Muhammad Abubakar" />

Shata Da Shekarun Karni Na 21 (K 21)

Hakika watanni hudu suka rage Dokta Mamman Shata Kachina (sunan Katsina na ainihi, na farko, tun daga zamanin Sarki Kumayau) ya cika shekaru 20 cif da barin wannan Duniya (ya rasu ran Juma’a 18/6/1999 da kimanin karfe 11 da kwata na dare) Idan muka waiwaya baya muka duba tarin dubban wakokin sa da irin gudunmuwar da ya bada wajen ci-gaban harshe da al’adar Bahaushe sai mu yi tunanin da wuya a manta da shi a Duniya duk yanda zamani ya ja da nisa.
Amma a fagen nazarin harshe da sha’anin adanawa da aiwatar da kimiyyar harshe da adabi da abin da mawaka su ka bar ma na baya sai mu yi tunanin na’ura na da adadin lokacin da ta kan kai kafin ta lalace. Wannan kuma sai a tambayi masu nazari na sashen harsuna, watau Language Technology wanda bangare ne na harshe watau Language Art. Nan fa gizo ke yin saka. Hakazalika masoya Shata da tarihinsa da ma wakokinsa suna iya fuskantar kalubale, idan har da gaske ne na’ura na da adadin lokacin rayuwa ko amfani.
Watakila Shata za ya iya tsallake wannan shinge, na adadin da masana nazarin harshe watau Language Art su ka bada/kididdige cewa duk mawaki ko marubuci, iyakacin zamanin abin da ya bari a cikin wannan na’ura ko takarda ko warka ya/su kai shekara 70 daidai ko kasa da haka a Duniya. Bayan shekarun nan 70 na’ura ko ma’adanar da aka kunshe wannan abu da ya bari za ta lalace.
Ni kai na, watarana a Kano na taba cin karo da wani Farfesa na sashen nazarin harshe na Jami’ar Maiduguri, inda zance ya yi zance har na yi masa tambaya. Shi kuma ya yi mani wani tsokaci makamancin wancan batu na sama. Har mu ka sunkuyar da kawunan mu kasa mu ka lissafa wasu ‘yan kwarorin mawaka da su ka shuda da ya ce yana sa ran za a daina jin duriyar su bayan sun shekara 70 da rasuwa.
Mun lissafa wasu mawaka kamar su Zabiya Tagoje wadda ta cira ta yi kaimi tun kafin ma Shata ya guguta, kafin ya rika ya zama abin tsoro, sannan ta rasu cikin 1970 tana da shekara 90. Ban da ita akwai Dadari Goje dan makahon birni wanda ya yi ma Malam Aminu likitan shanu na Ilorin waka, wanda marigayi Ladan Kontagora da marigayi Amadu Doka mai kukuma suka ba ni labarin sa. Ban da su akwai wasu fulani masu wakar jibtara ta mara ko sakaina. Mai jibtara da Dadari Goje, dukkan su sun kai shekara kusan 60 da ma doriya da rasuwa. Zancen ba na yau ba ne.

A tarin wakokin da ke a FRCN Kaduna, na tabbata akwai wakokin wadannan mawaka da na ambata amma fa ba a jin su sosai sabili da rashin kyawun na’urorin da aka dauki wakokin. Ke nan nan da shekaru kyas za ma su lalace. Na taba jin wakar Dadari Goje da FRCN su ka taba sanyawa a Rediyo amma ban ji abin da ma su ke cewa ba.
Idan mu ka karkata wajen rubuce-rubuce, muna iya tuna rubuce-rubucen Shehu Usamn Dan fodiyo da na Nana Asma’u diyar sa, wadda ta shahara wajen rubuta wakoki da littattafai, ta kuma fassara wasu littattafan da shi Bin Fodiyo ya rubuta da fillanci da kuma wasu da Larabci da bai samu damar wallafawa ba. A bayan su kuma an yi marubuta da su ka yi rubutattun wakoki, kamar misali: wakokin Sarkin Zazzau Aliyu Dan Sidi. A yau an wayi gari duk babu su saidai wadanda aka kwafa daga wadancan rubuce-rubucen na farko, amma ba dai ainihin wancan rubutun ba.
Shata mutum ne da Allah Ya ba baiwa ta musamman. Ilhamar sa ta daban ce. Kamanta ire-iren halayen sa na jaruntaka da dattaku da ma kawaici yana da wahalar gaske, saboda shi Shata, maroki ne kurum amma ba ya da halin maroka. Kamewar sa ta sanya da wuya ka gan shi ya je gidan ka ya ce ya zo ka bashi wani abu, saidai fa idan da waka ya zo. A kullum masoyan sa dada karuwa su ke yi, kamar ma yana raye. Hatta dan yau da ma aka haifa bayan Shatan ya rasu yana da sha’awar karanta tarihin Shata, ya san ko wanene shi.
Allah Ya hukunta mun shigo wani irin zamani ko Karni da aka samu sauye-sauye na ci-gaban kere-kere da haddasuwar na’urori, da suka kasance hanyoyin adana abaiban da magabata su ka yi ko su ka rubuta. Ga sh kuma kullum ma sai kara samun ci-gaban su ake yi. Ko a nan Social Media (kamar su facebook da whatsapp) zantuttuka da inuwowi na Shata sun fi daukar kaso mai yawa. Akalla akwai tsangaya ta tunawa da Mamman Shata da wakokin sa kusan kala 20 a whatsapp, akwai kuma abin da ya dan gaza haka a facebook. A yau dai a Duniya babu abin da ya wuce social media samun masu mu’amulla ko abotaka da ita, ta hanyar zamantakewa da nishadi da ma ayyukan da suka shafi kasuwanci ko saye da sayarwa, da ma ayyukan ofis. To duk wadannan sun saukake yanda sako za ya isa ga abokin hulda cikin hamzri ba ma tare da an sha wata wahala ko an dauki lokaci ba. To kuma sai gashi a wannan fage, al’amurran Shata sun fi dibar kaso mai yawa. Wakar Shata da ta shekara 70 ko 60 da yi sai ka ji ta a whatsapp ko facebook wani ya sanyo ta don sauraro ga masoyan sa.
Wani abin mamaki da tu’ajjabi, duk makaranta da cibiyar nazari da ka sani, ba su ki su rika yin tarurruka a kan Shata ba. Cikin Maris na 2013 Kwalejin Ilimi mai zurfi ta Tarayya da ke Yola ta gayyace ni na je na yi lacca akan makadin. Hakama a watan Janairun 2017 na gabatar da lacca a Kwalejin Ilimi ta jihar Yobe da ke Gashuwa, dukan su a sashen nazarin harshen Hausa.

Exit mobile version