…Ci Gaba daga Makaon jIya
Ba zan manta ba, ranar Litinin 3/5/2010 mutanen Rogo su 6, su MalamAmiru su ka kawo ma ni ziyara har Katsina, su ka ganni, suka tabbatar hirar Freedom Rediyo ba karya b ace, da gaske ce. A rannan kuma matata ta haifi ‘ya mace, Amira a asibiti a Katsina. Tare ma da su muka je asibiti dauko matar tawa. Ba kuma zan manta ba, bayan kwana biyu, watau ran Laraba 5/5/2010 Allah Ya yi ma Malam Umaru Musa ‘Yar’aduwa shugaban kasa rayuwa. Ina kuma iya tunawa bayan sunan jaririyar da kwana biyu su Malam Ado Musa Lawan daga birnin Kano, kimanin su 6 su ma, su ka kawo ma ni ziyara, duk dai a kan su gaisa da ni akan namijin kokarin da aka yi akan tarihin Shata, mai tambura na Bilkin Sambo. Ma’anar abin a nan, wani, saboda son Shata, idan ba ya ganni ido-da-ido ba, hankalin sa ba za ya kwanta ba. Ka ko ga ashe har yanzu Shata na nan bai mutu ba, zancen sa kuma ba za ya taba gogewa ba a doron Duniya, tunda masoyan sa ba za su kare ba.
Akwai ma wasu da dama, irin su Idris da Abdullahi da Jauro da Sani, da su ka taso takanas-takano a lokuta daban-daban tun daga Fataskum, Gombe, da kuma Mayo Balwa da kuma Abuja su ka zo wajena Katsina su ka ganni, saboda shaukin son Shata. Akwai kuma masu yin alkawurra na cewa za su zo har Katsina su ganni, mu gaisa, su amshi wakikon Shata su kuma samu tarihi amma Allah Bai kawo su ba, irin su Alhaji Lawal Dangoma Kazaure wanda ya yi aiki a ofishin huldar jakadancin Nijeriya da ke Rasha da Amurka da Sin, watau China da Ingila (Shata ya yi masa waka) da Inginiya Nura Kalil (Dan takarar gwamnan Katsina) da Abbas Machika (Mamba) da Abdulhamid Danmusa, tsohon jami’in gidan rediyon FRCN, da sauran su.
Akwai kuma wasu rukunin jama’a masoya Shatan da su ba su zuwa, ko ba su zo Katsina don gani na, saidai su kira ni ni in je inda su ke, a kwana, ko a wuni, ko kuma a raba dare ana hira, kamar su Ambasada Adamu Sa’idu Daura, Alhaji Ahmed Gwadabe tsohon ma’aikacin hukumar buga takardun kudi ta kasa, Abba Gwadabe tsohon ma’aikacin BBC London, da sauran su. Dukkan ku ina godiya kwarai. Shi shugaban gidan rediyon Freedom ta Kano, Sojan sama, marigayi Air Bice Marshal Mukhtar Mohammed (kuma tsohon gwamnan Kaduna), yana ta son a kira ni mu gaisa, shima ya ganni, ta hanyar wani aminin sa, Ibrahim Abubakar. An shirya, kafin ranar ta zo Allah Ya yi masa rasuwa. Ya kamata Duniya ta san wannan tarihin, na shima yana daga cikin tarihin Shata, cewa saboda shi, yau ga shi babu shi, amma ana so a ga mai ba da tarihin sa.
Idan muka tsallaka waje, ba za mu manta da kokarin Kabir Ahmed Sararin Kuka ba, Jami’in gidan Rediyon Jihar Katsina (da sauran ‘yan rakiyar mu Yazid Abdul’aziz Nasudan da Sani Shu’aibu ma’aikatan Asibitin ‘Yansanda na Katsina) saboda namijin kokarin sa na yi mana jagora zuwa Yamai da Maradi da Damagaran a lokuta daban-daban. Muna godiya ga dimbin masoyan Shata a can da su ka hada da Sarkin Zinder (Alhaji Sanda Umaru; Shata ya yi masa waka, 1978) da Alhaji Ali Zaki Sarkin Maradi, da Bin Umar, tsohon mataimakin Shugaban majalisar Dokoki ta Kasar Nijar, da Alhaji Salisu Madobi, tsohon ministan Sadarawa na Nijar, da tsohon ministan Wasanni na Nijar da sauran su. Godiya ga Hukumar Jami’ar Yamai, sashen nazarin Harsuna da suka amshi bakuncin mu da Abdulsalam Shatan Nijar da marigayi Mamman Barka) Babbar godiya ga Issa Boube, tsohon mai zirga-zirga da tsawatawa da kuma minista a gwamnatin Djori Hammani.
Wannan ya isa ya nuna maka cewa, abin nan namu na turanci: eben in death, Shata is the greatest.
Saidai, zan yi amfani da wannan dama in nuna rashin jin dadi na da wani yaro yake yawan zagi na a kan wannan littafi, da aka sha wahalar aiwatarwa.
Kai, ba ma ta dalilin littafin Shata ba, a ko da yaushe ya ga rubutu na a daya daga cikin inuwoyin sadarwa sai ya yi mani dogon sharhi yana zagi na, haka kawai. Ni ban taba ganin sa ba, shi bai taba gani na ba. Ba mu hada gari guda ba, babu kuma dalilin da za ya zo ya sa mu yi wata mu’amulla a rayuwa, tun daga nan Duniya har mu sauka lafira, daga nan har ma ‘ya’yan jikokin mu. Da ni da shi, kamar Kasar Barkina Faso ce da Kasar Jafan, ba inda suka hadu: ko ta huldar jakadanci ko ta kawancen tattalin arziki, kuma da wuya ka ga wani dan Barkina Faso ya je Jafan, ko da yawon bude ido ko da karatu.
Da farko, muna cikin guruf na Tunawa da Shata na Abdullahi Dantasi. Rannan na yi wani batu, yaron nan ya yi mani kaca-kaca, ya zage ni tas. Na fusata na bar guruf din. Rannan kuma na yi wani zance na cewa don Allah a daina hada zance ko sharhin marubuta da mawaka wuri daya, a cikin wani guruf na marubuta na kanwar mu Umma Rimaye. Nan ma yaron nan ya yi ta zagi na kamar na kashe masa uba. Nan ma na yi fushi na bar guruf din saboda shi. Ana nan ana nan, a cikin guruf dina na kai na na Taskar Mamman Shata Tare da Dokta Aliyu Kankara, nan ma wuci-wuci ya na zagi na. Sai na kore shi daga guruf din sai wani can ya maido shi. Nan ma na fusata na yi masa korar kare a ciki. To daga nan ban kara jin duriyar sa ba sai da na fiddo wannan littafin na Shata na biyu cikin 2018, na ma dauka ya canza hali ya kara hankali. Kuma har gobe ni ban san abin da na yi masa ba. An san cewa a sha’anin rayuwa, akwai kuskuren da Dan Adam kan yi, har wani ya lurar da shi ya nuna masa, shi kuma ya gyara, saboda ajizanci na Dan Adam. Nayarda da wannan. Amma a wani gyara, kai da ganin s aka san dama mutum jiran ka yak e yi, don yana jin haushin ka.