Sharri Osinbajo Ya Yi Min –Jonathan

Daga Abubakar Abba

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayanna cewar mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo sharri ya yi masa da ya ce, tsohuwar gwamnatinsa ta fitar da Naira Biliyan 100 da wasu gundarin Dalar Amurka har Miliyan 295 a cikin mako biyu don shirye-shiryen zaɓen shekarar 2015.

Jonathan ya zargi mataimakin Shugaban Ƙasan da sharri ne a  wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Reno Omokri ya fitar ranar Juma’ar da ta gabata a Legas. Sanarwar ta ci gaba da cewa, sharri sai ƙara zamo wa Osinbajo jiki yake.

Sanarwar wacce ke ƙumshe da martani, an fid da ita ne kan furucin da Osinbajo yayi a Jihar Legas a makon da ya gabata, a wani taron bita na fastoci, inda aka ruwaito Osinbajo ya ce, “Jonathan ya fitar da ɗimbin kuɗi a ckin mako biyu kafin gudanar da zaɓen shekarar 2015.”

Sanarwar ta Jonathan ta ce; “Wannan ƙarya da sharri ne, kuma zan iya bugun ƙirji ince Osinbajo yanzu ya ɗaukar wa kansa wata sabuwar ɗabi’a ta yin ƙarya.

“Idan ‘yan Nijeriya na iya tunawa, makon da gabata mataimakin shugaban ƙasa lokacin da ya je Jihar Anambra ya tabka ƙaryar cewa gwamnatin tarayya mai ci, ta biya Dalar Amurka biliyan biyu don aikin gadar Neja.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ina da damar in tona asirin waccan ƙaryar ta Osinbajo da kuma ƙalubalantar fadar shugaban ƙasa data fitar da sanarwa akan maganar.”

“Kuɗin da aka fitar Naira Biliyan biyu ne kuma kuɗin an samar dasu ne daga Gidauniyar Kuɗi ta dukiyar ƙasa da ƙasa  da tsohuwar gwamnatin Jonathan   ta kafa wadda kuma Gwamnatin APC taki amincewa da hakan har ta ƙalubalanci hakan a gaban kotu.”

Sanarwar ta ce, “ cikin watan fabarairun  shekarar 2016,Osinbajo  ya ƙara tabka wata ƙaryar acewar da ya yi tsohuwar gwamnatin Jonathan data Yar’adua basu gina koda hanya ɗaya ba a lokacin suna kan madafun iko.

“Wannan zargin na Osinbajo hatta muƙarraban wannan gwamnatin, har da ubangidan Osinbajo basu yarda da hakan ba. Shugaba Buhari, ya fara ƙaddamar da wasu ayyukan da tsohuwar gwamnatin Jonathan ta yi, harda hanyoyi da tsohuwar gwamnatin ta gina.

“Ina ‘yan Nijeriya za su iya tunawa, tshowar gwamnatin  Jonathan ta sake gina hanyar Benin-Ore wani ɓangare na hanyar Benin-zuwa jihar Legas da hanyar Ɓom-zuwa Manchok da hanyar Kano zuwa Zaria da gadar da aka sanya suna bayan rasuwar sarkin Kano Ado Bayero da sauransu da dama.

“Akan zargin kwanan baya kuwa da Osinbajo  ya yi dole ce ta sanya shi ya shara ta, don ya samu ya karkatar da tunanin ‘yan Nijeriya akan badaƙalar zargin da ake yiwa Maina ya yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin mai ci, hatta iyalan Maina sun faɗawa duniya cewar gwamnati mai ci ce ta dawo da Abdulrasheed  Maina ta ƙara masa girma ta kuma bashi muƙamin darakta a  sashen inganta alumma dake ma’aikatar harkar cikin gida.

“Da aka ɗago gwamnatin sai ta ɓuge da halinta data saba na ɗora laifi akan tsohuwar gwamnatin Jonathan, musamman danganta dawowar ta Maina akan Jonathan.

“Bugu da ƙari, Atoni janar na ƙasa Abubakar Malami shi da kanshi ya furta cewar,”an dawo da Maina ne a bisa buƙarae ƙasa.

“Akwai kuma zargin  badaƙalar dalar Amurka biliyan ashirin da biyar na Kamfanin matatar mai ta ƙasa (NNPC), wadda itace badaƙala mafi girma da aka tabka a tarihin ƙasar nan tun shekarar 1914 zuwa yau.

“A ƙarshe, ‘yan nijeriya suna son su sani gaskiyar magana akan binciken da ake yiwa Babachir Lawal, wadda tuni aka kammala aka kuma gabatarwa da shugaban ƙasa watanni da dama da suka wuce, wadda kuma ba wani mataki da aka zauka akai.

“Yan nijeriya suna son su san gaskiyar magana akan badaƙalar, ba kawai ai ta ƙoƙarin tabka ƙarya ba a game da kuɗaɗen da aka yi wawure bada ake ta ci gaba da juya su ba tare da wata shaida ba.”

“Ina son in sanar da mataimakin shugaban ƙasa ya san cewar shi fasto ne kuma yana da ilimin aya ta 21:8 dake  cikin littafin Linjila da tace,” duk kiristan da ya yi ƙarya sashen jikinsu zai kasance a cikin wutar jahannama.”

Sanarwar ta ƙara da cewa,“lokaci bai riga ya ƙurewa Osinbajo ba, yanzu kuma zai  juyo ya fara roƙon ‘yan Nijeriya dasu yafe masu tare da ubangidansa akan gazawarsu ta cika alƙawarin samar da aikin yi miliyan uku a duk shekara ga ‘yan ƙasa  inda alƙawarin ya janyo rasa ayyuka miliyan 4.5 a cikin shekaru biyu na gwamnatin. Osinbajo yana ta neman wa zai zarga akan taɓarɓarewar da tattalin arzikin ƙasar ya yi a yanzu.

“Gaggawar da gwamnatin ta yi wajen ƙaddamar da asusun bai ɗaya ya jefa tattalin arzikin ƙasar nan cikin halin ni ‘yasu, bayanan da shugaban ƙasa kanyi in ya yi tafiya ƙasashen waje akan tattalin arzikin ƙasar nan da tsarin kuɗin musaya na ƙasa da ƙasa na gwamnatin da shawarar da aka baiwa bankin duniya da ya maida hankali wajen arewacin nijeriya, inda hakan ya nuna a zahiri maida fifiko ne ga arewa kawai haka naɗa muƙamai anfi baiwa ‘yan arewa ba tare da duba ƙwarewarsu ko cancantarsu ba.” Inji takardar

 

Exit mobile version