Aisha Seyoji" />

Shawarata Ga Mace Ki Yi Kokari Ki Dogara Da Kanki Kafin Ki Yi Aure – Maryam

Ba na iya shiru in kyale Matan da su ke zaune ba sa Sana’a

Dogaro da kai kafin aure yana taimaka wa mace bayan ta yi aure domin da shi za ta dore, in ji bakuwar Adon Gari ta wannan makon. Ko mene ne dalilinta? Ku karanta hirar har karshe ku ji yadda ta kaya, da yake bakuwar tamu digiri biyu ke gare ta a fannin karatun boko da kuma kasancewa mai basira saboda ayyukan da ta gudanar a harkokin yau da kullum na kasuwanci da gwamnati.

Da farko masu karatu za su so jin cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki.
Sunana Maryam (Mairo) Muhammad. Ni ‘yar asalin jihar Gombe ce, amma a Bauchi na taso har na yi aure. Gida biyu maganin gobara (Dariya) mu takwas aka haife mu, bakwai mata namijin mu daya. Nice ta hudu a gidan mu.
Ni ce shugabar kungiya mai Tallafa wa mata da yara, Wato (syndicate in supporting women and children initiatibe) SISWACHI. Kuma nice na kirkiro kamfani mai suna kylsinteriors, sannan kuma ina da kamfanin jigila wato kylslogistics. Na yi makarantar firamare a Sa’ad Zungur Primary School ,Bauchi. Sakandare a federal Gobernment Girl College, Bauchi. Na yi Diploma a ‘Social Works’ a Jami’ar Maiduguri na karanta social works. Na yi Karantun ‘degree’ a Jami’ar Abuja, na karanta ‘Sociology’. Na yi Masters dina a international unibersity of Bamenda, Cameroon a Public health. Yanzu haka na yi aure ina zama a Abuja.

Bayan kungiyar da ki ke da ita, ko akwai wani abu da ki ke yi kamar sana’a ko makamancin haka?
Ina kula da kungiyata da na fadi sunanta a baya, Kuma ina dan kasuwanci a gefe.

Kamar wacce irin sana’a ki ke yi?
Ina Sana’ar duk abinda ya Shafi gyaran gida wa amare, ko Hotel ko sabon gida. ( Interior designing) sanan Ina harkar furniture.

Za ki kamar shekara nawa da fara ita wannan sana’ar?
Gaskiya zan yi shekara sama da Goma Yanzu da fara Kasuwanci , Amma har kar kungiya Yanzu haka shekara 7 kenan da farawa.

Me ya ja hankalinki ki ka bude kungiyar?
Abinda ya ja hankali na shin ne, na yi aiki a kan me talafa wa mai girma tsohon gwamnan Bauchi, Mal. Isa Yuguda, a kan harkokin muradun karni, (MDGs). A nan na ga abin tausayi kala-kala, na Kuma lura naga yadda mata da yara suke shan wahala, sai na yi sha’awar bude kungiya domin in dinga taimaka musu.

Ya za ki yiwa masu karatu bayanin yadda aikin kungiarki take?
Kamar aikin kungiya da yake abinda na karanta aiki ne na tallafawa Jama’a, sai ban sha wuya ba wurin koyon aiki. Kuma duk da haka ina neman taimako da kuma halartar taron kara wa juna sani don koyon aikin da kuma haduwa da wanda suka goge ta fanin harkar ta yanar gizo.

Toh ta ya ki ka koyi sana’ar gyaran gida?
Sana’ata ta gyaran gida dai tun da na taso ita ce baiwar da Allah ya yi min, tun ina yarinya na taso da sha’awar flower, har ba zan mantaba mahaifina yakan kawo mun rose fulawa kullum ya in ya dawo a wurin aiki. Sai nakan nemi kwalba in saka a ruwa. Nakan gyara wurin zaman shi in jera plates na tangaran. Sai a yi ta sha’awa. Da na girma Sai na yi wasu ‘yan kwasakwase don karawa kai ilimi.

Ita wannan sana’ar da ki ke yi kina da wani wajene na musamman da ki ka ware dan sana’ar ko kuwa a gida ki ke?
Gaskiya ko da na fara sana’ar ina yi wa ‘yan uwa da Abokan arziki a kyauta. Daga baya Sai na bude shago ina sai da kayan gyaran gida. A shagon ne sai na samu karbuwa ana yawan nemana don in yi aiki.

Ta wacce hanya kike bunkasa kasuwancinki?
Ina tallata kasuwanci na a kafofin sada zumunci da kuma raba katina na wurin sana’a ta, a haka sai ki ga an kirawo ni a waya.

Kamar wacce irin nasara kika samu game da ita wannan sana’ar da ki ke?
Alhamdulillah, na samu nasarori da dama. Babbar nasar da na samu da ba zan manta ba su ne lokacin da na samu aikin gyaran masaukin sojoji wato ‘command guest house’ a maiduguri da Bauchi, har yau ina alfahari da wadannan ayyuka guda 2.

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta cikin wannan sana’a wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?
Babbar kalubalan da na taba fuskanta shi ne, na samu wani aiki ana jiran kaya su iso ba su iso ba kuma da gari ya wayewar za a yi bikin bude daki. Na yi kuka har na ji ba dadi. Allah cikin ikonsa sai suka amince in gyara musu daki guda daya. A maimakon dakuna da yawa.

Ki na da wasu dalibai masu koyar ita wannan sana’ar, idan babu shin kina da sha’awar kouar da ita?
Gaskiya ina da shawa’awar koyar da Sana’ar nan gaba kadan. In Allah ya yarda.

Wanne irin shawara za ki bawa sauran mata na gida wanda basa sana’a?
Shawarar da zan bawa mata masu zaman gida shi ne, su dage su nemi abin yi. Idan kina da sana’a, babu abin da da zai gagare ki a rayuwa.

Idan kika ci karo da matan da basa sana’a ya ki ke ji?
Ba na iya shiru in kyale Matan da su ke zaune ba sa Sana’a idan na ci karo dasu. Abin yana bata min rai sosai, na kan ce musu ba sai da kudi da yawa ba za ki iya fara sana’a.

Wacce shawara za ki bawa mata na gida masu zaman jiran miji?
Shawarar da zan bawa mata masu jiran miji shi ne, ki yi kokari ki dogara da kanki kafin ki yi aure, domin idan kin yi aure, abin da ki ka dogara da shi, shi ne zai zama gatan ki nan gaba.

Ko kina da wani kira da za ki yiwa gwamnati game da masu sana’a?
Gaskiya kiran da zan ma gwamni shi ne, ta rika sayan hannun jari a wurin masu sana’a na kirkira, musanman mata domin su habaka su. Kuma su rika tallafa musu domin kara musu tattalin arziki.

Mene ne burinki na gaba game da sana’arki?
Burina anan gaba shi ne in ga na mallaki company na yin kujeru da gadaje wanda na kirkira da kaina.

Wacce shawara za ki bawa masu sana’a?
Shawarar da zan bawa masu sana’a shi ne, ya zama Akwai hadin kai tsakanin juna.

Me za ki ce ga makaranta shafin nan?
Abinda zan ce wa makaranta shafin nan shi ne su ci gaba da sayan jaridan nan domin su ma za su karu da bakin da ake daukowa na ko wani mako.

Exit mobile version