Khalid Idris Doya" />

Shari’ar Gwamnan Bauchi: Ranar Litinin Kotu Za Ta Raba Kwaya Da Tsakuwa Tsakanin M.A Da Kauran Bauchi

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Bauchi, ta ware ranar Litinin mai zuwa, 7 ga watan nan domin yanke hukuncin shari’ar da tsohon gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abubakar da jam’iyyarsa na APC suka shigar a gaban kotun, kan zaben da ya baiwa Sanata Bala Muhammad nasarar zama gwamnan jihar.

Shugaban tawagar Alkalai mai mutane uku, Justice Salihu Shuaibu shine ya yanke hukuncin a jiya jimkadan bayan masu kara da wadanda ake kara sun gama gabatar da bayaninsu na karshe kan shari’ar, inda shugaban Alkalai ya bayyana cewar za su yanke hukuncin a ranar 7 ga watan Oktoba.  

Da yake ganawa da ‘yan jarida bayan fitowa daga kotun, daya daga cikin tawagar Lauyoyin APC, Barista Rabiu Garba sun bukaci kotun ta amince da rokonsu kan zaben hadi da kwace kujerar gwamnan jihar da baiwa wanda suke karewa.

A cewar shi; “Mun roko kotu ne da ta amshi korafinmu. babban rokon da muke yi a gaban kotun shine, ta soke kuri’un zabe a mazabu 336 wadanda muke kara a kansu a kananan hukumomin Bauchi, Tafawa Balewa da Bogoro, musamman kuri’u na bogi da aka kara a wadanan mazabu.

“Muna son kotu ta cire kuri’un karya, a dawo a yi amfani da kuri’u na gaskiya wanda in aka tantance aka yi aiki a kansu da yardar Allah APC ce ta yi nasara kuma Muhammad Abdullahi Abubakar ne yayi nasara zaben gwamnan jihar Bauchi da aka gudanar na 2019,” A cewar shi.

Dangane da tambayar da ‘yan jarida suka masa, kun gabatar wa kotu da wani da kuka ce shi kwararre ne, amma ya zo da kansa ya ce shi ba kwararre ba ne, me za ka ce kan wannan batun? Lauyan ya amsa da cewa, “batun kwararre ko ba kwararre ba shine mai muhimmancin dubawa ba. Mu mun bar wa kotu ta tantance shi din kwararre ne ko ba kwararre ba. Amma abun da muka sani yayi kokari wajen yin bincike kan zaben da aka gudanar,” A cewar shi.

 A bangaren Lauyan gwamna mai ci, Bala Muhammad, Cif Chris Uche (SAN) Ibrahim Isyaku (SAN) sun bukaci kotun ta yi watsi da karar da tsohon gwamna da jam’iyyarsa ta APC ke yi, suna masu shaida wa kotun cewar karar ya gaza samun kwararan hujjoji daga masu gabatar shi.

Sun ce, shaidu 28 da APC suka gabatar, sun gaza tabbatarwa ko gamsar da zargin da APC ke yi a mazabu guda 336.

Wakilinmu ya shaida mana cewar jami’an tsaro na ‘yan sanda sun mamaye kotun domin tabbatar da tsaro a bisa barazanar tashin rikici a tsakanin magoya bayan masu kara da wadanda suke kare kansu.

Exit mobile version