Connect with us

ADABI

Sharhin littafin ‘ADAWAR SO’ Na Ayuba Muhammad Danzaki

Published

on

Ayuba Muhammada Danzaki, marubuci ne wanda ya shigo duniyar rubutu a shekara ta 2010 da littafinsa mai suna Shingen Kauna, memba ne na kungiyar marubuta ta Hausa Authors Forum da kuma ANA Kano, sannan shi ne tsohon shugaban kungiyar marubuta ta Tsintsiya Writers Association, yanzu haka kuma shi ne shugaban kungiyar marubuta ta Kainuwa Authors Kano. Ayuba Muhammad Danzaki ya rubuta littattafai da dama, daga cikinsu akwai:

– Shingen Kauna

– Adawar So

– Fadar So

– Rayuwar Bilkisu

– Hadin Zumunta

– Auren Kirista

– Labarina

Bayan haka Ayuba M. Danzaki, marubuci ne na wakokin Hausa, yana daya daga cikin shugabannin Kungiyar Marubuta Wakokin Hausa Ta Najeriya reshen jahar Kano.

 

Sharhin Littafin ‘Adawar So’ Na Ayuba Muhd Danzaki

Littafi: Adawar So

Marubuci: Ayuba Muhd Danzaki

Kamfanin Dab’i: Garba Muhd Bookshop

Shekarar Bugu: Ba a Sani ba

Yawan shafuka: 144

Farashin Littafi: Ba a sani ba

Lambar ISBN: Babu

Mai Sharhi: Muttaka A Hassan

Manufar Sharhi: Bunkasa Adabi Da Harshen Hausa A Duniya.

 

Labari

A garin Yaryasa aka haifi Umar Niga, duk da iyayensa talakawa ne sun so ya yi karatu sai dai ya fandare  ya zama takadari, kwarrare wajen ta’ammali da kayan maye kamar taba da wiwi da sholisho da sauransu, ga kuma 6atawa ‘yanmata rayuwa tare da sace-sace.

Wata rana ya shiga gidan Hajiya Hajara ba ta nan ya yi mata sata ashe a idon wani yaro ya yi, da asiri ya tonu ta ce sai an biya ta, tilas mahaifinsa ya biya da ya zo gida ya zane shi. Ashe Umar Niga ya ji haushin dukan don haka ya ja zugar abokansa suka yi wa Hajiya Hajara mugun dukan da ya yi sanadin mutuwarta. Bayan mutuwarta ‘yan uwanta suka zo daukar fansa ba su same shi ba suka huce a kan mahaifinsa wanda shi ma hakan ya zamto silar mutuwarsa, mutuwar mahaifinsa ta saka mahaifiyarsa jinya wadda ita ma a karshe ta ce ga garinku nan.

Mutuwar iyayensa ta sa ya bude sabon shafin iskanci. Wata rana ya haddasa gobara a wata rugar Fulani wadda ta yi matukar 6arna, uwa-uba ya yiwa ‘yanmata goma ciki, wannan al’amarin ya sa jami’an tsaro nemansa, shi kuma ya sulale ya gudu Legas.

To a can din sai ya hadu da abokai ‘yanfashi, bayan sun yi fashi ne sai ya tafi Saudiya ya yi addu’o’i da ya dawo sai ya gina babban gida da kamfani tare da sauya suna zuwa Alhaji Faruk.

Rayuwarsa a Kano tasa ya yi wani amini mutumin kirki mai suna Alhaji Yusuf dan aljanna, bayan da suka zama magidanta sai matansu ma suka zamto kawaye, Alhaji Faruk ya haifi da Faisal yayin da Alhaji Yusuf ya haifi Najib. Ko da yara suka taso su ma sai suka zama aminai.

Duk da Alhaji Faruk ya yi aure bai daina bibiyar matan banza ba, a karshe ya yiwa wata karuwa ciki ita kuma ta jefar da jaririyar inda amininsa ya tsinci jaririyar.

