wasu suna ganin sakamakon kungiyar bazata buga gasar zakarun turai ba shine yasa wasu manyan yan wasan suka ki amincewa su shiga kungiyar kuma shine yasa yan wasan kungiyar irinsu Sanches da Ozil sukace zasu bar kungiyar.
Yanzu dai abinda yake gaban mista Wenger shine dawo da kungiyar gasar zakarun turai ta hanyar ganin sun kammala gasar acikin kungiyoyin hudu na farko ko kuma su lashe gasar ta firimiya ko kuma gasar Europa kamar yadda Manchester united tayi.
CHELSEA
Antonio Conte yazo ya karbi Chelsea wadda ta kare a matsayi na 10 a kakar wasan shekara ta 2015 zuwa 2016 inda kungiyar tasha wahala wajen cin wasanni a hannun tsohon kociyan kungiyar wato Jose Mourinho kafin kungiyar ta koreshi .
Zuwansa kungiyar keda wuya ya farfado da martabar kungiyar ta hanyar sake salon buga wasa inda yakoma saka yan wasan baya guda uku a baya sai yan wasa biyar a tsakiya sai kuma uku a gaba.
Wannan salon wasan shine wanda kociyan yayi amfani dashi a tsohuwar kungiyarsa ta Jubentus da kuma tawagar yan wasan kasar italiya.
Kuma wanna salon buga wasanne yasa Conte yasamu nasara a gasar data gabata inda ya lashe gasar firimiya, sakamakon sabon salo dayazo dashi a gasar.
Sai dai kociyan yasamu sabani da masu gudanar da kungiyar wajen kawo sababbin yan wasa inda ya zargi mahukunta a kungiyar wajen rashin mayar da hankali akan yan wasannin da yace yanaso a kawo masa.
Acikin watan agusta ne rahotanni suka bayyana cewa Conte baiji dadin yadda kungiyar ta yadda Manchester united ta doketa ba wajen siyan tsohon dan wasan kungiyar ROMELU LUKAKU.
Haka kuma kociyan ya zargi masu gudanar da kungiyar wajen siyarwa da Manchester united dan wasan kungiyar Nemanja Matic, matakin da tsohon dan wasan kungiyar, Frank Lampard ya bayyana a matsayin gangancin dayafi kowanne a wannan shekarar.
Chelsea tafara kare kambunta da kafar hagu inda tayi rashin nasara a was anta na farko data buga a hannun kungiyar Burnley a filin wasa na Stamford Bridge, sai dai kungiyar ta farfado bayan data lashe dukkannin wasanninta uku data buga a baya kuma tafara gasar zakarun turai da kafar dama inda ta doke kungiyar Karabag daci 6-0 a ranar talata.
Wani mataki da ake ganin Conte yayi mafi muni shine na sanar da dan wasan gaba na kungiyar Diego Costa cewa bazaiyi amfani dashi ba a wannan kakar, Conte dai ya sanar da Costa ta hanya sakon karta kwana cewa babu shi a tsarinsa na wannan kakar, lamarin da yasa dole kungiyar tashiga kasuwa wajen neman dan wasan gaba, inda a karshe ta siyo MORATA daga real Madrid, morata dai yafara wasa da kafar daama a kungiyar domin kawo yanzu yaci kwallaye uku cikin wasanni hudu daya buga kuma ya taimaka anci kwallaye biyu.
Sai dai ko yaya kungiyar zata iya kare kambunta? Shin kungiyar tayi daidai wajen siyar da Matic zuwa Manchester united sannan ta maye grbinsa da wanda bai kaishi kwarewa ba wato Bakayoko?
Shin yaya matsayin Diego Costa yake a kungiyar? Tuni dai aka fara rade-radin cewa dan wasan zai koma tsohuwar kungiyarsa ta Atletico Madrid.
LIVERPOOL
Wasu masana harkokin wasanni suna ganin kociyan Liberpool yayi kokari wajen hana dan wasan kungiyar , Philippe Coutinho komawa Barcelona , sai dai kuma wasu suna ganin kamar bai kamata kungiyar ta zauna da dan wasan daya nuna bayason zama a kungiyar ba.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dai ta taya dan wasan har sau uku a jere inda Liberpool din tace dan was anta bana siyarwa bane, matakin da yakai har sai da dan wasan ya rubuta takardar bukatar kungiyar ta sakeshi.
Liberpool ta samu nasarar kawo yan wasa irinsu Mohammed Salah dan kasar masar daga Roma, sai chamberlain na arsenal wanda shima yakoma kungiyar a karshen watan Agusta.
Duk da cewa kungiyar bata kashe kudi da yaw aba, amma akwai manyan yan wasa irinsu Sadio Mane, firmino, Henderson da Coutinho.
Abinda yake gaban Klopp dai shine yadawo da martabar kungiyar sannan kuma tunda yanzu kungiyar ta dawo zakarun turai dole ya san yadda zaiyi amfani da yan wasansa domin yanzu wasanni zasu karu.
MANCHESTER CITY
Manchester city ce tafi kowacce kungiya kasha kudi a wannan shekarar, inda ta kasha kusan fam miliyan dari biyu da ashirin da daya, sannan ta kasha kusan fam miliyan dari wajen siyahn yan wasan baya, Killy Walker daga Tottenham akan kudi fam miliyan hamsin sai kuma Mendy daga Monaco akan kudi fam miliyan 42, sannan kociyan kungiyar Guardiola ya siyo dan wasan baya na real Madrid, wato DANILO, duk da cewa kociyan yace shi bai siyo Danilo a matsayin dan baya gaba day aba, yace zaiyi amfani dashi a waje daban-daban.
Duk da makudan kudin da kungiyar ta kasha wajen siyan mai tsaron ragab BARCELONA, wato Brabo a kakar wasan data gabata, Guardiola yaga kamar kokarin mai tsaron ragar mai masa abinda yakeso ba, haka yaje yakara kasha kusan sama da fam miliyan 40 wajen siyan maintsaron ragar Benfica, dan kasar Brazil wato Elderson wanda a yanzu haka shine yake kamawa kungiyar idan zasuyi wasa.
Tun a karshen kakar data gabata ne dai Guardiola yafara nunawa dan wasan gaban kungiyar wato Sergio Aguiro cewa yafara gajiya dashi kuma yana bukatar sabon dang aba, sai dai kociyan bai rabu da dan wasan ba, amma masana suna ganin kamar shekara mai zuwa zai rabu da dan wasan.
Ana tunanin kuma zai nemi kungiyar data ta siyo masa Messi, dan wasan da sukayi aiki tare dashi a Barcelona, kuma ana tunanin shima dan wasan zai iya zuwa ganin yadda Neymar yabar kungiyar a wannan kakar.
Tabbas akwai KaluBale akan Guardiola, domin ana ganin yanada damar cin kofin firimiya, domin yafi kowacce kungiya kasha kudi sannan kuma masa suna ganin kungiyarsa ce akan gaba a wajen jadawalin kungiyoyin da zasu iya lashe gasar ta bana.
Kungiyar dai tafara buga wasa da kafar dama, inda yanzu tanada maki 10 kuma tana matsayi na biyu, maki daya da wadda take na daya wato Manchester united.
MANCHESTER UNITED
A tarihin Mourinho duk kungiyar dayaje yana lashe gasar lig na kasar a shekararsa ta biyu a kungiyar, hakan yasa ake tunanin wannan lokacin ma zai iya maimaita wannan tarihin a Manchester united.
Tun a watan juni na wannan shekarar ne dai ya bayyana cewa yana bukatar yan wasa hudu domin kara karfin kungiyar, inda acikin watan agusta kungiyar ta samu nasasr siyan yan wasa guda uku, Bictor Lindelop daga Benfica, Rumelu Lukaku daga Eberton, sai Nemanja Matic daga Chelsea, amma daga bisani ya bayyana cewa ba dole sai yasamu yan wasa hudu ba guda ukun sun ida amma idan yasamu na hudun to daman abinda yakeso kenan.
Zuwan Nemanja Matic tasa dan wasan dayafi kowa tsada a kungiyar wato Poul Pogba yasamu damar matsawa gaba domin a baya shine kusan yake tarewa a kungiyar.
Kuma masana suna ganin daman kamar Mourinho ya tauyewa dan wasan hakkinsa ne domin daman bai kamata ayi amfani dashi ba a lamba hudu.
Kungiyar dai tafar buga wasannin firimiya da kafar dama inda ta lashe wasanni uku na farko kafin daga bisani ta buga canjaras a satin daya gabata a was anta da Stoke city.
Rumelu Lukaku shine dan wasan da kungiyar ta siya fam miliyan saba’in da biyar daga Everton, kuma kawo yanzu ya zura kwallaye hudu a gasar firimiya sannan yaci kwallo daya a wasan zakarun turai da kungiyar tafara bugawa a ranar talata.
Tuni dai aka bayyana kungiyar ta Manchester united a matsayin kungiyar da itama zata iya lashe gasar ta bana ganin yadda a halin yanzu suke buga wasa mai kyau.
Yanzu dai abinda yake gaban Mourinho shine ganin ya lashe gasar firimiya ta wannan shekarar domin ya dora akan nasarar daya samu a shekarar data gabata inda kungiyar ta lashe gasar cin kofin lig da kuma gasar Europa wadda itace tabawa kungiyar damar zuwa gasar zakarun turai.
TOTTENHAM
Tottenham ce ta kare a matsayi na biyu a shekarar data gabata, wanda hakan yasa ake tunanin suna bukatar manyan wasa domin ganin sun samu damar lashe gasar ta firimiya.
Sai dai kungiyar bata fara kasuwanci a kasuwar siyan yan was aba sai a karshen watan agusta, inda ta siyo Dan wasa baya na kungiyar Ajad, Dabinson Sanches sai kuma Aurier daga PSG.
Sai dai kungiyar ta siyar da Kelly Walker zuwa Manchester city, amma kungiyar har yanzu tanada karfin da zata iya bawa manyan kungiyoyi mamaki.
Dan wasan gaba dan kasar ingila Harry Kane da takwaransa Delle Alli sune suke jan ragamar kungiyar sai kuma Erickson wanda shima yana bada gudunmawa sosai a kungiyar.
Masana dai suna ganin kungiyar tana bukatar ta lashe kofi ko guda daya ne domin ta kwantar da hankalin manyan yan wasan kungiyar domin su zauna a kungiyar, domin indai har kungiyar takasa lashe kofi guda daya a wannan gasar ana ganin yan wasa irinsu Harry Kane, Delle Alli da Erickson zasu iya barin kungiyar zuwa manyan kungiyoyin da suka ciki da wajen kasar.
Gasar firimiya dai wasanni hudu akayi, kuma kungiyoyi da dama sun kasha kudi wajen siyan yan wasa, abinda yarage a gani shine yadda wadanda suka kasha kudi zasu kasance, da kuma yadda yan wasan da aka siya zasu bada gudunmawa sosai .