Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
An shawarci masu hannu da shuni a yankin karamar hukumar Rimi da su sadaukar da wani abu daga cikin dukiyar su wajen taimaka wa ayyukan al’umma a yankin.
Sabon shugaban karamar hukumar da aka nada a yankin, Alh.Hussaini Umar Rafindadi ya bada shawarar a lokacin da yake mika makullan azuzuwa guda uku wadanda tsohon gwamna a tsohuwar jihar Kaduna Alh. Abba Musa Rimi ya gina a unguwar Shema da ke garin Rimi.
Ya bayyana jindadinsa ga tsohon gwamnan bisa gudummowa da kuma taimaka wa kokarin gwamnati wajen bunkasa bangaren ilimi a yankin.
Alh. Hussaini Umar Rafindadi ya yaba wa Kauran Katsina Hakimin Rimi Alh. Nuhu Abdulkadir bisa cibiyar kiwon lafiya da ya gina, sannan kuma ya yaba wa tsohon gwamnan inda daga nan ya yi alkawarin samar da magunguna da sauran kayayyakin aiki ga cibiyar kiwon lafiyar.
A nasa bangaren, shugaban sashen mulki ya yi alkawarin samar da jami’in kula da lafiya da masu gadi a cibiyar kiwon lafiyar.
Da yake maida jawabi, Kauran Katsina Hakimin Rimi Alh.Nuhu Abdulkadir ya bayyana godiyarsa ga tsohon gwamnan Abba Musa Rimi bisa tallafin da ya bada ya kuma bukaci sauran al’umma da su yi koyi da shi.