Shari’ar Gwamnoni: An Tsaurara Tsaro A Kotun Koli

Rahotanni dake fitowa daga Kotun koli na nuni da cewa; an jigbe jami’an tsaro gabanin fara zaman Kotun Koli kan shari’o’in zaben jihohin da ke gabanta.

Lauyoyi da ‘yan jarida da ‘yan siyasa, mafi yawansu daga Kano da Sakkwato su ne suka cika kotun, kamar yadda majiyarmu ta shaida mana.

Akwai kuma ‘yan sanda da dama a cikin kotun wadanda suke kula da kofofin shiga cikinta.

Majiyarmu ta labarto mana cewa; wasu lokutan ‘yan sandan suna amfani da karfi wajen hana mutane shiga zauren kotun musamman idan an samu turmutsutsu.

Akwai matakan tsaro hudu da aka sanya a kan hanya kafin kai wa harabar ginin kotun.

Exit mobile version