A wata shekara ne da ya ji jami’an tsaro sun dawo da nemansu sai ya damka dansa Faisal a hannu amininsa matarsa kuwa ya saketa sannan ya bar kasar.

Bayan shekaru 25 dansa da dan amininsa sun zama samari, diyar da suka jefar ita ma ta zama buduruwa sai dansa Faisal yake neman auren Nasiba diyar da suka yar.

Amma amininsa Najib shi ya auri Nasiba, sai dai duk da haka Faisal ya nuna Adawar So, inda suka rika cin amanar Najib shi da Nasiba har ya yi mata ciki sai a karshe ya gane kanwarsa ce uba daya.

 

Warwarar Jigo

* Littafin ya tsoratar a kan illar bijirewa iyaye kamar yadda Umar

Niga ya yi a karshe mahaifinsa ya yi masa baki ya daidaice.

* A fakaice littafin ya nuna illar cin amana kamar yadda Faisal da

Nasiba suka yi a karshe suka ta6e.

* A fakaice littafin ya fadakar da mu a kan illar kyale abokanmu na

shiga gidanmu ko da ba ma nan.

* Littafin ya nusar da mu illar zuwa wurin boka.

 

Zubi Da Tsari

Marubucin bai yi amfani da babi ko lamba ba amma ya yi amfani da kanun labarai a wasu shafukan.

 

Salo Da Sarrafa Harshe

Marubucin ya yi amfani da salo mai armashi ta yadda kana karantawa littafin na kara dadi. A 6angaren sarrafa harshe ma ya nuna gwanintar harshe wajen amfani da karin magana da azanci.

 

Ka’idojin Rubutu

Littafin bai samu matsaloli da yawa a kan ka’ido jin rubutu ba sai wadanda ba za a rasa ba kamar; amfani da digo biyar a matsayin alamar zarce maimakon uku (…).

 

Kuskure Da Tambayoyi

1) Rububuta littafi babu shekarar bugu kuskure ne, ko marubucin ya san da haka?

2) A littafi na 1 marubucin ya nuna Alhaji Faruk sakin matarsa ya yi, yayin da a littafi na biyu kuma sai ya nuna mutuwa ta yi. Ko wenne ne gaskiya tsakanin sakin da mutuwar?

3) A littafi na daya shafi na 11 marubucin ya nuna Umar Niga ya sha sholisho guda biyar har ta bugar da shi, amma a sakin layi na 3 sai marubucin ya ce, “…A fusace Umar ya daga hannu ya mari Malam Isuhu ya dinga dukan shi sai da ya yi masa lilis…” Anya kuwa wanda ya sha sholisho 5 har ya bugu yana da karfin da zai iya yiwa wani duka har ya sa ya yi laushi?

4) Marubucin ya nuna Faisal na tare da Najib a gida daya wato gidan matarsa. Anya abu ne mai yiwuwa a samu wanda zai amince ya ginawa saurayin da ya ta6a neman auren matarsa daki a cikin gidansa?

5) Bayan Alhaji Faruk ya yiwa karuwarsa Binta ciki ya gujeta, marubucin ya nuna ta tsane shi, amma a littafi na 2 sakin layi na 3 sai ya nuna sun hadu da Binta sun yi gaisuwar mutunci har ta ba shi labarin yadda ta yi da jaririyar. Anya kuwa mutumin da aka tsana za a tsaya a yi gaisuwar mutunci har a tsaya ba shi labari?

6) Likitoci sun tabbatar Najib ba zai haihu ba amma a littafi na 2 shafi na 42 sakin layi na 5 Najib ya kai karar matarsa cewar ya kamata tana shan magananin zubar da ciki amma sai iyayensa suka ki nuna kulawa har suka yi masa fada. Hakan kuwa abu ne mai yiwuwa?

7) Su kuwa mutanen Yaryasa wadanne irin mutane ne da duk neman da suke wa Umar Niga zai fito takarar gwamna amma a kauye a rasa wanda zai gane shi?

8) An rubuta ‘KARSHE’ sai kuma marubucin ya zo da KARIN BAYANI ko ya san kuskure ne?

 
Advertisement

labarai