Bilkisu Yusuf Ali" />

Shehu Atiku Sanka: Gwarzonmu Na Mako

An haifi Marigayi Shehu Abubakar Atiku  Sanka dan Halliru dan Abubakar dan Musa (Mairisala)  a garin Katsina a shekarar 1896. Mahaifinsa Malam Halliru da kakansa malam Abubakar duk haifaffun Katsina ne. Amma mahaifin kakansa Mallam Musa (Mairisala) ya zo ne daga kasar Tunis shi da jama’arsa; shi ya sa a ke ce mu su Rumawa. Dalilin kiran sa da Mairisala kuwa shi ne malamin fikhu na farko da ya kawo littafin Risala kasar Hausa lokacin da ya je aikin Hajji ya gamu da ‘yan’uwansa Larabawan kasar Tunis sai ya fansheta daga wajensu ya taho da ita kasar Hausa ya kuma yada ta.

Shehu Abubakar Atiku ya girma a hannun ‘yar’uwar kakarsa mai suna Rahmatu (Yaya Babba) matar malam Abba Dan Fannah a Dandalin Turawa da ke Kano. Ta dalilin kulawarta ne har yay i karatun alkur’ani a hannun mijinta. An shaidi Rahmatu  da mace ce mai ibada da tsananin da rikon addini. Jajirtacciya mai  bin tafarkin darikar Tijjaniya sau da kafa. Sannan mai zartaccen Imani cikin Shehu Ahmadu Tijjani.  Ita ce ta tsaya tsayin daka a tarbiyyarsa har zuwa lokacin da Allah ya yi mata rasuwa a shekarar 1972.

Shehu Atiku ya fara da karatun al-kur’ani a hannun mijin kakarsa Malam Abba Dan Fanna  haka ya  yi ahalari da kurdabi da alburda da Badamasi duk a wajensa. Daga nan sai ya koma da karatu a wajen Shaihu Muhammadu Salga dan Alhaji Umaru inda ya karanci risala da Iziyya da arshada ta ibn Rushidi da Mukhtasarul Khalil har zuwa babin aure, ya kuma karanta littattafan akida kamar su Mukaddamatul Burhamiyya ta Imamu Sunusi da Akidatul wusda da sauransu.  Ya karanci littatafan darika kamar su Su’al wal jawab na shehu Muhammadu Salga da Yakutul faridah na shehu Nazifi. Ya ci gaba da neman ilimi a fannoni da dama kamar tafsiri da Hadisi da harshen Larabci inda ya karanci littattafan Alfiyya ta dan Malik da Ajrumiyya da Mulhatul I’irab da sauransu. 

Shehu Atiku ya zurfafa iliminsa da nean ilmai a fannonin fikhun darika da tasawwuf da sauran fannonin harshen Larabci a wajen Shehu Abubakar Mijinyawa Bakin ruwa.   Ya karanta littafai kamar haka a gun Shehu Mijinyawa kamar su Jawahirul ma’any da Durratul Kharidah ( Sarhin Yakutatul Faridah) da Bugyatul mustafida na shehu Arabi da Alfiyatul tasawwuf ta shehu Mustapha da sauran littattafai da dama

Shehu Atuku Sanka ya karbi darikar Tijjaniya a hannun Shehu  Muhammadu Sanka a shekarar 1916. Sannan ya yi tarbiyyar Ruhi a hannun Shehu Abubakar mijinyawa.

Shehu Atiku na Shehu bai tsaya a karatun littattafai ba, a’a har da harshen Larabci saboda shi ne harshen da malamai kan yi muhawara da shi a tsakaninsu a garin Kano a wancan lokacin. Ya karanta ilimin hisabi a wajen Muhammadu dan Ajurum da Mulhatul-irab ta Imamu Hariri mai littafin mukamah da sauran littattafan da suka shafi adabi da lugga (Harshe) da kuma ka’idojin Larabci.

Shehu Atiku na daya daga cikin manyan shaihunnan malamai na garin Kano da ma Afrika baki daya wanda tarihi ba zai taba mantawa da sunansa da gudummawarsa musamman a garin Kano da Najeriya da ma Afrika baki daya. Shehi Atiku ya kasance Shaihin darika wadda ya yi mata hidima jini da tsoka  da tunaninda da lokacinsa da ruhinsa.  Shehu Atiku ya wallafa litttattafai da daman gaske wadanda a kiyasi ana da tabbacin sun haura casa’in tun daga na rubutun zube da rubutattun  wakoki wanda ma fi yawa suna Magana ne a kan al’amuran addini da harshen larabci da kuma sufanci. A takaice rubuce-rubucensa sun kasu gida uku wato Sufanci da Adabi da kuma Fikhu.

Babu shakka Shehu Atiku ya yi gagarumin kokarin da ba za a raina ba dangane da rubuce-rubucensa litattafai ya kuma tsara wakoki a harshen Hausa da Larabci a kan abubuwa daban-daban. Misali ya rubuta wakoki na:

Yabon Annabi SAW

Yabon Shehi Tijjani

Yabon Shehi Ibrahim Inyass

Wa’azi da gargadi

Akida

Ibada

Da sauransu

Daga cikin wakokinsa akwai

8-Wakar amsar mai tambaya a cikin ma’aloli da yawa.

-Tusamma

-Taimakon Dakiki

-Asma’u zatil jamali

-Matserar mata

-Nasiha ga ‘yan’uwa

-Yabon fiyayyen halitta

-Arzikin masoya

-Tarihin kwaki

-Begen Muhammadu

-Rakada’u

Shehu Atiku Sanka yana da madaukakiyar daraja a wajen malaman amaninsa musamman ta bangarorin ilimai daban-daban tare da karfin hujja da kwarewa wajen bincike da gogewa wajen hujja da fasahar zance. Kuma ya nutse aa cikin ilimin sanin darikar Tijjaniyya hakan ta sanya ya himatu da darussan ta da bincike a kanta har sai da ya zamana ba shi da wanda za a kwatanta shi  da shi a wannan fanni.

Shehi Atiku malami ne da har a karshen rayuwarsa yana neman sani, mai hakuri da rashin gazawa da kyauta da daukar nauyi. Gidansa ya zama sansani na neman sani inda almajirai ke zuwa daga ko’ina a fadin kasar nan har da Nijar.

Daga cikin Almajiransa akwai:-

Shehu Balarabe Jega

Shehu Ibrahim Alti Funtua

Shehu Ahmad Abulfathi Maiduguri

Shehu Muhammadu Jibiya

Shehu Yahya Jibiya

Shehu Muhammadu Birnin magaji

Shehu Ibrahim Kaya

Shehu Adamu Katibi

Shehu Imrana Damari

Allah ya yi wa Shehi Atiku rasuwa ranar laraba 9 ga watan rabi-ul thani 1394 Hijiriyya. Yana dan shekaru 64 an binne shi a makabartar Gwauron Dutse.

Exit mobile version