Connect with us

Uncategorized

Shaye-shayen Da Matasa Ke Ciki Abin Takaici Ne

Published

on

A kowane gari, Kuma a kowace Unguwa a zamanin nan ba a rasa irin matasan nan masu shaye-shayen miyagu kwayoyi, wadanda a wasu lokuta abin har ya kan kai su ga maye mai tsanani, har ma ya kai wasu ga haukacewa.
Wannan matsala, matsala ce da za a iya cewa ta zama ruwan dare a tsakanin matasa, ta yadda wasu ma wannan dabi’ar ta raba su da kowa nasu.
Idan muka duba a cikin wannan matsala za mu gano cewa shaye-shayen nan wani mummunan abu ne Wanda ke bata tarbiyyar matsanmu, tare da kuma Neman kawo babbar matsala a mahangar gobenmu.
Na Kawo wannan ne bisa la’akari da cewa matasa dai su ne ginshikin kowace al’umma. To idan ya zama an yi sake wannan rukunin na al’umma ya lalace, to ya ake jin gobe za ta kasance ma jama’a.
Wani Bincike da na yi ya tabbatar mani da cewa Arewacin Nijeriya, musamman jihar Kano Na daya daga cikin wuraren da wannan abu ya yi kamari, musamman yawan masu shan Codeine, wani maganin tari mai sanya mutum barci.
Wani Binciken ya tabbatar da cewa wannan yana da alaka da halayyar jama’ar Arewa, Wanda yanzu haka ma yana haifar wa da ‘yan mata da matan aure damuwa da rashin abin yi, don haka sai suka ga shaye-shayen ne akwai zai samar da natsuwa.
Wannan ne ya sa nake ganin idan Hukumomi da shugabannin Al’umma ba su yi wani abu na gaggawa don kawo gyara a wannan fannin ba, to lallai akwai babbar matsala, musamman yadda ya zama abin ya shiga cikin Matan aure.
Abin yana da matukar Hadarin gaske, musamman idan aka yi la’akari da cewa Matan auren nan fa iyayen wasu ne, Haihuwa suke yi. Don haka ya ake so ‘ya’yan su su kasance, idan ba yi sa’a ba, su ma dole su taso a masu shaye-shayen.
Wani abin tada hankali kuma, shi ne yadda ‘yan mata suke shiga irin wannan mummunar dabi’a. Tun daga fatauci da sayarwa har zuwa shaye-shayen.
Don haka ne za ka ga irin wadannan matasa mata sun zama wasu gagararru a wajen iyayensu da ma al’ummar da suke cikinta.
Da yawan mata nan masu wannan mummunar dabi’a suna shiga ne don kawar da wani bakin cikin da ya dame su, inda ta kan ma kai har su dinga yawo Otal bin samari ana lalacewa.
Kamar yadda wani binciken kuma ya nuna cewa wasu da yawan su, musamman matan auren suna fama ne da bakin cikin zamantakewar aure, suna shan kwayoyin ne saboda su dauke hankalinsu daga damuwar da suke ciki, shigen dai abin da na yi bayani a sama.
Da yawan su suna shan Codeine din ne saboda ya yaye musu bakin ciki da damuwa, kamar yadda wata mata ta shaida wa manema labarai, inda ta tabbatar da cewa ta fara sha ne bayan mutuwar aurenta.
Wasu kuma ‘yan matan suna shan kwayoyin ne saboda su yaye wa kan su damuwa. Kamar yadda wasunsu kan fada cewa, sunan wannan shaye-shayen ne don su yaye wa kansu wani bakin cikin da suka shiga saboda wata matsala, musamman ta samari.
Na fi mayar da hankali a wannan rubutun nawa ne wajen mata saboda a fi Hadari Kuma ya fi muni. Domin su mata su ne iyayen mu, yau idan aka ce suna cikin wannan hali, to lallai ba za a samu nagartacciyar al’umma ba.
Kuma a bangare samari, ai abin ba a cewa komai, domin ya zama ruwan dare, har yana neman ya zama ado ne a tsakaninsu.
Saboda haka ne nake ganin akwai jan aiki a gaban iyaye, al’ummar da muke ciki da kuma Hukumomi. Domin idan aka bar wannan abu ya ci gaba da tafiya a haka, akwai matsala.
Na san Saboda munin wannan abu ne ya sa gwamnati ke da Hukumar kula da Sha da safarar miyagu kwayoyi, wato NDLEA, wacce kuma ke aiki tukuru don magance, ko kuma rage wannan abu.
Amma yana da muhimmanci mu gane cewa ‘idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai.’ Don haka wannan ba abu ne da za a bar wa gwamnati ita kadai ba, kowa ya wajaba ya bayar da tasa gudumawar.
Allah ya shiryar da mu gaba daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: