An Shawarci Fasinjoji Da Su Daina Shiga Mota A Wajen Tasha

Shugaban kungiyar direbobin haya masu gijilar daukar jamma’a zuwa garuruka daban-daban na jihar Katsina NURTW shiyyar Funtuwa Alhaji Hamisu Miloniya, ya shawarci fasinjojin da ke shiga motar haya zuwa wuraren da suke bukatar zuwa, da su daina shiga motar haya a wajen tasha domin kare lafiyarsu da dukiyoyinsu.

Shugaban ya bada wannan shawar ce lokacin da ya shiga babbar tashar motar don gane wa indonsa yadda aikin gyaran tashar ke gudana. Daga nan kuma sai ya nuna jin dadinsa bisa goyon bayan da suke samu daga direbobi masu shiga tashar domin yin lodi.

A cewarsa babu shakka gwamnan jihar Katsina Honarabul Aminu Bello Masari ya taka rawar gani a kan wanna aiki da yake yi musu wanda zai inganta bangaren sana’ar ta su da kuma sauran ayyukan raya kasa da yake yi a sassa daban-daban, domin al’ummar jihar Katsina su amfana. Haka kuma ya ci gaba da cewa, da zarar an kammala wannan aiki za su saukin gudanar da harkokin sana’arsu.

Da yake tsokaci game da mutane masu ra’ayin  shiga motar haya a wajen tasha cewa ya yi wajibi ne jama’a surinka kiwon lafiyarsu da kuma kare dukiyoyinsu. Haka kuma daga cikin abin da miloniyan ya bayyana a matsayin amfanin da fasinjojin da ke hawa mta a cikn tasah za su amfana da shi shi ne, idan suka manta kayansu za su dawo su same su. Domin duk direban da ya yi lodi a tasha aka manta akaya a motarsa zai kawo kayn ofishinmu, har sai mai kayan ya zo in tabbatar na sa ne a ba shi kayansa.

Saboda haka sai ya shawarci fasinjoji musamman masu hawan mota a wajen tasha da su daina yin haka domin su tsira da rayuwarsu da kuma dukiyoyinsu.

 

Exit mobile version