Sharhin Littafin ‘Gidan Haya’

Gidan Haya sanannen littafi ne wanda ya yi shuhura a kafar sadarwa ta zamani, musamman ma a dandalin abokai na facebook da kuma Whatsapp. Labarin na Gidan Haya dai fitaccen marubuci Lawan Muhammad Prp ne ya rubuta, wanda shi ne marubucin littafin BAKIN DARE, KWANAN GIDA, KURMAN ZANCE, MATAR MARUBUCI da kuma fim din AZAZILA da dai sauransu.

Malam Lawan shi ne ya lashe gasar nan ta gajerun labarai ta MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA a mataki na Biyu (2) da labarinsa mai taken HANGEN DALA… wacce aka yi a karkashin jagorancin Farfesa Ibrahim Malumfashi a shekarar 2014/2015. Kuma shi ne zavavven sakatare na kungiyar marubuta ta HAUSA AUTHORS FORUM (HAF).

Ga dai sharhin littafin na GIDAN HAYA daga alkalamin MD Asnanic, marubucin littafin ALKAWARIN JIYA da kuma UMMUL-KHAIRI.

Sharhin Littafin ‘Gidan Haya’

Marubuci: Lawan Muhammad PRP

Sharhi: MD Asnanic

 

Shimfida

Littafin da marubuci Lawan Muhammad PRP ya yi wa lakabi da Gidan Haya, yana kunshe da wani irin rikitaccen labari mai bukatar nazari matuka yayin fahimtarsa. An yi kokari sosai wajen tsari da zubin labarin da kuma yadda akai ta koari wajen kauce wa kurakurai. Labari ne mai salo irin na rike makaranci.

 

Duk da labarin ya kunso mabambantan jigogi, amma babban jigon da ke jan akalar labarin shi ne Kwadayi, in na ce kwaďayi ina nufin inma a kan kyakkywar mace ko kuma a kan dukiya da kyale-kyalen duniya. Bayan wannan jigon na ci karo da jigo mai matukar muhimmanci a kan abota. Akwai abokai biyu a labarin (Nagari da na banza). Duk da alhakin shiga haďarin Usman ba ya kan Lauje dari bisa ďari amma ya taka rawar-gani wajen kara dulmiya shi a haďari. Sai akai dace abokinsa na kirki wato Abubakar ya yi sandin tsirarsa. Sannan na ci karo da jigo mai tambihi game da *kishi*, wanda a yanzu ba kumallo kawai ya zame wa mata ba, shi ne ma ruwan shansu, kowacce da iyakar makawrwar da ta kwankwaďa.

 

Duk da yunkuri gami da taka-tsan-tsan da marubucin ya yi wajen kauce wa kurakurai hakan bai hana ni tsinkayar wasu lamura masu kama da kuskure ba, sai dai na bar su a babin ajizanci irin na mutum (Allah ne kawai ke yin dai-dai), ko kuma ta yuwu makantar alkalami ne. Ga kurakuran kamar haka :-

  1. Labarin ya nuna mana Abubakar ya hadu da Jamila ne yayin da suke bautar kasa, in ko haka ne Abubakar yana da kwalin digiri ko na babbar difuloma. Wanda kuma yake da wannan kwali da zai nemi aikin ďan sanda (police), akalla zai fito ne da mukamin ASP, amma kuma sai na ji an kira shi da Sargent.
  2. Labari ya nuna mana a farkon labari lokacin da iyayen Aisha suka hana Usman aurenta, har alfarma ya nema da su bari ya je Gwambe ya shaida wa iyayensa ko zai samu wani abu, amma ina duk da haka suka buďa wa idanunsu toka. To amma kuma a can cikin labarin sai marubucin ya nuna cewa Mahaifin Usman ya daďe da rasuwa tun Usman ďin yana karami, ita kuma Mahaifiyarsa tana wani kauye a Maiduguri tare da ýanuwanta, bugu da kari ma bai san inda zai ga ýanuwansa a Gwambe ba. Ko marubucin ya manta da waccan ibarar farko ne?
  3. Lokacin da aka kai Usman gidan yari, an kai shi ne a matsayin ‘Suspect’ ba ‘Guilty’ ba, kuma idan mutum Suspect ne (wanda ake zargi) ba a saka ma sa Uniform na bursuna har sai lokacin da ya tabbata Guilty (mai laifi). Amma kuma sai dai kash! Labarin ya nuna an saka masa kayan bursuna, domin suna jikinsa ya gudu.
  4. Daga karshe Abubakar ya anso wa Usman kayan aikinsa, har da su na’urarsa ta Laptop, amma sai na ji ba a yi bayanin littafin Check din da Aisha ta ba shi ba, domin har da shi aka nuna ’yan sandan sun wawura a yayin bincike. Kuma ya na da muhimmanci a wajen Usman ďin.

 

  1. Irin wannan labari yana bukatar zurfafaffen bincike, domin ya ta6o sassa na ilimi da yawa. Misali ilimin aikin ýan sanda, likitoci, alkalai da gidan yari.
  2. Yadda labarin ya tsaru gaskiya ya samu nakasu wajen mallakar suna mai jan hankali. Sunan labarin bai dace da labarin ba. Akwai sunaye da za su iya ďaukar hankali kuma su dace da gundarin jigon labarin, kamar:-

Savanin Hankali

Tsaka Mai Wuya

Mabuďin Wahala

Tangalili

Jumurda

Rikita-rikita

Da dai sauran sunaye masu fassara cikin labarin.

  1. Marubucin ya kamata ya dinga lura da duk abinda ya faďa idan yana rubutu, ta hanyar komawa baya yana bincikawa don kauce wa tufka da warwara.
Exit mobile version