Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta taka wa gwamnatin tarayya birki a shirinta na gurfanar da alkalin alkalan Nijeriya Mai Shari’a Walter Onnoghen, a gaban Kotun Da’ar Ma’iakata.
A ranar Jumma’a ne gwamnatin tarayya ta hannun kotun da’ar ma’aikata ta shigar da tuhumar 5 a kan alkalin alkalan.
An shirya gurfanar da shi ne a jiya Litinin amma bai samu halartar kotun ba, sai dai kuma a hukuncin da mai Shari’a N.E Maha ya yanke ya bayar da umurnin cewa, dukkan bangarorin su dakatar da daukar duk wani mataki har sai ya yanke hukunci a ranar 17 ga watan Janairu 2019.
Ya kuma bayar da umurnin ne a kan kara ta bangarori biyu na cewa a tabbatar da gabatar da dukkan takardun da suka kamata sannan kuma dukkan wadanda karar ya shafa su tabbatar da sun bayana a gaba kotun a ranar da aka sanya don saurarar kasar.
Cibiyar “Centre for Justice and Peace Initiatibe” ta shigar da karar guda biyu mai lamba FHC/ABJ/CS/27/2019.
Wadanda aka hada a cikin karar sun hada da Ministan shari’a kuma Antony Janar na tarayya, Abubakar Malami da shugaban Kotun da’ar ma’aikata, Danladi Umar da Shugaban Rundunar ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, da kuma shugaban Majalisar Dattijai, Daka Bukola Saraki.
Daya karar kuma wanda kungiyar dalibai ‘yan kasashen waje (International Association of Students Economists and Management) mai lamba FHC/ABJ/CS/28/2019 an shigar ne don a dakatar da ci gaba da tuhumar alkalin alkalan na kasa.
Shi ma wannna karar ya hada da Ministan shari’a kuma Antony janar na tarayya, Malami da shugabanin kotu na CCT da CCB, da kuma shugaban rundunar ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris.
Kara mai lamba FHC/ABJ/CS/27/2019 da babban Lauya na kasa R.A Lawal-Rabana, SAN, ya gabatar a gaban mai shari’a Maha a ranar Litinin, haka kuma Mista Jeph Njikonye ya tallafa wa gabatar da tuhumar a takarda mai lamba FHC/ABJ/CS/28/2019.
A dai dai lokacin da ake gabatar da karar a babban kotun na Abuja ana kuma can na shirye shiryen gurfanar da Onnoghen a kotun da’a ma’akata na Abuja.
Sai dai maishar’a Onnoghen bai halarci zaman kotun bah aka kuma ya tilastawa kotun tad age sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Janairru 2019.
Mai shari’a Maha na babbar kotun tarayya ya yanke hukuncin cewa dukan bangaririn su dakatar da daukar mataki har sau ya yanke hukunci a ranar 17 ga watan Janairu.
EFCC Tana Neman Jami’an Gwamnatin Benuwe Kan Satar Naira Biliyan 1.3 Na Albashi
Hukumar EFCC ta shirya cigiyar jami’an ma’aikatar kananan hukumomi da...