Na Adamun Adamawa Bauchi
Daga Yusuf Kabir
09063281016
Sunan wannan littafin da ke sama kadan baya, littafin gajerun labarai ne na gaskiya da zamantakewar aure a wannan zamanin, wanda zauren “Marital Sulutions” na Whatsapp suka tattauna a kan labaran gaskiya da suka faru a aurensu a yayin da shaharren dan Jarida kuma gogaggen Marubuci Mal. Adamun Adamawa Bauchi ya tattara tare da tsarawa ne. Littafin yana da gayar muhimmanci da daraja ga wanda ya mallake shi tattare da karanta shi cikin nutsuwa. Littafin yana da shafi 128 yana dauke da labaran gaskiya da suka faru a rayuwar aure har guda 40. An buga shi da kyakyawan bugu da tsari mai inganci tattare da bango wanda zai dauki hankalin duk wanda ya gan shi.
- A shafi na 105 na littafin labarin Malama Sakinat Ibrahim Gwadabe (shaharriyar ‘yar jarida ce kuma marubuciya) ta bayyana yadda mijinta ya share mata wata damuwar kudin rijistar wani zangon karatu da bata biya ga shi kuma ana daf da fara jarabawa, sai ga mijinta ya samo mata kudin nan a sadda tana daliba a Makaranta tana cewa:”Can wajen karfe 8:00na safiya na farka, cikin mamaki da tsoro na kalli gefen ‘pillow’da nake kwace akai,wallahi sai ga fararen ‘yan dubu-dubu turus a wajen!”
Wannan labarin na nuna yadda mijinta ya yi fafutikar share mata hawayen damuwa a yayin da take tsananin bukatar hakan.
- A shafi na 91 kuwa Malama Sumayya Makki,Bauchi ta bayar da labarin yadda mijinta ya yi saurin yi mata hakuri da yafe laifin da ta yi masa a sadda suka je yin ‘NYSC REGISTRATION’tare da shi.Ya kuma gargade ta a kan ta dauki dukkanin file dinta daga gida domin ka da sai sun tafi a nemi wata takardar, amma ta sabawa umarninsa. Abin da yake gudun kuwa shi ne ya faru. Sai ta ki daukar takardunta duka, a sadda aka zo sai da aka nemi wata takardar. A nan ne take ba shi hakurin rashin bin umarninsa da ta yi tana cewa: “Wallahi ina ba shi wannan hakurin,take na ga abin da ke cikin idanunsa ya ragu da kusan kashi 50/100.”
- A shafi na 33 na littafin kuwa,labarin sadaukarwar da matar Malama Zunnuraita ta yi wa Malam Adamun Adamawa Bauchi ne da ta yi masa a yayin da ta dauki tiramen atamfofinta da less masu tsada ta ba shi domin ya kaiwa Mahaifiyarsa da ke Yola a wani lokaci na rashin kudi. Ga abunda yake cewa: “Haka ta dauki zannuwanta uku da Less (dukkansu masu tsada) ta bani, daga ranar na sa ranar zuwa ganin gida, wannan sutura da na kaiwa mahaifiyata ba karamin jin dadi ta yi ba, ta rinka sa mun albarka, duk dangina suka rika yabon zannuwan, har wata yayata tana cewa gaskiya ba za su bari tsohuwa ta sa wadannan turame masu tsada ba, kwashewa za su yi su canza mata su da masu araha daidai da ita!
Allah ya yi miki albarka Zunnuraty! Allah ya sa ki cikin tawagar ‘yan rakiyar Sayyida Fatima Zahara ‘yar Manzon Allah (s) a gobe kiyama! A ko da yaushe ina alfahari da ke!!
- A shafina 20 na littafin Malama Juwairiyya Kano cewa ta yi tana mai bayyana yadda mijinta yake da kyankyami (kyama) sosai, domin da zaran an ce Akuya ko Tunkiya ta haihu a gidansu, to shi kenan ya daina shan ruwan gidan, amma saboda sadaukarwarsa shi ne wata rana da ta haihu cikin dare shi ne ya zamanto mata tamkar Unguzoma domin kuwa a cikin daren sai da ya wanke komai na kazantar haihuwar tana cewa: “Duk wani taimako da nake bukata a daidai wannan lokaci ya yi mun, amma abu mafi muhimmanci da ya zauna mun a rai si hi ne, bayan na haihu na yanke cibiya,to dum sauran hidimar mai jego da mata ke yi shi ne ya yi mun a wannan lokacin, shi ya kwashe komai na kazanta ya wanke wurin tas, ya gyara yarinya ya shirya mun komai da mai jego ke bukata, ko da safiya ta waye abincin da zan kai a bakina shi ya dafa mun. Saninsa da na yi da tsananin kyama,da kuma irin yadda ya manta da wannan kyamar ya dumulmule a cikin kazantar haihuwa, shi ne abu mafi girma da ya zauna mini a rai game da shi, ba zan taba mantawa da wannan ba! Na gode da kulawarka maigidana! Na jinjina wa sadaukarwarka gareni!
- A shafi na 113 na littafin kuwa Malama Fatima (Ummu Abiyha) Jigawa cewa ta yi:”Ranar da ba zan taba mantawa da ita a rayuwata da Habibina ba ita cewa matsayina na Principal a daya daga cikin makarantun sakandiren ‘yan mata da ke jigawa, akwai wani mako (Weekend) din da na kira ‘Meeting’na manyan gari da iyayen yara (PTA/SBMC MEETING).To a ranar Lahadi bisa hadari sai ya zamo babu kudi a asusun mu na makaranta, ga shi wata ya yi nisa ni ma ba abubuwa (kudi) a hannuna.Ta ci gaba da cewa, ina cikin wannan boyayyen tashin hankali, kawai sai na ga shigowar Habibina,ya shigo dakin taron ‘Unedpected’ dauke da kayan ‘Refreshments’ na alfarma kala-kala! Yana shigowa ya fara rabawa da kansa, nan da nan wurin kowa sai murna. Wani abu mafi burgewa shi ne, da kansa ya zo ‘High Table’ kan kujerar da nake ya ajiye mun nawa kayan makulashen a gabana! Wannan abun ya mun dan karen dadin da ba zan taba mantawa da shi ba, domin ya fitar da ni kunyar jama’a! Kuma ya mutuntani a gaban kowa! Na gode wa Allah da samun ka Habibina!”
- A shafina bakwai na littafin kuwa, Malam Abu Ubaida Kazaure ne ya bayyana sadaukarwar matarsa a gare shi yana mai cewa: “Akwai wani lokaci ana cikin yanayin babu abubuwa (kudi), kuma ga shi ina karatu a Katsina, ga lokacin biyan kudin Makaranta ya yi,komai ya tsaya cak,a lokacin ina Katsina,sai na yi waya da Madam (ita tana Kazaure) ina fada mata ga halin da ake ciki, ita kuma tana cikin yanayi na bukatun rayuwar yau da kullum,sai na ce mata to sai na ce ya za a yi mu rufawa kan mu asiri? Sai ta ce ba matsala,in ba ta izinin za ta je unguwa,na ce mata adawo lafiya.To,ni sai na kasa samun nutsuwa,abinka da mai iyali,ina tunanin dole in dawo in nema musu abinci,sai na kamo hanya daga Katsina na taho gida Kazaure,lokacin da na iso sai na iske ta gyara gida tsaf,ga kua wasu kudade masu yawa ta samo,sai na tambayeta daga ina aka samo wannan kudin? Sai ta ce mani ta yi sammako ne ta je Kano ta sayar da Gwal dinta domin mu rufawa kanmu asiri.”
Wannan tsakure kenan daga wannan littafin. Allah ya sa mu amfana da shi.