Sharhin The Lancet Ya Tabbatar Da Nasarar Da Sin Ta Samu A Yaki Da Annoba

Daga CRI Hausa

Sharhin da shahararriyar mujallar kiwon lafiyar nan ta “The Lancet” ta wallafa ya bayyana cewa, tun bayan da aka bude birnin Wuhan, kasar Sin ta samu manyan nasarorin yaki da annoba kuma ta sake farfado da harkokin tattalin arzikinta da hada hadar al’umma ta yau da kullum. Game da batutuwan dake shafar kimiyya da kiwon lafiya kuwa, hadin gwiwa shi ne mafi inganci sama da yin fito na fito da juna. Kalubalolin kiwon lafiya na duniya suna bukatar daukar matakai na kasa da kasa da yin hadin gwiwa tare da juna. Yanzu lokaci ne da ya fi dacewa da hada kai domin amfanin dukkan bil adama. (Ahmad Fagam)

Exit mobile version