Daga Abdulrazaq Yahuza Jere, Abuja
Limamin Masallacin Shiyya ta biyu (Zone B) a rukunin gidajen ‘yanmajalisun tarayya da ke Abuja, Ustaz Ibrahim Lawal Usamah ya bayyana cewa matasan Nijeriya sun daran ma na sauran kasashen duniya kaifin basira da kwalkwalwa.
Sai dai yana da matukar ban takaici ganin yadda aka bullo masu ta bayan gida aka lalata su da shaye-shaye.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan abin da ya kamata Shugaba Buhari ya yi wa matasan kasar nan a matsayin tsarabarsa ta samun koshin lafiya don magance wa matasan abin da yake ci masu tuwo-a-kwarya.
Imam Ibrahim Usamah ya kuma yi bayanin cewa wannan harkar shaye-shayen da ake tsunduma matasan a ciki wata munakisa ce daga waje domin karya tunaninsu ga samar wa Nijeriya cigaban da ya dace.
“Babu inda shaye-shayen nan ke illa ga matasa irin Nijeriya, saboda idan ka lura da matasan Nijeriya nagartarsu ta fi ta matasan galibin kasashen duniya. Matasanmu ana koyar da su karatu da wani harshen da ba nasu ba na asali amma sai a wayi gari sun fi wadanda suke da wannan harshen na asali fahimtar karatun da aka yi musu. Su kansu mutanen kasashen waje suna mamakin irin kwakwalwa da fahimtar da ‘Yan Nijeriya suke da ita.
“Shi ya sa suke ganin idan suka kyale mu haka kawai za a samu wani lokaci da kodai mu fi su sanin kimiyya da fasaha da kere-kere ko kuma mu yi kafada da kafada da su. Saboda haka yawanci suka ki barin mu mu samu cigaba. Babban abin da za a iya cewa muna kerawa babu kokwanto a kasar nan bai wuce roba ba. Domin matasanmu sun gama karatu babu sararin da za a ba su dama su baje hajar kolin fasahar abubuwan da suka goge a kai a makaranta”.
Ustaz Usamah ya cigaba da cewa wannan ya sa dole matasan suka saki layin abubuwan da suka karanta a makaranta suka rungumi wasu kananan sana’o’I domin samun na sawa a bakin salati
“Akwai yarinya mace da na sani ta yi har digirinta na biyu amma shagon gyaran gashi ta bude, akwai wani matashi mai digiri yana nan yana tuka keke napep, akwai wani makamancinsa bera yake samu ya sa masa ‘chemical’ yana ratayawa a wuya yana tallar maganin bera har ma wasu suna masa dariya. Kuma sai ka ga wani tun ma kafin ya kammala sakandare an samar masa da aikin yi kuma daga baya ya zo yana so ya takura wa wadannan da suka fi shi ilimin ya hana su neman na abinci. Shin idan ba su yi sana’a ba, so ake su yi sata?” ya tambaya.
A cewarsa, wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka fi damun matasa a kasar nan da kuma irin yadda ake dankwafar da su wajen neman aiki saboda ba su da wani a sama duk kuwa da irin kwazo da basirar da suke da su.
“Sai wanda aka zaba masu ubangida ake ba su aiki. Tunda Allah ya sa Baba Buhari ya dawo cikin koshin lafiya, ya kamata ya duba wannan matsalar”.
“Matasan nan sun fi kowa jajircewa wajen zabe, amma wajen nada mukamai ko ba da aikin yi sai a yi watsi da su. Ko ita wannan gwamnatin mai ci matasa nawa ta nada su a manyan mukamai, idan ma akwai? Ba wani abu ne sabo ba a kasar nan a rika nada matasa sabbin jini a mukamai. Janar Yakubu Gowon ya karbi mulki yana da shekara nawa a duniya? Haka nan Baba Buhari a farkon mulkinsa, haka shi ma Janar Babangida. Dukkansu shekarunsu nawa? Suna matasa lokacin. Matashi na kwarai ba zai yi satar dukiyar kasa ba domin yana ganin yana da rayuwa a gaba, zai so a ce shi ma ya yi wani abu da za a rika yabawa da shi”.
Sai dai kuma a cewar Imam Usamah, idan za a nada matasan a yi kyakkyawan dubawa domin akwai masu sakin-layi a cikinsu, inda ya ce “Dole a dauko matashin da yake da akida, kuma ba barawo ba, wanda ba zai ci amanar kasa ba ko a hada kai da shi a cuci al’umma. Sannan ba irin wanda da karfi da yaji aka canza masu tunaninsu ba, kamar irin matasan da a zahiri za ka gani ga su mutane ne cikakku amma idan ka fara magana daya zuwa biyu da mutum sai ka ji ya saki layi saboda an gurbata shi da kayan shaye-shayen da suka fitar da shi cikin hayyacinsa”. In ji shi.