Ibrahim Muhammad" />

Shaukin Son Cigaban Karamar Hukumar Minjinbir Ne Yasa Na Fito Takara – Saleh Ado Minjibir 5

Dan takarar neman shugabancin Karamar hukumar Minjibir karkashin jam’iyyar APC Alhaji Saleh Ado  ya bayyana cewa tsananin shaukinsa da son ganin cigaban yankin ne yasa ya fito domin yin takara in akayi la’akari da yanda karamar hukumar ta zama koma baya duk da cewa tana daga cikin dadaddun kananan hukumomi a jahar Kano.

Saleh Ado wanda shi ne shigaban dattawan APC na Minjibir  da yake takarar shugabancin karamar hukumar ya ce mukaminsa da sai bari a yanzu na babban sakatare a ma’aikatar kananan hukumomi da duk kananan hukumomi 44 suke har aka nemi yazo ya yi takara ta karamar hukuma guda daya wannan akwai dalili wanda shine cike da shauki na ganin cigaban Minjibir da aka kirkireta samada shekaru 40 amma har zuwa yanzu  wadanda aka kirkira a bayan bayanta sun fita cigaba wannan ga mutum.mai kishi abin kaico ne abin a duba ne.

Ya ce da yawa shugabanninda suka rike karamar hukumar  Minjibir rashin biya yya ya jawo rashin cigabanta da yawa sai su tika kai da gindi  da shugabanni na jaha wannan kuma bai haifarda da mai ido ba irin wadannan abubuwa sune suka hadu a zuciyarsa ya zama tilas sai an sami mutumai kishi da jajircewa domin ya rike wurin ya farfado da cigaba al’umma su mori romon damakwaradiyya wannan dalilinda yasa akaga cewa lallai suzo su   dafa domin samarda  cigaba mai nagarta.

Alhaji Sale Ado Minjibir ya yi nuni  da cewa rashin biya yya da ake samu daga shugabannin karamar hukumar da Gwamnatoci ko shugabanni na jaha ya taimaka saboda ya ya kai da kake kasa da kake bukatar sahalewar sama kuma zaka rika rashin biya yya ko ka rika kawa abubuwa dake jawo cikas a tsakanin shugabanni da mabiya ba wanda zai saki jiki ya kama ya taimaka wajen cigaban wurin bayan ana cin dunduniyarsa.Su kuwa bs yanda za’ayi suyi irin wannan domin mutanen sune ke cutuwa wajibine su dago su kuma za suyi iya yi suga cewa wannan yanki na Minjibir shima ya farfado ya zama kamar sauran yankunan ko fiye domin lamarin nasu ne sai sun tsaya akai sannan zai samu.

Alhaji Saleh Ado ya ce  cikin abubuwa da ya sani na garuruwa na dagatai 63 na yankin ba inda bai sa kafarsa ba.Yasan babban matsalatda tafi kowacce damun karamar hukumar Minjibir abu uku ne na Farko titindk ya tashi daga Ungogo yazo Minjibir ba karamar matsala bace in Allah ya yarda zasuyi kokari wajen Gwamna daya yaba cewa  in Allah ya yarda shine Gwamnanda zai ga nayan wannan titin.Amma masu tuntuba da bibiya da ladabi sune ba’a samu ba shiya hana aiwatarda wannan.Sannan titi daya tashi daga cikin garin Minjibir ya aYola yazo Ladin dsn dake ya tafi zango ya tafi can wannan titi koda karkara salamu alaikum ne akayi shima an gama dinke minjibir gaba da yamma.

Ya ce Asibitocinsu na Minjibir babban asibitine amma babu yanda yake ba gidan ma’aikatan da zasu zauna sannan anyi kaso na farko wajen gyara shi ba’ayi na Biyu dana Uku ba duk inda abin yake a jaha za suyi kokarin suje su nemo su tabbatar anyi haka a sauran Asibitoci  da sauran nashan magani za’ayi kokari a bunkasa su domin su taimakawa al’umma dan maganta cututtuka nan da nan.

Ya ce akwai matsala ta ruwa a bangaren Kau-kai, Kunya,Kwanar Dumawa,Kunya gari,Jirgabawa da sauran wurare nan sunfi ko’ina matsalar ruwa idan Allah ya yi taimakesu ruwa da yake zuwa daga danbatta ko aikin ruwa da akayi daha Ganduje zasu roki alfarma a sako musu layi guda da zai gangara har garin Jirgabawa duk sai a maganta matsalar ruwan ta nan.Sauran dayw bangaren akwai aikin ruwa da ake sa ran Gwamnatin jaha zatayi a Minjibir amma rashin tuntuba yasa an haka rijiyoyin amma an barsu ba’asa sauran kaya ytakin ba.Za suyi kokari suga sun tuntubi Gwamnati ko hadaka za’ayi da ita za’ayi domin azo ayi ayyukan .Sai bangaren gidan gona sunada dam da ake anfana rani da damina za’a taimakawa mutane a bunkasa noman a Minjibir.

Exit mobile version