Abdullahi Usman, " />

Shari’ar El-Zakzaky: Harkokin Kasuwanci Sun Tsaya Cak A Kaduna

Harkokin kasuwanci sun tsaya cak a garin Kaduna in da babbar kotun tarayya ta jihar Kaduna ta dage Shari’ar da Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar in da ta ke karar Shaikh Ibrahim Zazzaky da Mai dakin sa Malama Zeenatu Ibrahim da kuma wasu mutum biyu.

Bankuna da kasuwannin jihar da kuma harkokin zirga-zirga a fadin garin Kaduna duk sun tsaya. In da mutane suka koma tafiya da kafafunsu saboda jami’an tsaro duk sun tare hanyoyin da suka hada da tikin Ahmadu Bello, Indifenda, Ibrahim Taiwo, Kano da kuma sauran manyan titinuna Kaduna irin su Yakubu Gowon, Muhammdu Buhari.

Su kuwa kasuwanni irin su babbar kasuwar Kaduna, wato Shaikh Abubakar Gumi da ta kasuwar Checheniya da sauran shagunan da ke kan titin Ahmadu Bello da sauransu duk sun kasance a kulle.

A zaman da aka yi jiya Laraba, Lauyoyin Malam Ibrahim suka nemi da a ba su dama don amsa bayanan neman beli da lauyoyin Gwamnati suka rubuto masu.

Da yake zantawa da manema labarai bayan fitowa daga kotun, Lauyan Gwamnati ya bayyana cewa an dage zaman yau ne don ba su sami damar kai sammaci ga sauran mutane biyun da ake tuhuma ba. Wato wandanda ake kara na uku da na hudu.

A na sa jawabin, Lauyan Shaikh Ibrahim Zakzaky da sauran wadanda ake kara, Mista Madwell Kyon ya bayyana cewa an dage zaman ne don sun shaida wa alkali cewa ba a ba su takardun jawabin lauyoyin Gwamnati ba na nema beli sai ranar talata da misalin karfe shida ya yamma. Wato ana gobe za a shiga kotu kenan. Don haka ba su sami damar dubasu yadda ya kamata ba ballantana su ba Lauyoyin Gwamnati amsa. Saboda haka suka nemi a ba su lokaci don yin nazari tare da ba su amsa.

Mista Madwell ya yi Allah wadai da yadda jami’an tsaro suka hana ‘yan jarida shiga kotu. Ya ce wannan shari’a tana bukatar adalci kuma adalci din duniya na bukatar su ganshi a zahiri. Saboda haka dole a baiwa ‘yan jarida damar shiga kotu don dauko abubuwan da suke wakana a cikin kotu don sanar da al’umma.

Exit mobile version